< Job 31 >

1 “I made a covenant with my eyes; how then should I look lustfully at a young woman?
“Na yi alkawari da idanuna kada su dubi budurwa da muguwar sha’awa.
2 For what is the portion from God above, and the heritage from the Almighty on high?
Gama mene ne rabon mutum daga Allah a sama, gādonsa daga Maɗaukaki a sama?
3 Is it not calamity to the unrighteous, and disaster to the workers of iniquity?
Ba masifa ba ne domin mugaye, hallaka kuma ga waɗanda suka yi ba daidai ba?
4 Doesn’t he see my ways, and count all my steps?
Bai ga hanyoyina ba ne bai ƙirga kowace takawata ba?
5 “If I have walked with falsehood, and my foot has hurried to deceit
“In da na yi tafiya cikin rashin gaskiya ko kuma ƙafata ta yi sauri zuwa yin ƙarya,
6 (let me be weighed in an even balance, that God may know my integrity);
Bari Allah yă auna a kan ma’auni na gaskiya zai kuma san cewa ni marar laifi ne.
7 if my step has turned out of the way, if my heart walked after my eyes, if any defilement has stuck to my hands,
In takawata ta kauce daga hanya, in zuciyata ta bi abin da idanuna ke so, ko kuma in hannuwana suna da laifi;
8 then let me sow, and let another eat. Yes, let the produce of my field be rooted out.
bari waɗansu su ci abin da na shuka, kuma bari a tuge amfanin gonata.
9 “If my heart has been enticed to a woman, and I have laid wait at my neighbor’s door,
“In sha’awar mace ya shiga mini zuciya, ko kuma na laɓe a ƙofar maƙwabcina,
10 then let my wife grind for another, and let others sleep with her.
sai matata ta niƙa hatsin wani kuma waɗansu maza su kwana da ita.
11 For that would be a heinous crime. Yes, it would be an iniquity to be punished by the judges,
Gama wannan zai zama abin kunya, zunubin da za a yi shari’a a kai.
12 for it is a fire that consumes to destruction, and would root out all my increase.
Wuta ce take ƙuna har ta hallakar; za tă cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.
13 “If I have despised the cause of my male servant or of my female servant, when they contended with me,
“In da na danne wa bayina maza da mata hakkinsu, sa’ad da suke da damuwa da ni,
14 what then will I do when God rises up? When he visits, what will I answer him?
me zan yi lokacin da Allah ya tuhume ni? Me zan ce lokacin da ya tambaye ni?
15 Didn’t he who made me in the womb make him? Didn’t one fashion us in the womb?
Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba? Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba?
16 “If I have withheld the poor from their desire, or have caused the eyes of the widow to fail,
“In na hana wa matalauta abin da suke so, ko kuma in sa idanun gwauruwa su yi nauyi don kuka,
17 or have eaten my morsel alone, and the fatherless has not eaten of it
in na ajiye burodina don kaina kaɗai, ban kuwa ba wa marayu abinci sa’ad da suke jin yunwa,
18 (no, from my youth he grew up with me as with a father, I have guided her from my mother’s womb);
amma tun suna tasowa na lura da su, kamar yadda mahaifi zai lura da ɗa, kuma tun da aka haife ni ina lura da gwauruwa.
19 if I have seen any perish for want of clothing, or that the needy had no covering;
In da na ga wani yana mutuwa don rashin sutura, ko wani mai bukata da ba shi da riga,
20 if his heart hasn’t blessed me, if he hasn’t been warmed with my sheep’s fleece;
kuma zuciyarsa ba tă gode mini ba don na yi masa sutura da gashin tumakina,
21 if I have lifted up my hand against the fatherless, because I saw my help in the gate;
in na ɗaga hannuna don in cuci maraya, domin na san in na faɗa za a ji ni a wurin masu shari’a,
22 then let my shoulder fall from the shoulder blade, and my arm be broken from the bone.
bari hannuna yă guntule daga kafaɗata, bari yă tsinke daga inda aka haɗa shi.
23 For calamity from God is a terror to me. Because of his majesty, I can do nothing.
Gama ina jin tsoron hallaka daga Allah, kuma domin tsoron ɗaukakarsa ba zan iya yin waɗannan abubuwa ba.
24 “If I have made gold my hope, and have said to the fine gold, ‘You are my confidence;’
“In na dogara ga zinariya ko kuma na ce wa zallan zinariya, ‘Gare ki nake dogara,’
25 If I have rejoiced because my wealth was great, and because my hand had gotten much;
in na yi fahariya don yawan dukiyata, arzikin da hannuwana suka samu.
26 if I have seen the sun when it shined, or the moon moving in splendor,
In na dubi rana cikin haskenta, ko kuma wata yana tafiyarsa,
27 and my heart has been secretly enticed, and my hand threw a kiss from my mouth;
zuciyata ta jarrabtu gare su a ɓoye, hannuna kuma ya sumbace su.
28 this also would be an iniquity to be punished by the judges, for I would have denied the God who is above.
Waɗannan ma za su zama zunubin da za a shari’anta ke nan don zai zama na yi wa Allah na sama rashin aminci.
29 “If I have rejoiced at the destruction of him who hated me, or lifted up myself when evil found him
“In na yi murna domin mugun abu ya faru da maƙiyina; ko kuma domin wahala ta same shi,
30 (I have certainly not allowed my mouth to sin by asking his life with a curse);
ban bar bakina yă yi zunubi ta wurin la’anta shi ba,
31 if the men of my tent have not said, ‘Who can find one who has not been filled with his meat?’
in mutanen gidana ba su taɓa cewa, ‘Wane ne bai ƙoshi da naman Ayuba ba?’
32 (the foreigner has not camped in the street, but I have opened my doors to the traveler);
Ba baƙon da ya taɓa kwana a titi, gama koyaushe ƙofata tana buɗe domin matafiya,
33 if like Adam I have covered my transgressions, by hiding my iniquity in my heart,
in na ɓoye zunubina yadda mutane suke yi, ta wurin ɓoye laifina a cikin zuciyata,
34 because I feared the great multitude, and the contempt of families terrified me, so that I kept silence, and didn’t go out of the door—
domin ina tsoron taron mutane kuma ina tsoron wulaƙancin da dangina za su yi mini, sai na yi shiru kuma ban fita waje ba.
35 oh that I had one to hear me! Behold, here is my signature! Let the Almighty answer me! Let the accuser write my indictment!
(“Kash, da ina da wanda zai ji ni! Na sa hannu ga abin da na faɗa don kāre kaina, bari Maɗaukaki yă amsa mini; bari mai tuhumata da laifi yă yi ƙarata a rubuce.
36 Surely I would carry it on my shoulder, and I would bind it to me as a crown.
Ba shakka sai in ɗora a kafaɗata, zan aza a kaina kamar rawani.
37 I would declare to him the number of my steps. I would go near to him like a prince.
Zan ba shi lissafin duk abin da na taɓa yi; zan zo gabansa kamar ɗan sarki.)
38 If my land cries out against me, and its furrows weep together;
“In ƙasata tana kuka da ni kunyoyinta duk sun cika da hawaye,
39 if I have eaten its fruits without money, or have caused its owners to lose their life,
in na kwashe amfaninta ban biya ba ko kuma na kashe masu ita,
40 let briers grow instead of wheat, and stinkweed instead of barley.” The words of Job are ended.
bari ƙaya ta fito a maimakon alkama ciyawa kuma a maimakon sha’ir.” Maganar Ayuba ta ƙare.

< Job 31 >