< 2 Samuel 9 >

1 David said, “Is there yet any who is left of Saul’s house, that I may show him kindness for Jonathan’s sake?”
Wata rana Dawuda ya yi tambaya ya ce, “Akwai wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu wanda zan nuna masa alheri saboda Yonatan?”
2 There was of Saul’s house a servant whose name was Ziba, and they called him to David; and the king said to him, “Are you Ziba?” He said, “I am your servant.”
To, akwai wani bawa na gidan Shawulu mai suna Ziba. Sai aka kira shi yă bayyana a gaban Dawuda, sarki ya ce masa, “Kai ne Ziba?” Sai ya ce, “I, ni ne, ranka yă daɗe.”
3 The king said, “Is there not yet any of Saul’s house, that I may show the kindness of God to him?” Ziba said to the king, “Jonathan still has a son, who is lame in his feet.”
Sa’an nan sarki ya yi tambaya ya ce, “Babu wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu don in nuna masa alherin Allah?” Ziba ya ce wa sarki, “Har yanzu akwai ɗan Yonatan da ya rage, sai dai shi gurgu ne a dukan ƙafafu.”
4 The king said to him, “Where is he?” Ziba said to the king, “Behold, he is in the house of Machir the son of Ammiel, in Lo Debar.”
Sarki ya ce, “Ina yake?” Ziba ya ce, “Yana a gidan Makir ɗan Ammiyel a Lo Debar.”
5 Then King David sent and brought him out of the house of Machir the son of Ammiel, from Lo Debar.
Saboda haka Sarki Dawuda ya umarta aka kawo shi daga gidan Makir ɗan Ammiyel, daga Lo Debar.
6 Mephibosheth, the son of Jonathan, the son of Saul, came to David, fell on his face, and showed respect. David said, “Mephibosheth?” He answered, “Behold, your servant!”
Sa’ad da Mefiboshet ɗan Yonatan, ɗan Shawulu, ya zo wurin Dawuda, sai ya rusuna har ƙasa ya yi gaisuwar bangirma. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!” Shi kuwa ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, ga ni, bawanka.”
7 David said to him, “Don’t be afraid, for I will surely show you kindness for Jonathan your father’s sake, and will restore to you all the land of Saul your father. You will eat bread at my table continually.”
Dawuda ya ce, “Kada ka ji tsoro, gama tabbatacce zan nuna maka alheri saboda mahaifinka Yonatan. Zan mayar maka da dukan ƙasar da take ta kakanka Shawulu, kullum kuma za ka ci a teburina.”
8 He bowed down, and said, “What is your servant, that you should look at such a dead dog as I am?”
Mefiboshet ya rusuna ya ce, “Ni ne wa har da za ka kula da ni? Ai! Ni bawanka ne da bai ma fi mataccen kare daraja ba.”
9 Then the king called to Ziba, Saul’s servant, and said to him, “All that belonged to Saul and to all his house I have given to your master’s son.
Sai sarki ya kira Ziba bawan Shawulu, ya ce masa, “Na ba wa jikan maigidanka kome da yake na Shawulu da iyalinsa
10 Till the land for him—you, your sons, and your servants. Bring in the harvest, that your master’s son may have bread to eat; but Mephibosheth your master’s son will always eat bread at my table.” Now Ziba had fifteen sons and twenty servants.
Kai da’ya’yanka maza da bayinka za ku riƙa yin masa noma, ku kuma kawo hatsin, don jikan maigidanka yă sami abinci. Mefiboshet kuma, jikan maigidanka, zai riƙa ci a teburina.” (Ziba kuwa yana da’ya’ya maza goma sha biyar da kuma bayi ashirin.)
11 Then Ziba said to the king, “According to all that my lord the king commands his servant, so your servant will do.” So Mephibosheth ate at the king’s table like one of the king’s sons.
Sai Ziba ya ce wa sarki, “Bawanka zai aikata dukan abin da ranka yă daɗe sarki, ya umarce shi.” Saboda haka Mefiboshet ya riƙa ci a teburin Dawuda kamar sauran’ya’yan sarki.
12 Mephibosheth had a young son, whose name was Mica. All who lived in Ziba’s house were servants to Mephibosheth.
Mefiboshet yana da wani ƙaramin ɗa sunansa Mika, dukan iyalin gidan Ziba kuwa bayin Mefiboshet ne.
13 So Mephibosheth lived in Jerusalem, for he ate continually at the king’s table. He was lame in both his feet.
Mefiboshet ya zauna a Urushalima, gama kullum yana ci a teburin sarki, shi kuwa gurgu ne a dukan ƙafafu.

< 2 Samuel 9 >