< Jeremiah 35 >

1 The word which came to Jeremiah from Yahweh in the days of Jehoiakim the son of Josiah, king of Judah, saying,
Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji a lokacin mulkin Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda.
2 “Go to the house of the Rechabites, and speak to them, and bring them into Yahweh’s house, into one of the rooms, and give them wine to drink.”
“Ka tafi wurin iyalin Rekabawa ka gayyace su su zo a ɗaya daga cikin ɗakunan da suke gefe a gidan Ubangiji ka kuma ba su ruwan inabi su sha.”
3 Then I took Jaazaniah the son of Jeremiah, the son of Habazziniah, with his brothers, all his sons, and the whole house of the Rechabites;
Sai na tafi don in kawo Ya’azaniya ɗan Irmiya, ɗan Habazziniya, da’yan’uwansa da kuma dukan’ya’yansa maza, dukan iyalin Rekabawa.
4 and I brought them into Yahweh’s house, into the room of the sons of Hanan the son of Igdaliah, the man of God, which was by the room of the princes, which was above the room of Maaseiah the son of Shallum, the keeper of the threshold.
Na kawo su cikin gidan Ubangiji, a cikin ɗakin’ya’yan Hanan ɗan Igdaliya maza mutumin Allah. Ɗakin ne kusa da ɗakin fadawa, wanda yake bisa na Ma’asehiya ɗan Shallum mai tsaron ƙofa.
5 I set before the sons of the house of the Rechabites bowls full of wine, and cups; and I said to them, “Drink wine!”
Sai na ajiye ƙwarya cike da ruwan inabi da waɗansu kwaf a gaban iyalin Rekabawan na kuma ce musu, “Ku sha ruwan inabin.”
6 But they said, “We will drink no wine; for Jonadab the son of Rechab, our father, commanded us, saying, ‘You shall drink no wine, neither you nor your children, forever.
Amma sai suka amsa suka ce, “Ba ma shan ruwan inabi, domin kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu cewa, ‘Ko ku, ko zuriyarku kada ku sha ruwan inabi.
7 You shall not build a house, sow seed, plant a vineyard, or have any; but all your days you shall dwell in tents, that you may live many days in the land in which you live as nomads.’
Haka kuma ba za ku gina gidaje, ku dasa iri ko ku nome gonakin inabi ba; kada ku kasance da wani daga cikin waɗannan abubuwa, amma dole kullum ku zauna a tentuna. Ta haka za ku yi dogon rai a cikin ƙasar baƙuncinku.’
8 We have obeyed the voice of Jonadab the son of Rechab, our father, in all that he commanded us, to drink no wine all our days, we, our wives, our sons, or our daughters;
Mun yi biyayya da kome da kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu. Mu ko matanmu ko’ya’yanmu maza da mata ba mu taɓa shan ruwan inabi ba
9 and not to build houses for ourselves to dwell in. We have no vineyard, field, or seed;
ba mu kuma gina gidaje mu zauna a ciki ba ko mu yi gonakin inabi, gonaki ko hatsi ba.
10 but we have lived in tents, and have obeyed, and done according to all that Jonadab our father commanded us.
Mun yi rayuwarmu a cikin tentuna mun kuma yi biyayya ƙwarai da kowane abin da kakanmu Yehonadab ya umarce mu.
11 But when Nebuchadnezzar king of Babylon came up into the land, we said, ‘Come! Let’s go to Jerusalem for fear of the army of the Chaldeans, and for fear of the army of the Syrians; so we will dwell at Jerusalem.’”
Amma da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kawo wa ƙasan nan hari, sai muka ce, ‘Ku zo, dole mu tafi Urushalima don mu tsira daga Babiloniyawa da kuma sojojin Arameyawa.’ Saboda haka ne muke a Urushalima.”
12 Then Yahweh’s word came to Jeremiah, saying,
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
13 “Yahweh of Armies, the God of Israel, says: ‘Go and tell the men of Judah and the inhabitants of Jerusalem, “Will you not receive instruction to listen to my words?” says Yahweh.
“Ga abin da Ubangiji, Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ka tafi ka faɗa wa mutanen Yahuda da kuma mutanen Urushalima cewa, ‘Ba za ku koyi darasi ku kuma yi biyayya da maganata ba?’ In ji Ubangiji.
14 “The words of Jonadab the son of Rechab that he commanded his sons, not to drink wine, are performed; and to this day they drink none, for they obey their father’s commandment; but I have spoken to you, rising up early and speaking, and you have not listened to me.
‘Yehonadab ɗan Rekab ya umarci’ya’yansa maza kada su sha ruwan inabi sun kuma kiyaye wannan umarni. Har yă zuwa yau ba sa shan ruwan inabi, domin sun yi biyayya da umarnin kakansu. Amma na yi muku magana sau da sau, duk da haka ba ku yi biyayya ba.
15 I have sent also to you all my servants the prophets, rising up early and sending them, saying, ‘Every one of you must return now from his evil way, amend your doings, and don’t go after other gods to serve them. Then you will dwell in the land which I have given to you and to your fathers;’ but you have not inclined your ear, nor listened to me.
Sau da sau na aika dukan bayina annabawa gare ku. Suka ce, “Kowannenku ya juyo daga mugayen hanyoyinsa ya sabunta ayyukansa; kada yă bi waɗansu alloli don yă bauta musu. Ta haka za ku zauna a cikin ƙasar da na ba ku da kuma kakanninku.” Amma ba ku saurara ba, ba ku kuwa ji ni ba.
16 The sons of Jonadab the son of Rechab have performed the commandment of their father which he commanded them, but this people has not listened to me.”’
Zuriyar Yehonadab ɗan Rekab sun yi biyayya da umarnin da kakansu ya ba su, amma waɗannan mutane ba su yi mini biyayya ba.’
17 “Therefore Yahweh, the God of Armies, the God of Israel, says: ‘Behold, I will bring on Judah and on all the inhabitants of Jerusalem all the evil that I have pronounced against them, because I have spoken to them, but they have not heard; and I have called to them, but they have not answered.’”
“Saboda haka, ga abin da Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Ku saurara! Zan kawo wa Yahuda da kuma kowane mutumin da yake zama a Urushalima kowace masifar da na ambata a kansu. Na yi musu magana, amma ba su saurara ba; na kira su, amma ba su amsa ba.’”
18 Jeremiah said to the house of the Rechabites, “Yahweh of Armies, the God of Israel, says: ‘Because you have obeyed the commandment of Jonadab your father, and kept all his precepts, and done according to all that he commanded you,’
Sai Irmiya ya ce wa iyalin Rekabawa, “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kun yi biyayya da umarnin kakanku Yehonadab kuka kuma kiyaye dukan umarnansa kuka yi kome bisa ga tsari.’
19 therefore Yahweh of Armies, the God of Israel, says: ‘Jonadab the son of Rechab will not lack a man to stand before me forever.’”
Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Yehonadab ɗan Rekab ba zai taɓa rasa mutumin da zai yi mini hidima ba.’”

< Jeremiah 35 >