< Lamentations 1 >

1 How doth the city sit desolate, that was full of people! how is she become as a widow! she that was great among the nations, and princess among the provinces, how is she become a forced labourer!
Yanzu birnin ya zama babu kowa a ciki, birnin da a dā yake cike da mutane! Yanzu birnin ya zama kamar gwauruwa, wadda a dā babba ce ita a cikin ƙasashe! Ita da take sarauniya a cikin larduna yanzu ta zama baiwa.
2 She weepeth bitterly in the night, and her tears are on her cheeks: among all her lovers she hath none to comfort her: all her friends have dealt treacherously with her, they are become her enemies.
Tana yin kuka mai zafi da dare, hawaye na gangara a kan kumatunta. A cikin masoyanta duka babu wanda ya yi mata ta’aziyya. Duk abokanta sun yashe ta; sun zama abokan gābanta.
3 Judah is gone into captivity because of affliction, and because of great servitude: she dwelleth among the heathen, she findeth no rest: all her persecutors overtook her in the midst of distress.
Bayan wahala da baƙin ciki, Yahuda ta tafi bauta. Ta zauna a cikin ƙasashe, ba tă samu wurin hutawa ba. Duk masu fafararta sun same ta sa’ad da take cikin matuƙar ɓacin rai.
4 The ways of Zion do mourn, because none come to the solemn feasts: all her gates are desolate: her priests sigh, her virgins are afflicted, and she is in bitterness.
Hanyoyin zuwa Sihiyona suna makoki, gama ba wanda ya zo bikin da ta shirya. Ba kowa a hanyoyin shiganta. Firistocinta suna gurnani,’yan matana kuma suna wahala, kuma tana cikin shan wahala ƙwarai.
5 Her adversaries are the head, her enemies prosper; for the LORD hath afflicted her for the multitude of her transgressions: her children are gone into captivity before the enemy.
Maƙiyanta sun zama shugabanninta; Abokan gābanta suna da kwanciyar rai. Ubangiji ya kawo mata ɓacin rai domin yawan zunubanta.’Ya’yanta sun tafi bauta, a ƙarƙashin maƙiyanta.
6 And from the daughter of Zion all her beauty hath departed: her princes are become like harts that find no pasture, and they are gone without strength before the pursuer.
Diyar Sihiyona ba ta da sauran daraja.’Ya’yan sarakunanta sun zama kamar bareyi waɗanda suka rasa wurin kiwo; cikin rashin ƙarfi suka guje wa masu fafararsu.
7 Jerusalem remembered in the days of her affliction and of her miseries all her pleasant things that she had in the days of old, when her people fell into the hand of the enemy, and none helped her: the adversaries saw her, and mocked at her sabbaths.
A cikin kwanakin da take shan wahala take kuma yawo Urushalima ta tuna da dukan dukiyar da take da ita a kwanakin dā can. Sa’ad da mutanenta suka faɗa cikin hannun abokan gābanta, ba wanda ya taimake ta. Maƙiyanta suka dube ta suka yi mata dariya don hallakar da ta auko mata.
8 Jerusalem hath grievously sinned; therefore she is removed: all that honoured her despise her, because they have seen her nakedness: yea, she sigheth, and turneth backward.
Urushalima ta yi zunubi ƙwarai saboda haka ta zama marar tsarki. Dukan masu martaba ta sun raina ta, gama sun ga tsiraicinta; ita ma da kanta tana nishi da ƙyar ta kuma juya baya.
9 Her filthiness is in her skirts; she remembereth not her latter end; therefore she hath been marvellously abased: she had no comforter. O LORD, behold my affliction: for the enemy hath magnified himself.
Ƙazantarta ta manne wa rigunanta; ba tă kula da nan gaba ba, fāɗuwarta kuwa babban abu ne; babu wanda zai yi mata ta’aziyya. “Duba, ya Ubangiji, ka ga wahalata, gama maƙiyi ya yi nasara.”
10 The adversary hath spread out his hand upon all her pleasant things: for she hath seen that the heathen entered into her sanctuary, whom thou didst command that they should not enter into thy congregation.
Maƙiya ya kwashe dukiyarta duka; ta ga mutanen da ba su san Allah ba sun shiga wuri mai tsarkinta waɗanda ka hana su shiga taron jama’arka.
11 All her people sigh, they seek bread; they have given their pleasant things for food to relieve the soul: see, O LORD, and consider; for I am become vile.
Dukan mutanenta suna nishi da ƙyar suna neman burodi; sun sayar da dukiyarsu don su samu abinci don kada su mutu da yunwa. “Ubangiji, ka duba ka gani, gama an yashe ni.”
12 Is it nothing to you, all ye that pass by? behold, and see if there is any sorrow like my sorrow, which hath fallen upon me, which the LORD hath afflicted me in the day of his fierce anger.
“Ko wannan ba wani abu ba ne a wurinku, dukanku masu wucewa? Ku duba ku gani. Ko akwai wata wahala kamar irin wadda nake sha, wadda Ubangiji ya auko mini a cikin zafin fushinsa?
13 From above hath he sent fire into my bones, and it prevaileth against them: he hath spread a net for my feet, he hath turned me back: he hath made me desolate and faint all the day.
“Daga sama ya aiko da wuta, ya aiko ta cikin ƙasusuwana. Ya shimfiɗa raga a ƙafafuna ya juyo da ni. Ya bar ni ni kaɗai, sumamme dukan yini.
14 The yoke of my transgressions is bound by his hand: they are knit together, and come up upon my neck: he hath made my strength to fall, the Lord hath delivered me into their hands, from whom I am not able to rise.
“Ya ɗaura zunubaina a wuyana; aka naɗe su a hannuwansa. Aka rataye su a wuyana Ubangiji ya kwashe ƙarfina. Ya bashe ni ga waɗanda suka fi ni ƙarfi.
15 The Lord hath trodden under foot all my mighty men in the midst of me: he hath called an assembly against me to crush my young men: the Lord hath trodden the virgin, the daughter of Judah, as in a winepress.
“Ubangiji ya ƙi duk mayaƙan da suke tare da ni; ya sa wata runduna ta tayar mini ta kuma tattake samarina. Ubangiji ya tattake budurwa Diyar Yahuda kamar’ya’yan inabi a wurin matsewa.
16 For these things I weep; my eye, my eye runneth down with water, because the comforter that should relieve my soul is far from me: my children are desolate, because the enemy prevailed.
“Dalilin da ya sa nake kuka ke nan idanuna kuma suna ta zubar da hawaye. Babu wani a kusa da zai yi mini ta’aziyya, ba wanda zai sabunta ruhuna.’Ya’yana sun zama fakirai domin maƙiyina ya yi nasara.”
17 Zion spreadeth forth her hands, and there is none to comfort her: the LORD hath commanded concerning Jacob, that his adversaries should be around him: Jerusalem is as a menstruous woman among them.
Sihiyona ta miƙa hannunta, amma ba wani da zai yi mata ta’aziyya. Ubangiji ya umarta cewa maƙwabtansa za su zama maƙiyansa; Urushalima ta zama abar ƙyama a cikinsu.
18 The LORD is righteous; for I have rebelled against his commandment: hear, I pray you, all people, and behold my sorrow: my virgins and my young men are gone into captivity.
“Ubangiji mai adalci ne, duk da haka na yi tawaye da umarninsa. Ku saurara, jama’a duka; ku dubi wahalar da nake sha. Samarina da’yan matana duka sun tafi bauta.
19 I called for my lovers, but they deceived me: my priests and my elders gave up the ghost in the city, while they sought their food to relieve their souls.
“Na kira abokaina amma sun yashe ni. Firistocina da dattawana sun hallaka a cikin birnin yayinda suke neman abinci don kada su mutu da yunwa.
20 Behold, O LORD; for I am in distress: my heart is troubled; my heart is turned within me; for I have grievously rebelled: abroad the sword bereaveth, at home there is as death.
“Duba, Ubangiji, ka ga ƙuncin da nake ciki! Ina shan azaba a raina, ba ni da kwanciyar rai a cikin zuciyata, domin na yi tawaye sosai. A waje takobi na kisa; a ciki kuma akwai mutuwa.
21 They have heard that I sigh: there is none to comfort me: all my enemies have heard of my trouble; they are glad that thou hast done it: thou wilt bring the day that thou hast called, and they shall be like me.
“Mutane suna ji ina nishi da ƙyar, amma ba wanda zai yi mini ta’aziyya. Dukan maƙiyana sun ji wahalar da nake ciki; suna farin ciki da abin da ka yi. Ka kawo ranan nan da ka sanar domin su ma su zama kamar ni.
22 Let all their wickedness come before thee; and do to them, as thou hast done to me for all my transgressions: for my sighs are many, and my heart is faint.
“Bari ka ga muguntarsu duka; ka yi musu yadda ka yi mini domin dukan zunubansu. Nishina da yawa kuma zuciyata ta gaji.”

< Lamentations 1 >