< 1 Chronicles 28 >

1 David assembled all the princes of Israel, the princes of the tribes, the captains of the companies who served the king by division, the captains of thousands, the captains of hundreds, and the rulers over all the substance and possessions of the king and of his sons, with the officers and the mighty men, even all the mighty men of valor, to Jerusalem.
Dawuda ya sa aka kira dukan shugabannin Isra’ila su taru a Urushalima, shugabannin kabilu, manyan hafsoshin ɓangarorin hidimar sarki, manyan hafsoshin dubu-dubu da manyan hafsoshin ɗari-ɗari, da kuma shugabanni masu lura da dukan mallaka da dabbobin da suke na sarki da kuma’ya’yansa maza, tare da fadawa, jarumawa da kuma dukan mayaƙa masu kwarjini.
2 Then David the king stood up on his feet and said, “Hear me, my brothers and my people! As for me, it was in my heart to build a house of rest for the ark of the LORD’s covenant, and for the footstool of our God; and I had prepared for the building.
Sarki Dawuda ya miƙe tsaye ya ce, “Ku saurare ni,’yan’uwana da kuma mutanena. Na yi niyya in gina gida a matsayin wurin hutu domin akwatin alkawarin Ubangiji, domin zatin Allahnmu, na kuma yi shiri don in gina shi.
3 But God said to me, ‘You shall not build a house for my name, because you are a man of war and have shed blood.’
Amma Allah ya ce mini, ‘Ba za ka gina gida domin Sunana ba, saboda kai mayaƙi ne ka kuma zub da jini.’
4 However the LORD, the God of Israel, chose me out of all the house of my father to be king over Israel forever. For he has chosen Judah to be prince; and in the house of Judah, the house of my father; and among the sons of my father he took pleasure in me to make me king over all Israel.
“Duk da haka Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya zaɓe ni daga dukan iyalina don in zama sarki bisa Isra’ila har abada. Ya zaɓi Yahuda a matsayin shugaba, kuma daga gidan Yahuda ya zaɓi iyalina, daga’ya’yan mahaifina maza kuwa ya gamsu ya mai da ni sarki bisa dukan Isra’ila.
5 Of all my sons (for the LORD has given me many sons), he has chosen Solomon my son to sit on the throne of the LORD’s kingdom over Israel.
Cikin dukan’ya’yana maza, Ubangiji kuwa ya ba ni su da yawa, ya zaɓi ɗana Solomon yă zauna a kujerar mulkin Ubangiji a bisa Isra’ila.
6 He said to me, ‘Solomon, your son, shall build my house and my courts; for I have chosen him to be my son, and I will be his father.
Ya ce mini, ‘Solomon ɗanka shi ne wanda zai gina gidana da filayen da suke kewaye da shi, gama na zaɓe shi yă zama ɗana, ni kuma zan zama mahaifinsa.
7 I will establish his kingdom forever if he continues to do my commandments and my ordinances, as it is today.’
Zan kafa mulkinsa har abada in bai kauce ga kiyaye umarnaina da dokokina ba, yadda ake yi a wannan lokaci.’
8 Now therefore, in the sight of all Israel, the LORD’s assembly, and in the audience of our God, observe and seek out all the commandments of the LORD your God, that you may possess this good land, and leave it for an inheritance to your children after you forever.
“Saboda haka yanzu ina umartanku a gaban dukan Isra’ila da na taron jama’ar Ubangiji, da kuma a kunnuwan Allahnmu. Ku yi hankali ku kiyaye dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki wannan kyakkyawar ƙasa ku kuma bar wa zuriyarku gādo har abada.
9 You, Solomon my son, know the God of your father, and serve him with a perfect heart and with a willing mind; for the LORD searches all hearts, and understands all the imaginations of the thoughts. If you seek him, he will be found by you; but if you forsake him, he will cast you off forever.
“Kai kuma ɗana Solomon, ka san Allah na mahaifinka, ka kuma yi masa hidima da dukan zuciya da kuma yardar rai, gama Ubangiji yana binciken zuciya, yana kuma gane dukan aniyar tunani. In ka neme shi, za ka same shi; amma in ka yashe shi, zai ƙi ka har abada.
10 Take heed now, for the LORD has chosen you to build a house for the sanctuary. Be strong, and do it.”
Ka lura fa, gama Ubangiji ya zaɓe ka don ka gina haikali a matsayin wuri mai tsarki. Ka yi ƙarfin hali ka kuma yi aiki.”
11 Then David gave to Solomon his son the plans for the porch of the temple, for its houses, for its treasuries, for its upper rooms, for its inner rooms, for the place of the mercy seat;
Sa’an nan Dawuda ya ba ɗansa Solomon tsari domin shirayin haikalin, gine-ginensa, ɗakunan ajiyarsa, ɓangarorin bisansa, ɗakunan cikinsa da kuma wurin kafara.
12 and the plans of all that he had by the Spirit, for the courts of the LORD’s house, for all the surrounding rooms, for the treasuries of God’s house, and for the treasuries of the dedicated things;
Ya ba shi tsarin dukan abin da Ruhu ya sa a zuciyarsa saboda filayen haikalin Ubangiji da ɗakunan kewaye, da ma’ajin haikalin Allah da kuma baitulmali na kayayyakin da aka keɓe.
13 also for the divisions of the priests and the Levites, for all the work of the service of the LORD’s house, and for all the vessels of service in the LORD’s house—
Ya ba shi tsari game ɓangarori na firistoci da Lawiyawa, da game dukan aikin hidima a cikin haikalin Ubangiji, da kuma game da dukan kayayyakin da za a yi amfani da su a hidima.
14 of gold by weight for the gold for all vessels of every kind of service, for all the vessels of silver by weight, for all vessels of every kind of service;
Ya kimanta yawan zinariya don dukan kayayyakin zinariyar da za a yi amfani a kowane irin hidima, da yawan azurfa don dukan kayayyakin azurfan da za a yi amfani a kowace irin hidima.
15 by weight also for the lamp stands of gold, and for its lamps, of gold, by weight for every lamp stand and for its lamps; and for the lamp stands of silver, by weight for every lamp stand and for its lamps, according to the use of every lamp stand;
Da yawan zinariya don wurin ajiye fitilan fitilu da fitilunsu, da yawan zinariyan da za a yi amfani don kowace fitila da wurin ajiye fitilanta; da kuma yawan azurfa don kowane wurin ajiye fitila da fitilunsa bisa ga yadda za a yi amfani da kowane wurin ajiye fitila;
16 and the gold by weight for the tables of show bread, for every table; and silver for the tables of silver;
yawan zinariya don kowane tebur saboda burodi mai tsaki; da kuma yawan azurfa saboda teburin azurfa;
17 and the forks, the basins, and the cups, of pure gold; and for the golden bowls by weight for every bowl; and for the silver bowls by weight for every bowl;
yawan zinariya zalla, don cokula masu yatsu, kwanonin yayyafawa ruwa da kuma tuluna; yawan zinariya don kowane kwanon zinariya; yawan azurfa don kowane kwanon azurfa;
18 and for the altar of incense, refined gold by weight; and gold for the plans for the chariot, and the cherubim that spread out and cover the ark of the LORD’s covenant.
da kuma yawan tacecciyar zinariya don bagaden turare. Ya kuma ba shi tsari don keken yaƙi, wato, kerubobin zinariyar da suka miƙe fikafikansu suka inuwantar da akwatin alkawarin Ubangiji.
19 “All this”, David said, “I have been made to understand in writing from the LORD’s hand, even all the works of this pattern.”
Dawuda ya ce, “Dukan wannan, ina da shi a rubuce daga hannun Ubangiji zuwa gare ni, ya kuma ba ni ganewa cikin dukan tsarin fasalin, filla-filla.”
20 David said to Solomon his son, “Be strong and courageous, and do it. Don’t be afraid, nor be dismayed, for the LORD God, even my God, is with you. He will not fail you nor forsake you, until all the work for the service of the LORD’s house is finished.
Dawuda ya kuma ce wa Solomon ɗansa, “Ka yi ƙarfin hali, ka kuma yi aikin. Kada ka ji tsoro ko ka fid da zuciya, gama Ubangiji Allah, Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ko yă yashe ka ba, sai an gama dukan aikin saboda hidimar haikalin Ubangiji.
21 Behold, there are the divisions of the priests and the Levites for all the service of God’s house. Every willing man who has skill for any kind of service shall be with you in all kinds of work. Also the captains and all the people will be entirely at your command.”
Sassan firistoci da na Lawiyawa suna a shirye domin dukan aiki a haikalin Allah, kuma kowane gwani mai niyya a kowace sana’a, zai taimake ka a cikin dukan aikin. Shugabanni da dukan mutane za su yi biyayya da kowane umarninka.”

< 1 Chronicles 28 >