< Jeremiah 7 >

1 The word that came to Jeremiah from the LORD, saying,
Maganar da ta zo wa Irmiya ke nan daga Ubangiji.
2 “Stand in the gate of the LORD’s house, and proclaim this word there, and say, ‘Hear the LORD’s word, all you of Judah, who enter in at these gates to worship the LORD.’”
“Ka tsaya a ƙofar gidan Ubangiji, a can kuwa ka yi shelar wannan saƙo. “‘Ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuda waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi don yin sujada ga Ubangiji.
3 The LORD of Hosts, the God of Israel says, “Amend your ways and your doings, and I will cause you to dwell in this place.
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allahna Isra’ila, yana cewa ku gyara hanyoyinku da ayyukanku, zan kuwa bar ku ku zauna a wannan wuri.
4 Don’t trust in lying words, saying, ‘The LORD’s temple, the LORD’s temple, the LORD’s temple, are these.’
Kada ku dogara ga maganganun nan na ruɗarwa cewa, “Wannan shi ne haikalin Ubangiji, haikalin Ubangiji, haikalin Ubangiji!”
5 For if you thoroughly amend your ways and your doings, if you thoroughly execute justice between a man and his neighbour;
In dai kuka canja hanyoyinku da ayyukanku kuma kuna aikata adalci da junanku,
6 if you don’t oppress the foreigner, the fatherless, and the widow, and don’t shed innocent blood in this place, and don’t walk after other gods to your own hurt,
in ba ku zalunci baƙo, maraya ko gwauruwa ba kuma in ba ku zub da jinin marar laifi a wannan wuri ba, in kuma ba ku bi waɗansu alloli da za su cuce ku ba,
7 then I will cause you to dwell in this place, in the land that I gave to your fathers, from of old even forever more.
to, zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasar da na ba kakanninku har abada abadin.
8 Behold, you trust in lying words that can’t profit.
Amma ga shi, kuna dogara ga maganganu na ruɗami marasa amfani.
9 Will you steal, murder, commit adultery, swear falsely, burn incense to Baal, and walk after other gods that you have not known,
“‘Za ku yi sata da kisa, ku yi zina da rantsuwar ƙarya, kuna ƙone turare wa Ba’al kuna kuma bin waɗansu allolin da ba ku sani ba,
10 then come and stand before me in this house, which is called by my name, and say, ‘We are delivered,’ that you may do all these abominations?
sa’an nan ku zo ku tsaya a gabana a wannan gida, wanda ake kira da Sunana, kuna cewa, “An cece mu,” mun dace mu aikata waɗannan abubuwa banƙyama?
11 Has this house, which is called by my name, become a den of robbers in your eyes? Behold, I myself have seen it,” says the LORD.
Wannan gidan da ake kira da Sunana ya zama kogon’yan fashi ne a gare ku? Amma ina kallo! In ji Ubangiji.
12 “But go now to my place which was in Shiloh, where I caused my name to dwell at the first, and see what I did to it for the wickedness of my people Israel.
“‘Yanzu ku fita zuwa Shilo inda na fara maishe shi wurin zama don Sunana, ku ga abin da na yi masa saboda muguntar mutanen Isra’ila.
13 Now, because you have done all these works,” says the LORD, “and I spoke to you, rising up early and speaking, but you didn’t hear; and I called you, but you didn’t answer;
Yayinda kuke yin dukan waɗannan abubuwa, in ji Ubangiji, na yi muku magana sau da sau, amma ba ku ji ba; na kira ku, amma ba ku amsa ba.
14 therefore I will do to the house which is called by my name, in which you trust, and to the place which I gave to you and to your fathers, as I did to Shiloh.
Saboda haka, abin da na yi wa Shilo shi ne yanzu zan yi wa gidan da ake kira da Sunana, haikalin da kuka dogara a kai, wurin da na ba ku da kuma kakanninku.
15 I will cast you out of my sight, as I have cast out all your brothers, even the whole offspring of Ephraim.
Zan kore ku daga gabana, kamar yadda na yi ga dukan’yan’uwanku, mutanen Efraim.’
16 “Therefore don’t pray for this people. Don’t lift up a cry or prayer for them or make intercession to me; for I will not hear you.
“Saboda haka kada ka yi addu’a don wannan mutane ko ka yi wani kuka ko roƙo dominsu, gama ba zan ji ka ba.
17 Don’t you see what they do in the cities of Judah and in the streets of Jerusalem?
Ba ka gani abin da suke yi a biranen Yahuda da kuma a titunan Urushalima?
18 The children gather wood, and the fathers kindle the fire, and the women knead the dough, to make cakes to the queen of the sky, and to pour out drink offerings to other gods, that they may provoke me to anger.
Yara sukan tara itace, iyaye suka hura wuta, mata kuma sukan kwaɓa kullu don su yi wa Sarauniyar Sama waina. Sukan miƙa hadayun sha ga waɗansu alloli don su tsokane ni in yi fushi.
19 Do they provoke me to anger?” says the LORD. “Don’t they provoke themselves, to the confusion of their own faces?”
Amma ni ne suke tsokana? In ji Ubangiji Ashe, ba kansu ne suke cuta, suna kunyata kansu ba?
20 Therefore the Lord GOD says: “Behold, my anger and my wrath will be poured out on this place, on man, on animal, on the trees of the field, and on the fruit of the ground; and it will burn and will not be quenched.”
“‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa fushina da hasalata za su kwarara a wannan wuri, a kan mutum da dabba, a kan itatuwan fili da a kan amfanin gona, za su yi ta kuna, ba kuwa za a kashe ba.
21 The LORD of Hosts, the God of Israel says: “Add your burnt offerings to your sacrifices and eat meat.
“‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa ci gaba, ku ƙara hadayun ƙonawarku da sauran sadakoki ku kuma yi ta cin naman!
22 For I didn’t speak to your fathers or command them in the day that I brought them out of the land of Egypt concerning burnt offerings or sacrifices;
Gama sa’ad da na fitar da kakanninku daga Masar na kuma yi musu magana, ban ba su dokoki kawai game da hadayun ƙonawa da sadakoki ba,
23 but this thing I commanded them, saying, ‘Listen to my voice, and I will be your God, and you shall be my people. Walk in all the way that I command you, that it may be well with you.’
amma na ba su wannan umarni cewa ku yi mini biyayya, zan kuwa zama Allahnku ku kuma ku zama mutanena. Ku yi tafiya cikin dukan hanyoyin da na umarce ku, don ku zauna lafiya.
24 But they didn’t listen or turn their ear, but walked in their own counsels and in the stubbornness of their evil heart, and went backward, and not forward.
Amma ba su saurara ba, ba su kuwa kula ba; a maimako, suka bi shawarar kansu da ta taurare muguwar zukatansu. Su ja da baya a maimakon yin gaba.
25 Since the day that your fathers came out of the land of Egypt to this day, I have sent to you all my servants the prophets, daily rising up early and sending them.
Daga lokacin da kakanninku suka bar Masar har yă zuwa yau, kullum na yi ta aikan bayina annabawa.
26 Yet they didn’t listen to me or incline their ear, but made their neck stiff. They did worse than their fathers.
Amma ba su saurare ni ba, ba su kula ba. Sai suka taurare zukatansu suka aikata mugun abu fiye da na kakanninsu.’
27 “You shall speak all these words to them, but they will not listen to you. You shall also call to them, but they will not answer you.
“Sa’ad da ka faɗa musu wannan duka, ba za su saurare ka ba; sa’ad da ka kira su, ba za su amsa ba.
28 You shall tell them, ‘This is the nation that has not listened to the LORD their God’s voice, nor received instruction. Truth has perished, and is cut off from their mouth.’
Saboda haka ka faɗa musu cewa, ‘Wannan ce al’ummar da ba tă yi biyayya ga Ubangiji Allahnta ba, ba kuwa ta karɓi gyara ba. Gaskiya ta ƙare; ta ɓace gaba ɗaya daga leɓunansu.
29 Cut off your hair, and throw it away, and take up a lamentation on the bare heights; for the LORD has rejected and forsaken the generation of his wrath.
“‘Ku aske gashin kanku ku zubar; ku yi makoki a filayen tuddai, gama Ubangiji ya ƙi’yan zamanin nan ya kuma rabu da su saboda fushin da suka ba shi.
30 “For the children of Judah have done that which is evil in my sight,” says the LORD. “They have set their abominations in the house which is called by my name, to defile it.
“‘Mutanen Yahuda sun yi mugunta a gabana, in ji Ubangiji. Sun kafa gumakansu masu banƙyama a gidan da ake kira da Sunana suka ƙazantar da shi.
31 They have built the high places of Topheth, which is in the valley of the son of Hinnom, to burn their sons and their daughters in the fire, which I didn’t command, nor did it come into my mind.
Sun gida masujadan Tofet a Kwarin Ben Hinnom don miƙa’ya’yansu maza da mata a wuta, abin da ban yi umarni ba, ba kuwa yi tunaninsa ba.
32 Therefore behold, the days come”, says the LORD, “that it will no more be called ‘Topheth’ or ‘The valley of the son of Hinnom’, but ‘The valley of Slaughter’; for they will bury in Topheth until there is no place to bury.
Saboda haka ku yi hankali, kwanaki suna zuwa in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara kira wurin Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma Kwarin Kisa, gama za su binne matattu a Tofet sai har ba sauran wuri.
33 The dead bodies of this people will be food for the birds of the sky, and for the animals of the earth. No one will frighten them away.
Sa’an nan gawawwakin wannan mutane za su zama abinci ga tsuntsayen sama da kuma namun jeji, ba za a kuwa sami wani da zai kore su ba.
34 Then I will cause to cease from the cities of Judah and from the streets of Jerusalem the voice of mirth and the voice of gladness, the voice of the bridegroom and the voice of the bride; for the land will become a waste.”
Zan kawo ƙarshen muryar murna da farin ciki da muryar amarya da ango a garuruwan Yahuda da kuma a titunan Urushalima, gama ƙasar za tă zama kufai.

< Jeremiah 7 >