< 1 Timothy 3 >

1 This is a faithful saying: If someone aspires to the office of overseer, he desires a good work.
Ga wata tabbatacciyar magana. In wani ya sa zuciyarsa a kan zama mai kula da ikkilisiya, yana marmarin yin aiki mai daraja ne.
2 The overseer, therefore, must be beyond criticism, the husband of one wife, temperate, self-controlled, respectable, hospitable, good at teaching;
To, dole mai kula da Ikkilisiya yă kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa,
3 not a drunkard, not violent, but gentle, not quarrelsome, not a lover of money;
ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba.
4 one who rules his own house well, having children in subjection with all reverence;
Dole yă iya tafiyar da iyalinsa da kyau, yă kuma tabbata cewa’ya’yansa suna yin masa biyayya da ladabin da ya dace.
5 (but if someone does not know how to manage his own house, how will he take care of the church of God?)
(In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?)
6 not a new convert, lest being puffed up he fall into the same condemnation as the devil.
Kada yă zama sabon tuba, in ba haka zai zama mai girman kai yă kuma fāɗa cikin irin hukuncin da ya fāɗo wa Iblis.
7 Moreover he must have good testimony from those who are outside, to avoid falling into disgrace and the trap of the devil.
Dole kuma yă kasance da shaida mai kyau ga waɗanda suke na waje, don kada yă zama abin kunya yă kuma fāɗa cikin tarkon Iblis.
8 Deacons, in the same way, must be reverent, not double-tongued, not devoted to a lot of wine, not greedy for money;
Haka masu hidima a cikin ikkilisiya; su ma, su zama maza da sun cancanci girmamawa, masu gaskiya, ba masu yawan shan ruwan inabi ba, ba masu kwaɗayin ƙazamar riba ba.
9 holding the mystery of the faith in a pure conscience.
Dole su riƙe asirin bangaskiya su kuma kasance da lamiri mai tsabta.
10 Let them also first be tested; then let them serve as deacons, if they are blamesless.
Dole a fara gwada su tukuna; sa’an nan in ba a sami wani abin zargi game da su ba, sai su shiga aikin masu hidima.
11 Their wives in the same way must be reverent, not slanderers, temperate, faithful in all things.
A haka kuma, dole matansu su zama matan da suka cancanci girmamawa, ba masu gulma ba, sai dai masu sauƙinkai da kuma masu aminci a cikin kome.
12 Let deacons be husbands of one wife, ruling their children and their own houses well.
Dole mai hidimar ikkilisiya yă zama mijin mace guda dole kuma yă iya tafiyar da’ya’yansa da kuma iyalinsa da kyau.
13 For those who have served well as deacons gain for themselves a good standing, and great boldness in the faith which is in Christ Jesus.
Waɗanda suke hidima da kyau suna samar wa kansu kyakkyawan suna da kuma cikakken tabbatarwa a cikin bangaskiyarsu cikin Kiristi Yesu.
14 These things I write to you, hoping to come to you shortly;
Ko da yake ina sa zuciya zo wurinka nan ba da daɗewa ba, ina rubuta muka waɗannan umarnai domin,
15 but if I wait long, that you may know how people ought to behave themselves in the house of God, which is the church of the living God, the pillar and ground of the truth.
in na yi jinkiri, za ka san yadda ya kamata mutane su tafiyar da halayensu a cikin jama’ar Allah, wadda take ikkilisiyar Allah rayayye, ginshiƙi da kuma tushen gaskiya.
16 Without controversy, the mystery of godliness is great: He was revealed in the flesh, justified by the Spirit, seen by angels, preached among the nations, believed on in the world, and received up in glory.
Ba shakka, asirin addini da girma yake. Ya bayyana cikin jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, mala’iku suka gan shi, aka yi wa’azinsa cikin al’ummai, aka gaskata shi a duniya, aka ɗauke shi sama cikin ɗaukaka.

< 1 Timothy 3 >