< Zechariah 10 >

1 Ask of Yahweh rain in the spring time, Yahweh who makes storm clouds, and he gives rain showers to everyone for the plants in the field.
Ku roƙi Ubangiji yă ba ku ruwa a lokacin bazara; Ubangiji ne yake yin gizagizan hadari. Shi ne yake ba wa mutane yayyafin ruwan sama yana kuma ba da tsire-tsire na fili ga kowa.
2 For the teraphim have spoken vanity, and the diviners have seen a lie; and they have told false dreams. They comfort in vain. Therefore they go their way like sheep. They are oppressed, because there is no shepherd.
Gumaka suna maganganun ruɗu, masu duba suna ganin wahayoyin ƙarya, suna faɗa mafarkan ƙarya suna ba da ta’aziyyar banza. Saboda haka mutane suna yawo kamar tumaki waɗanda suke shan wahala saboda rashin makiyayi.
3 My anger is kindled against the shepherds, and I will punish the male goats, for Yahweh of Armies has visited his flock, the house of Judah, and will make them as his majestic horse in the battle.
“Ina fushi da makiyayan, zan kuma hukunta shugabannin; gama Ubangiji Maɗaukaki zai lura da garkensa, wato, gidan Yahuda, zai kuma sa su zama kamar doki mai fariya cikin yaƙi.
4 From him will come the cornerstone, from him the tent peg, from him the battle bow, from him every ruler together.
Daga Yahuda dutsen kusurwa zai fito, daga gare shi za a samu abin kafa tenti, daga gare shi za a sami bakan yaƙi, daga gare shi za a sami kowane mai mulki.
5 They will be as mighty men, treading down muddy streets in the battle. They will fight, because Yahweh is with them. The riders on horses will be confounded.
Tare za su zama kamar mutane masu ƙarfi suna tattake lakar tituna a cikin yaƙi. Domin Ubangiji yana tare da su, za su yi faɗa su kuma yi nasara a kan masu yaƙi a kan dawakai.
6 “I will strengthen the house of Judah, and I will save the house of Joseph. I will bring them back, for I have mercy on them. They will be as though I had not cast them off, for I am Yahweh their God, and I will hear them.
“Zan ƙarfafa gidan Yahuda in kuma ceci gidan Yusuf. Zan maido da su domin ina jin tausayinsu. Za su zama kamar ban taɓa ƙinsu ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu zan kuma amsa musu.
7 Ephraim will be like a mighty man, and their heart will rejoice as through wine. Yes, their children will see it and rejoice. Their heart will be glad in Yahweh.
Mutanen Efraim za su zama kamar mutane masu ƙarfi, zukatansu kuwa za su yi murna kamar sun sha ruwan inabi.’Ya’yansu za su gani su yi murna; zuciyarsu za tă yi farin ciki a cikin Ubangiji.
8 I will signal for them and gather them, for I have redeemed them. They will increase as they were before.
Zan ba da alama in kuma tattara su. Ba shakka zan fanshe su; za su yi yawa kamar yadda suke a dā.
9 I will sow them among the peoples. They will remember me in far countries. They will live with their children and will return.
Ko da yake na warwatsa su cikin mutane, duk da haka a can ƙasashe masu nisa za su tuna da ni. Su da’ya’yansu za su rayu, za su kuwa komo.
10 I will bring them again also out of the land of Egypt, and gather them out of Assyria. I will bring them into the land of Gilead and Lebanon; and there won’t be room enough for them.
Zan komo da su daga Masar in kuma tattara su daga Assuriya. Zan kawo su Gileyad da Lebanon, har wuri yă kāsa musu.
11 He will pass through the sea of affliction, and will strike the waves in the sea, and all the depths of the Nile will dry up; and the pride of Assyria will be brought down, and the scepter of Egypt will depart.
Za su ratsa cikin tekun wahala; zan kwantar da raƙuman teku dukan zurfafan Nilu kuma za su bushe. Za a ƙasƙantar da Assuriya, sandar sarautar Masar kuma za tă rabu da ita.
12 I will strengthen them in Yahweh. They will walk up and down in his name,” says Yahweh.
Zan ƙarfafa su a cikin Ubangiji kuma a cikin sunansa za su yi tafiya,” in ji Ubangiji.

< Zechariah 10 >