< 2 Corinthians 3 >

1 Are we beginning again to commend ourselves? Or do we need, as do some, letters of commendation to you or from you?
Muna fara sake yabon kanmu ne? Ba mu bukatar wasikun shaida daga gare ku ko zuwa gare ku, kamar wadansu mutane, ko ba haka ba?
2 You are our letter, written in our hearts, known and read by all men,
Ku da kanku kune wasikar shaidarmu, wadda aka rubuta a zukatanmu, wadda Kuma dukan mutane suka sani suke kuma karantawa.
3 being revealed that you are a letter of Christ, served by us, written not with ink, but with the Spirit of the living God; not in tablets of stone, but in tablets that are hearts of flesh.
Kuma kun nuna ku wasika ne daga Almasihu, wadda muka isar. Ba da tawada aka rubuta ta ba amma da Ruhun Allah mai rai. Ba bisa allunan duwatsu aka rubuta ta ba, amma bisa allunan zukatan mutane.
4 Such confidence we have through Christ toward God,
Gama wannan ne gabagadin da muke da shi cikin Allah ta wurin Almasihu.
5 not that we are sufficient of ourselves to account anything as from ourselves; but our sufficiency is from God,
Ba mu da wata gwanintar kanmu da za mu yi takamar wani abu ya zo daga gare mu. Maimakon haka, gwanintar mu daga Allah take.
6 who also made us sufficient as servants of a new covenant, not of the letter but of the Spirit. For the letter kills, but the Spirit gives life.
Allah ne ya maishe mu kwararrun bayi na sabon alkawari. Wannan alkawari ne ba na rubutu ba amma na Ruhu. Gama rubutu kisa yake yi, amma Ruhu rai yake bayarwa.
7 But if the service of death, written engraved on stones, came with glory, so that the children of Israel could not look steadfastly on the face of Moses for the glory of his face, which was passing away,
To hidimar da ta haifar da mutuwa- wadda aka rubuta bisa duwatsu- ta zo cikin irin wannan daukaka da har Israila ba su iya kallon fuskar Musa kai tsaye ba. Wannan kuwa saboda daukakar da ke fuskarsa ne, daukaka mai shudewa.
8 won’t service of the Spirit be with much more glory?
Ina misalin girman daukakar hidimar da Ruhu ke yi?
9 For if the service of condemnation has glory, the service of righteousness exceeds much more in glory.
Gama idan hidimar kayarwa tana da daukaka, ina misalin yalwatar daukaka da hidimar adalchi za ta yi!
10 For most certainly that which has been made glorious has not been made glorious in this respect, by reason of the glory that surpasses.
Babu shakka, abin da aka maishe shi mai daukaka a da, ba ya da sauran daukaka a wannan fanni, saboda irin daukakar da ta zarce shi.
11 For if that which passes away was with glory, much more that which remains is in glory.
To idan har mai shudewar nan ya na da daukaka, ina misalin daukakar da abu na dindindin zai samu!
12 Having therefore such a hope, we use great boldness of speech,
Dashike muna da wannan tabbaci, muna da gabagadi sosai.
13 and not as Moses, who put a veil on his face so that the children of Israel wouldn’t look steadfastly on the end of that which was passing away.
Ba kamar Musa muke ba wanda ya sa mayafi ya rufe fuskarsa, ta yadda mutanen Isra'ila basu iya kallon karshen daukaka mai shudewa ba kai tsaye.
14 But their minds were hardened, for until this very day at the reading of the old covenant the same veil remains, because in Christ it passes away.
Amma tunaninsu ya zama a rufe. Har yau kuwa mayafin na nan sa'adda ake karanta tsohon alkawari. Ba a bude shi ba, saboda a cikin Almasihu ne kadai ake kawar da shi.
15 But to this day, when Moses is read, a veil lies on their heart.
Amma har yau, duk lokacin da ake karanta littafin Musa, akwai mayafi shimfide a zukatansu.
16 But whenever someone turns to the Lord, the veil is taken away.
Amma sa'adda mutum ya juyo wurin Ubangiji, an kawar da mayafin.
17 Now the Lord is the Spirit; and where the Spirit of the Lord is, there is liberty.
To Ubangiji shine Ruhun. Inda Ruhun Ubangiji yake, akwai 'yanci.
18 But we all, with unveiled face seeing the glory of the Lord as in a mirror, are transformed into the same image from glory to glory, even as from the Lord, the Spirit.
Dukan mu yanzu, da fuskoki marasa mayafi, muna ganin daukakar Ubangiji. Muna samun sakewa zuwa cikin irin wannan daukaka, daga wannan mataki na daukaka zuwa wani matakin, kamar dai daga wurin Ubangiji, wanda shine Ruhun.

< 2 Corinthians 3 >