< Isaiah 31 >

1 Woe to those who go down to Egypt for help, and rely on horses, and trust in chariots because they are many, and in horsemen because they are very strong, but they don’t look to the Holy One of Israel, and they don’t seek the LORD!
Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako, waɗanda suke dogara ga dawakai, waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu, amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila, ko ya nemi taimako daga Ubangiji.
2 Yet he also is wise, and will bring disaster, and will not call back his words, but will arise against the house of the evildoers, and against the help of those who work iniquity.
Shi ma yana da hikima kuma zai iya kawo masifa; ba ya janye kalmominsa. Zai yi gāba da gidan mugu, gāba da waɗanda suke taimakon masu aikata mugunta.
3 Now the Egyptians are men, and not God; and their horses flesh, and not spirit. When the LORD stretches out his hand, both he who helps shall stumble, and he who is helped shall fall, and they all shall be consumed together.
Amma Masarawa mutane ne ba Allah ba; dawakansu nama da jini ne ba ruhu ba. Sa’ad da Ubangiji ya miƙa hannunsa, shi da yake taimako zai yi tuntuɓe shi da aka taimaka zai fāɗi; dukansu biyu za su hallaka tare.
4 For the LORD says to me, “As the lion and the young lion growling over his prey, if a multitude of shepherds is called together against him, will not be dismayed at their voice, nor abase himself for their noise, so the LORD of Hosts will come down to fight on Mount Zion and on its heights.
Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Kamar yadda zaki kan yi ruri babban zaki a kan abin da ya yi farauta, kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyaya sun taru wuri ɗaya a kansa, ba zai jijjigu ta wurin ihunsu ba ko ya damu da kiraye-kirayensu, ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai sauko don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa.
5 As birds hovering, so the LORD of Hosts will protect Jerusalem. He will protect and deliver it. He will pass over and preserve it.”
Kamar tsuntsaye masu shawagi a sama haka Ubangiji Maɗaukaki zai kiyaye Urushalima; zai kāre ta ya kuma fanshe ta, zai ‘ƙetare’ ta ya kuma kuɓutar da ita.”
6 Return to him from whom you have deeply revolted, children of Israel.
Ku dawo gare shi ku da kuka yi masa babban tayarwa, ya Isra’ilawa.
7 For in that day everyone shall cast away his idols of silver and his idols of gold—sin which your own hands have made for you.
Gama a wannan rana kowannenku zai ƙi gumakan azurfa da zinariya da hannuwanku masu zunubi suka yi.
8 “The Assyrian will fall by the sword, not of man; and the sword, not of mankind, shall devour him. He will flee from the sword, and his young men will become subject to forced labor.
“Za a karkashe Assuriyawa da takobin da ba na yin mutum ba; takobi, da ba na yin mutum ba, zai cinye. Za su gudu daga takobi za a kuma sa samarinsu aikin dole.
9 His rock will pass away by reason of terror, and his princes will be afraid of the banner,” says the LORD, whose fire is in Zion, and his furnace in Jerusalem.
Kagararsu za tă fāɗi saboda razana; da ganin matsayin yaƙin, shugabannin yaƙinsu za su firgita,” in ji Ubangiji, wanda wutarsa tana a Sihiyona, wanda matoyarsa tana a Urushalima.

< Isaiah 31 >