< Micah 2 >

1 Woe to those who devise iniquity and work evil on their beds! When the morning is light, they practice it, because it is in the power of their hand.
Taku ta ƙare, ku da kuke shirya makirci, ku da kuke ƙulle-ƙullen mugunta a kan gadonku! Da gari ya waye sai ku fita ku aikata mugunta domin ikon aikatawa yana hannunku.
2 They covet fields and seize them, and houses, then take them away. They oppress a man and his house, even a man and his heritage.
Kukan yi ƙyashin gonaki ku kuma ƙwace su, ku yi ƙyashin gidaje ku kuma ƙwace. Kukan zalunci mutum, ku ƙwace masa gidansa, har ku ƙwace masa gādonsa.
3 Therefore the LORD says: “Behold, I am planning against these people a disaster, from which you will not remove your necks, neither will you walk haughtily, for it is an evil time.
Saboda haka, Ubangiji ya ce, “Ina shirya wa waɗannan mutane bala’i, yadda ba za ku iya ceton kanku ba. Ba za ku ƙara tafiya kuna taƙama ba, gama zai zama lokacin bala’i ne.
4 In that day they will take up a parable against you, and lament with a doleful lamentation, saying, ‘We are utterly ruined! My people’s possession is divided up. Indeed he takes it from me and assigns our fields to traitors!’”
A wannan rana mutane za su yi muku ba’a za su yi muku gwalo da wannan waƙar makoki, ‘An lalatar da mu sarai; an rarraba mallakar mutanena. Ya ɗauke shi daga gare ni! Ya miƙa filayenmu ga maciyan amanarmu.’”
5 Therefore you will have no one who divides the land by lot in the LORD’s assembly.
Saboda haka ba za ku kasance da wani a taron jama’ar Ubangiji da zai raba ƙasar ta wurin jefa ƙuri’a ba.
6 “Don’t prophesy!”—they prophesy— “Don’t prophesy about these things. Disgrace won’t overtake us.”
“Kada ku yi annabci” in ji annabawansu. “Kada ku yi annabci game da waɗannan abubuwa; abin kunya ba zai same mu ba.”
7 Shall it be said, O house of Jacob, “Is the LORD’s Spirit angry? Are these his doings? Don’t my words do good to him who walks blamelessly?”
Daidai ne a ce, ya gidan Yaƙub, “Ruhun Ubangiji yana fushi ne? Yana yin irin waɗannan abubuwa?” “Ashe, maganata ba tă amfane wanda ayyukansa suke daidai ba?
8 But lately my people have risen up as an enemy. You strip the robe and clothing from those who pass by without a care, returning from battle.
Ba da daɗewa ba mutanena sun tashi kamar magabci. Kun tuɓe riga mai tsada daga waɗanda suke wucewa ba tare da kun damu ba, sai ka ce mutanen da suke komowa daga yaƙi.
9 You drive the women of my people out from their pleasant houses; from their young children you take away my blessing forever.
Kun kori matan mutanena daga gidajensu masu daɗi. Kuka kawar da albarkata har abada daga wurin’ya’yansu.
10 Arise, and depart! For this is not your resting place, because of uncleanness that destroys, even with a grievous destruction.
Ku tafi, ku ba ni wuri! Gama wannan ba wurin hutunku ba ne, gama ya ƙazantu, ya zama kangon da ya wuce gyara.
11 If a man walking in a spirit of falsehood lies, saying, “I will prophesy to you of wine and of strong drink,” he would be the prophet of this people.
In maƙaryaci da mazambaci ya zo ya ce, ‘Zan yi muku annabci ku sami wadataccen ruwan inabi da barasa,’ zai dai zama annabin da ya dace da wannan mutane ne!
12 I will surely assemble all of you, Jacob. I will surely gather the remnant of Israel. I will put them together as the sheep of Bozrah, as a flock in the middle of their pasture. They will swarm with people.
“Tabbatacce zan tattara ku duka, ya gidan Yaƙub; zan tattara ku raguwar Isra’ila. Zan kawo su wuri ɗaya kamar tumaki a cikin garke, kamar garke a wajen kiwonsa; wurin zai cika da mutane.
13 He who breaks open the way goes up before them. They break through the gate, and go out. Their king passes on before them, with the LORD at their head.
Wanda ya fasa ƙofa ya buɗe, shi zai haura yă yi musu jagora, za su fashe bangon su fita. Sarkinsu zai wuce gabansu, Ubangiji kuma zai kasance a gaba.”

< Micah 2 >