< Romans 4 >

1 What then will we say that Abraham, our forefather, has found according to the flesh?
Me kenan zamu ce game da Ibrahim, kakanmu a jiki, me ya samu?
2 For if Abraham was justified by works, he has something to boast about, but not towards God.
Domin idan Ibrahim ya sami kubutarwa ta wurin ayuka, ai da ya sami dalilin fahariya, amma ba a gaban Allah ba.
3 For what does the Scripture say? “Abraham believed God, and it was accounted to him for righteousness.”
Kuma fa me nassi ke fadi? “Ibrahim ya bada gaskiya ga Allah, sai aka lisafta ta adalci gare shi.”
4 Now to him who works, the reward is not counted as grace, but as something owed.
Yanzu fa shi dake yin ayyuka, ladansa ba a lisafta shi alheri ba ne, amma abun da ke nasa.
5 But to him who doesn’t work, but believes in him who justifies the ungodly, his faith is accounted for righteousness.
Amma kuma shi da bai da ayyuka kuma maimakon haka ya gaskanta ga wanda ke kubutar da masu zunubai, bangaskiyarsa an lisafta ta a misalin adalci.
6 Even as David also pronounces blessing on the man to whom God counts righteousness apart from works:
Dauda ya yi furcin albarka bisa mutumin da Allah ya lisafta mai adalci da rashin ayyuka.
7 “Blessed are they whose iniquities are forgiven, whose sins are covered.
Sai ya ce, “Masu albarka ne wadanda aka yafe laifofinsu, kuma wadanda zunubansu a rufe suke.
8 Blessed is the man whom the Lord will by no means charge with sin.”
Mai albarka ne mutumin da ko kadan Ubangiji ba zaya lisafta zunubin sa ba.”
9 Is this blessing then pronounced only on the circumcised, or on the uncircumcised also? For we say that faith was accounted to Abraham for righteousness.
To albarkar da aka fadi ko a bisansu wadanda aka yi wa kaciya ne kadai, ko kuwa a bisan su ma marasa kaciya? Domin mun yi furcin, “Bangaskiyar Ibrahim an lisafta ta adalci ce agare shi.”
10 How then was it counted? When he was in circumcision, or in uncircumcision? Not in circumcision, but in uncircumcision.
Yaya aka lisafta ta? Bayan Ibrahim ya yi kaciya, ko kuwa a rashin kaciya? Ba a cikin kaciya ba, amma a rashin kaciya.
11 He received the sign of circumcision, a seal of the righteousness of the faith which he had while he was in uncircumcision, that he might be the father of all those who believe, though they might be in uncircumcision, that righteousness might also be accounted to them.
Ibrahim ya amshi alamar kaciya. Wannan shi ne hatimin adalcin bangaskiyar da ya ke da ita tun cikin rashin kaciyarsa. Albarkacin wannan alama ce, ta sa shi ya zama uban dukkan wadanda suka badagaskiya, ko da shike ba su da kaciya. Wato ma'ana, adalci za a lisafta masu.
12 He is the father of circumcision to those who not only are of the circumcision, but who also walk in the steps of that faith of our father Abraham, which he had in uncircumcision.
Wannan kuma yana da ma'anar cewa Ibrahim ya zama uban kaciya ga wadanda suka fito ba domin masu kaciya kadai ba, amma kuma domin wadanda ke biyo matakin ubanmu Ibrahim. Kuma wannan itace bangaskiyar da ya ke da ita a rashin kaciya.
13 For the promise to Abraham and to his offspring that he would be heir of the world wasn’t through the law, but through the righteousness of faith.
Domin ba ta wurin shari'a aka bada alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim da zuriyarsa ba, wannan alkawarin da ya ce zasu gaji duniya. Maimako, a ta wurin adalcin bangaskiya ne.
14 For if those who are of the law are heirs, faith is made void, and the promise is made of no effect.
Domin idan su da ke na shari'a magada ne, bangaskiya bata da komai, kuma alkawarin an wofintar da shi kenan.
15 For the law produces wrath; for where there is no law, neither is there disobedience.
Domin shari'a ta kan jawo fushi, amma ta wurin rashin shari'a, babu karya umarni.
16 For this cause it is of faith, that it may be according to grace, to the end that the promise may be sure to all the offspring, not to that only which is of the law, but to that also which is of the faith of Abraham, who is the father of us all.
Saboda wannan dalili haka ta faru ta wurin bangaskiya, domin ya zama bisa ga alheri. Kamar haka, alkawarin ya tabbata ga dukkan zuriya. Kuma wannan zuriya ba zata kunshi wadanda suke da sanin shari'a ba kadai, har ma da wadanda ke daga bangaskiyar Ibrahim. Saboda shi ne uban dukkan kowa,
17 As it is written, “I have made you a father of many nations.” This is in the presence of him whom he believed: God, who gives life to the dead, and calls the things that are not, as though they were.
kamar yadda aka rubuta, “Na maishe ka uba ga kasashe masu yawa.” Ibrahim na gaban aminin sa, wato, Allah, mai bada rai ga mattatu kuma ya kan kira abubuwan da basu da rai su kuma kasance.
18 Against hope, Abraham in hope believed, to the end that he might become a father of many nations, according to that which had been spoken, “So will your offspring be.”
Duk da halin da ke a bayyane, Ibrahim ya gaskata ga Allah kai tsaye game da abubuwan da ke nan gaba. Sai ya zama uba ga kasashe masu yawa, kamar yadda aka ambata, “... Haka zuriyarka zata kasance.”
19 Without being weakened in faith, he didn’t consider his own body, already having been worn out, (he being about a hundred years old), and the deadness of Sarah’s womb.
Ba ya karaya a bangaskiya ba. Ibrahim ya yarda da cewa jikinsa ya rigaya ya tsufa (shekarun sa na misalin dari). Ya kuma yarda da cewa mahaifar Saratu bata iya bada 'ya'ya ba.
20 Yet, looking to the promise of God, he didn’t waver through unbelief, but grew strong through faith, giving glory to God,
Amma domin alkawarin Allah, Ibrahim bai ji nauyin rashin bangaskiya ba. Maimakon haka, ya sami karfafawa a bangaskiyarsa sai ya daukaka Allah.
21 and being fully assured that what he had promised, he was also able to perform.
Ya na da cikakkiyar gamsuwa cewa idan Allah ya yi alkawari, shi mai iya kammalawa ne.
22 Therefore it also was “credited to him for righteousness.”
Haka nan ne kuma aka lisafta masa wannan a matsayin adalci.
23 Now it was not written that it was accounted to him for his sake alone,
To ba'a rubuta kawai damin amfaninsa kadai ba, da aka lisafta dominsa.
24 but for our sake also, to whom it will be accounted, who believe in him who raised Yeshua our Lord from the dead,
A rubuce yake domin mu, domin wadanda za'a lisafta su, mu da muka bada gaskiya gare shi wanda ya tada Yesu Ubangijinmu daga matattu.
25 who was delivered up for our trespasses, and was raised for our justification.
Wannan shi ne wanda aka bashe shi domin zunubanmu kuma an tada shi saboda fasar mu.

< Romans 4 >