< Leviticus 17 >

1 The LORD spoke to Moses, saying,
Ubangiji ya ce wa Musa,
2 “Speak to Aaron, and to his sons, and to all the children of Israel, and say to them, ‘This is the thing which the LORD has commanded:
“Yi magana da Haruna da’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji ya umarta.
3 Whatever man there is of the house of Israel who kills a bull, or lamb, or goat in the camp, or who kills it outside the camp,
Duk mutumin Isra’ilan da ya yanka sa, ɗan rago ko akuya a sansani ko waje da shi
4 and hasn’t brought it to the door of the Tent of Meeting to offer it as an offering to the LORD before the LORD’s tabernacle: blood shall be imputed to that man. He has shed blood. That man shall be cut off from among his people.
a maimakon kawo shi a matsayin hadaya ga Ubangiji a gaban tabanakul na Ubangiji, za a ɗauki wannan mutum a matsayi mai laifin zub da jini, ya zub da jini, kuma dole a raba shi da mutanensa.
5 This is to the end that the children of Israel may bring their sacrifices, which they sacrifice in the open field, that they may bring them to the LORD, to the door of the Tent of Meeting, to the priest, and sacrifice them for sacrifices of peace offerings to the LORD.
Wannan ya zama haka saboda Isra’ilawa su kawo wa Ubangiji hadayun da suke yi a filaye. Dole su kawo su ga firist, wato, ga Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, su miƙa su a matsayin hadayun salama.
6 The priest shall sprinkle the blood on the LORD’s altar at the door of the Tent of Meeting, and burn the fat for a pleasant aroma to the LORD.
Firist zai yayyafa jinin a bagaden Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, yă kuma ƙone kitsen kamar ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.
7 They shall no more sacrifice their sacrifices to the goat idols, after which they play the prostitute. This shall be a statute forever to them throughout their generations.’
Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare su wa tsararraki masu zuwa.’
8 “You shall say to them, ‘Any man there is of the house of Israel, or of the strangers who live as foreigners among them, who offers a burnt offering or sacrifice,
“Faɗa musu, ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko wani baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka
9 and doesn’t bring it to the door of the Tent of Meeting to sacrifice it to the LORD, that man shall be cut off from his people.
kuma bai kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă miƙa shi ga Ubangiji ba, dole a raba wannan mutum da mutanensa.
10 “‘Any man of the house of Israel, or of the strangers who live as foreigners among them, who eats any kind of blood, I will set my face against that soul who eats blood, and will cut him off from among his people.
“‘Duk mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya ci wani jini, zan yi gāba da wannan mutum wanda ya ci jinin, za a kuma raba shi da mutanensa.
11 For the life of the flesh is in the blood. I have given it to you on the altar to make atonement for your souls; for it is the blood that makes atonement by reason of the life.
Gama ran halitta yana a cikin jinin, kuma na ba da shi gare ku don kafara a kan bagade, jini ne yake kafara saboda ran mutum.
12 Therefore I have said to the children of Israel, “No person among you may eat blood, nor may any stranger who lives as a foreigner among you eat blood.”
Saboda haka na ce wa Isra’ilawa, “Babu waninku da zai ci jini, babu wani baƙon da yake zama a cikinku da zai ci jini.”
13 “‘Whatever man there is of the children of Israel, or of the strangers who live as foreigners among them, who takes in hunting any animal or bird that may be eaten, he shall pour out its blood, and cover it with dust.
“‘Duk wani mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinku wanda ya ji wa wani dabba ko tsuntsu wanda ake ci ciwo, dole yă tsiyaye jinin yă rufe shi da ƙasa,
14 For as to the life of all flesh, its blood is with its life. Therefore I said to the children of Israel, “You shall not eat the blood of any kind of flesh; for the life of all flesh is its blood. Whoever eats it shall be cut off.”
domin ran kowace halitta yana cikin jini. Shi ya sa na ce wa Isra’ilawa, “Kada ku ci jinin wani halitta, domin ran kowace halitta yana cikin jinin; duk wanda ya ci shi dole a fid da shi.”
15 “‘Every person that eats what dies of itself, or that which is torn by animals, whether he is native-born or a foreigner, shall wash his clothes, and bathe himself in water, and be unclean until the evening. Then he shall be clean.
“‘Kowa, ko haifaffe ɗan ƙasa ko baƙo, da ya ci wani abin da aka sami a mace, ko naman jeji ya yayyage, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma; sa’an nan zai tsarkake.
16 But if he doesn’t wash them, or bathe his flesh, then he shall bear his iniquity.’”
Amma in bai wanke rigunansa ya kuma yi wanka ba, alhaki zai kasance a kansa.’”

< Leviticus 17 >