< Ecclesiastes 6 >

1 There is an evil which I have seen under the sun, and it is heavy on men:
Na ga wani mugun abu a duniya, ya kuma nawaita wa mutane ƙwarai.
2 a man to whom God gives riches, wealth, and honor, so that he lacks nothing for his soul of all that he desires, yet God gives him no power to eat of it, but an alien eats it. This is vanity, and it is an evil disease.
Allah yakan ba mutum dukiya, da wadata da kuma girma, don kada yă rasa abin da ransa yake so, amma Allah bai ba shi zarafin more su ba, a maimakon haka ma sai baƙo ne yă more su. Wannan ba shi da amfani, mugun abu ne ƙwarai.
3 If a man fathers a hundred children, and lives many years, so that the days of his years are many, but his soul is not filled with good, and moreover he has no burial, I say that a stillborn child is better than he;
Mutum zai iya kasance da’ya’ya ɗari, yă kuma yi shekaru masu yawa; duk da haka kome daɗewarsa, in bai more wadatarsa ba, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba, na ce, gara wanda aka haife shi gawa.
4 for it comes in vanity, and departs in darkness, and its name is covered with darkness.
Haihuwa ba tă amfane wanda aka haifa gawa ba, gama ya zo daga duhu ya koma duhu inda aka manta da shi.
5 Moreover it has not seen the sun nor known it. This has rest rather than the other.
Ko da yake bai ga hasken rana ba, bai kuma san kome ba, duk da haka ya dai huta, fiye da mutumin da bai more wa ransa ba,
6 Yes, though he live a thousand years twice told, and yet fails to enjoy good, don’t all go to one place?
ko da ya yi shekara dubu biyu amma bai more wadatarsa ba. Ba wuri ɗaya dukansu biyu za su tafi ba?
7 All the labor of man is for his mouth, and yet the appetite is not filled.
Dukan ƙoƙarin da mutum yake yi, yana yi ne domin bakinsa, duk da haka bai taɓa gamsar da abin da yake marmari.
8 For what advantage has the wise more than the fool? What has the poor man, that knows how to walk before the living?
Da me mai hikima ya fi wawa? Wace riba ce matalauci yakan samu don yă iya zama da mutane?
9 Better is the sight of the eyes than the wandering of the desire. This also is vanity and a chasing after wind.
Gara abin da ido ya gani da kwaɗayin da bai sami biyan bukata ba. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
10 Whatever has been, its name was given long ago; and it is known what man is; neither can he contend with him who is mightier than he.
Duk abin da ya kasance, to, yana da suna, kuma duk abin da mutum yake, an riga an sani. Ba mutumin da zai iya ƙarawa da wanda ya fi shi ƙarfi.
11 For there are many words that create vanity. What does that profit man?
Yadda yawan magana take haka ƙarancin amfaninta, yaya wannan zai amfane wani?
12 For who knows what is good for man in life, all the days of his vain life which he spends like a shadow? For who can tell a man what will be after him under the sun?
Gama wa ya san abin da ya fi dacewa ga mutum a’yan kwanakinsa marasa amfani da sukan wuce kamar inuwa? Wa kuma zai iya faɗa masa abin da zai faru a duniya bayan ya rasu?

< Ecclesiastes 6 >