< Matthew 10 >

1 And, calling near his twelve disciples, he gave them authority over impure spirits, —so as to be casting them out, and curing every disease and every infirmity.
Sai ya kira almajiransa goma sha biyu wurinsa ya kuma ba su iko su fitar aljanu, su kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
2 Now, the twelve apostles’ names, are these: —first Simon, who is called Peter, and Andrew his brother, —and James, the son of Zebedee, and John, his brother;
Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu, da fari, Siman (wanda ake kira Bitrus) da ɗan’uwansa Andarawus; Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna;
3 Philip, and Bartholomew, —Thomas, and Matthew, the tax-collector; James, the son of Alphaeus, and Thadaeus;
Filibus da Bartolomeyu; Toma da Mattiyu mai karɓar haraji; Yaƙub ɗan Alfayus da Taddayus;
4 Simon, the zealot, and Judas Iscariot, who also delivered him up.
Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu.
5 These twelve, Jesus sent forth, charging them, saying: —Into any way to the nations, do not depart, —and, into any city of Samaritans, do not enter;
Waɗannan sha biyun ne Yesu ya aika da umarni cewa, “Kada ku je cikin Al’ummai, ko kuwa ku shiga wani garin Samariyawa.
6 But be going, rather, unto the lost sheep of the house of Israel.
A maimakon haka ku je wajen ɓatattun tumakin Isra’ila.
7 And, as ye go, proclaim, saying, The kingdom of the heavens hath drawn near!
Sa’ad da kuke tafiya, ku yi wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin sama ya kusato.’
8 Be curing, the sick, raising, the dead, —cleansing, lepers, casting out, demons: freely, ye have, received, freely, give.
Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.
9 Ye may procure—neither gold, nor silver, nor copper, for your belts, —
“Kada ku riƙe wata zinariya ko azurfa ko jan ƙarfe a aljihunanku,
10 neither satchel for journey, nor two tunics, nor sandals, nor staff; for, worthy, is the labourer, of his maintenance.
kada ku ɗauki jaka don tafiya, ko ƙarin riga, ko takalma ko sanda; domin ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.
11 And, into whatsoever city or village ye enter, search out who in it is, worthy, and, there, abide, till ye go forth.
Kowane gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a wurin, ku kuma zauna a gidansa har sai kun tashi.
12 And, as ye enter the house, salute it;
Da shigarku gidan, ku yi gaisuwa.
13 And, if the house be worthy, let your peace come upon it, but, if it be not worthy, let your peace, unto you, return.
In gidan na kirki ne, bari salamarku ta zauna a kansa; in kuwa ba mai kirki ba, salamarku ta komo muku.
14 And, whosoever shall neither welcome you, nor hear your words, as ye go forth outside that house or city, shake off the dust of your feet:
Duk wanda ya ƙi marabtarku ko ya ƙi sauraron kalmominku, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita gidan ko garin.
15 Verily, I say unto you, —More tolerable, will it be, for the land of Sodom and Gomorrha in the day of judgment, than for, that, city!
Gaskiya nake gaya muku, za a fi jin tausayin Sodom da Gomorra a ranar shari’a fiye da wannan gari.
16 Lo! I, send you forth as sheep amidst wolves; become ye therefore—prudent, as serpents, and simple, as doves.
“Ina aikan ku kamar tumaki a cikin kyarketai. Saboda haka ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.
17 But beware of men; for they will deliver you up into high-councils, and, in their synagogues, will they scourge you, —
Ku yi hankali da mutane; za su miƙa ku ga majalisa su kuma yi muku bulala a majami’unsu.
18 And, before both governor and kings, shall ye be brought, for my sake—for a witness to them and the nations.
Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Al’ummai.
19 And, when they deliver you up, be not anxious how or what ye shall speak, —for it shall be given you in that hour what ye shall speak;
Amma sa’ad da suka kama ku, kada ku damu game da abin da za ku faɗa ko kuwa yadda za ku faɗe shi. A lokacin za a ba ku abin da za ku faɗa,
20 For it is not, ye, who are speaking, but, the Spirit of your Father, that is speaking in you.
gama ba ku ba ne kuke magana, amma Ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku.
21 And, brother, will deliver up, brother, unto death, and, father, child, —and, children, will rise up, against parents, and will put them to death.
“Ɗan’uwa zai ci amanar ɗan’uwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa;’ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.
22 And ye will be hated by all, because of my name, —but, he that endureth throughout, the same, shall be saved.
Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto.
23 And, when they persecute you in this city, flee into another, —for, verily, I say unto you, in nowise shall ye finish the cities of Israel, till, he Son of Man, come.
Sa’ad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo.
24 A, disciple, is not above, the teacher, nor, a servant, above, his lord:
“Ɗalibi ba ya fin malaminsa, haka ma, bawa ba ya fin maigidansa.
25 Sufficient for the disciple, that he become, as his teacher, and, the servant, as, his lord. If, the master of the house, Beelzebul, they called, how much more, the men of his house!
Ya isa wa ɗalibi yă zama kamar malaminsa, haka ma bawa kamar maigidansa. In har an kira wanda yake kan gida Be’elzebub, me za su ce game da mutanen gidansa?
26 Then do not fear them, —for, nothing hath been covered, which shall not be, uncovered, and, hidden, which shall not be, made known.
“Saboda haka kada ku ji tsoronsu. Ba abin da yake a rufe da ba za a tone ba, ko kuwa a ɓoye da ba za a bayyana ba.
27 What I am saying to you in the darkness, tell ye in the light, —and, what [whispered] into the ear ye are hearing, proclaim ye on the housetops.
Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki.
28 And be not in fear, by reason of them that are killing the body, —and, the soul, are not able to kill. But fear, rather, him who is able, both soul and body, to destroy in gehenna! (Geenna g1067)
Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta. (Geenna g1067)
29 Are not, two sparrows, for a farthing, sold? And, one from among them, shall not fall upon the ground, without your Father;
Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku.
30 But, even the hairs of, your, head, have all been numbered.
Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su.
31 Then be not in fear—than many sparrows, better are, ye!
Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.
32 Every one therefore who shall confess me before men, I also, will confess, him, before my Father who is in the heavens;
“Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama.
33 But, whoever shall deny me before men, I also, will deny, him, before my Father who is in the heavens.
Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama.
34 Do not think, that I came to thrust peace upon the earth, —I came not to thrust, peace, but, a sword;
“Kada fa ku ɗauka na zo ne don in kawo salama a duniya. A’a, ban zo don in kawo salama ba, sai dai takobi.
35 For I came to set at variance—a man, against, his father, and, a daughter, against, her mother, and, a bride, against, her mother-in-law;
Gama na zo ne in sa, “‘gāba tsakanin mutum da mahaifinsa,’ya da mahaifiyarta, matar ɗa da surukarta,
36 And, a man foes, are, they of his own house.
abokan gāban mutum, za su zama mutanen gidansa ne.’
37 He that loveth father or mother above me, is not, worthy, of me, —and, he that loveth son or daughter above me, is not, worthy, of me;
“Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba;
38 And, he that doth not take his cross and follow after me, is not, worthy, of me.
duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba.
39 He that hath found his life, shall lose it, —and, he that hath lost his life, for my sake, shall find it.
Duk mai son adana ransa zai rasa shi, duk wanda kuwa ya rasa ransa saboda ni zai same shi.
40 He that giveth welcome unto you, unto me, giveth welcome, and, he that, unto me, giveth welcome, giveth welcome—unto him that sent me forth.
“Wanda ya karɓe ku, ya karɓe ni ne, wanda kuma ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.
41 He that giveth welcome unto a prophet, in the name of a prophet, the reward of a prophet, shall receive; and, he that giveth welcome unto a righteous man, in the name of a righteous man, the reward of a righteous man, shall receive; —
Duk wanda ya karɓi annabi don shi annabi ne, zai sami ladar annabi, duk kuwa wanda ya karɓi mutum mai adalci don shi mai adalci ne, zai sami ladar mai adalci.
42 And, whosoever shall give to drink—unto one of these little ones—a cup of cold water only, in the name of a disciple, Verily, I say unto you, in nowise, shall lose his reward!
In kuma wani ya ba wa ɗaya daga cikin ƙananan nan ko da kwaf ruwan sanyi ne kan shi almajirina ne, gaskiya nake gaya muku, ba shakka ba zai rasa ladarsa ba.”

< Matthew 10 >