< Revelation 20 >

1 I saw an angel coming down out of heaven, having the key of the abyss and a great chain in his hand. (Abyssos g12)
Sai na ga mala'ika na saukowa daga sama. Yana da makullin rami marar iyaka, yana kuma da babar sarka a hannunsa. (Abyssos g12)
2 He seized the serpent, the ancient snake, which is the devil and Satana, and bound him for a thousand years,
Sai ya dauki tsohon macijin, wanda shine iblis, ko shaidan, ya daure shi shekaru dubu.
3 and cast him into the abyss, and shut it, and sealed it over him, that he should deceive the nations no more, until the thousand years were finished. After this, he must be freed for a short time. (Abyssos g12)
Ya jefa shi cikin rami marar iyaka, ya rufe shi ya kuma sa hatimi a bisansa. Hakan ya faru ne domin kada ya kara yaudarar al'ummai har sai bayan shekaru dubu. Bayan wannan, dole a sake shi na dan lokaci. (Abyssos g12)
4 I saw thrones, and they sat on them, and judgment was given to them. I saw the souls of those who had been beheaded for the testimony of Yeshua, and for the word of God, and such as did not worship the beast nor his image, and did not receive the mark on their forehead and on their hand. They lived, and reigned with Meshikha for a thousand years.
Sa'annan na ga kursiyoyi. Wadanda ke zaune a bisansu sune wadanda aka ba ikon hukunci. Na kuma ga rayukan wadanda aka fille wa kai saboda shaidar Yesu da maganar Allah. Ba su yi wa dabban sujada ba ko siffarsa, suka ki su karbi alamar a goshinsu ko a hannu. Sun sake rayuwa, suka yi mulki tare da Kristi shekaru dubu.
5 The rest of the dead did not live until the thousand years were finished. This is the first resurrection.
Sauran matattun basu sake dawowa da rai ba har sai da shekaru dubu din suka cika. Wannan shine tashin matattu na fari.
6 Blessed and holy is he who has part in the first resurrection. Over these, the second death has no power, but they will be priests of God and of Meshikha, and will reign with him one thousand years.
Mai albarka ne mai tsarki ne kuma wanda yake da rabo cikin tashin matattu na fari! Mutuwa ta biyu ba ta da iko akan wadannan. Za su zama firistocin Allah da na Almasihu za su kuma yi mulki tare da shi shekaru dubu.
7 And after the thousand years, Satana will be released from his prison,
Sa'adda shekaru dubu suka zo ga karshe, za a saki shaidan daga kurkukunsa.
8 and he will come out to deceive the nations which are in the four quarters of the earth, Gog and Magog, to gather them together to the war; the number of whom is as the sand of the sea.
Za ya fito domin ya yaudari al'ummai da ke kursuyoyi hudu na duniya, Gog da Magog ya tattara su domin yaki. Yawan su zai zama kamar yashin teku.
9 They went up over the breadth of the earth, and surrounded the camp of the saints, and the beloved city, and fire came down out of heaven and devoured them.
Suka bazu a fuskar duniya suka kuma kewaye sansanin masu ba da gaskiya, kaunataccen birni. Amma wuta ta sauko daga sama ta lankwame su.
10 The devil who deceived them was thrown into the lake of fire and sulfur, where the beast and the false prophet are also. They will be tormented day and night forever and ever. (aiōn g165, Limnē Pyr g3041 g4442)
Shaidan, wanda ya yaudare su, aka jefa shi cikin korama ta farin wuta mai ci, inda aka jefa dabban da makaryacin annabin. Za su sha azaba dare da rana har abada abadin. (aiōn g165, Limnē Pyr g3041 g4442)
11 I saw a great white throne, and him who sat on it, from whose face the earth and the heaven fled away. There was found no place for them.
Sai na ga babban kursiyi da wanda ke zaune a kansa. Duniya da sama suka guje wa fuskarsa, amma babu wurin da za su tafi.
12 I saw the dead, the great and the small, standing before the throne, and they opened books. Another book was opened, which is the Book of Life. The dead were judged out of the things which were written in the books, according to their works.
Na ga matattu manya da kanana- suna tsaye gaban kursiyin, aka bude litattafai. Sai aka bude wani littafi - Littafin rai. Aka yi wa matattu shari'a bisa ga abinda aka rubuta cikin litattafan, gwargwadon ayyukansu.
13 The sea gave up the dead who were in it. Death and Sheyul gave up the dead who were in them. They were judged, each one according to his works. (Hadēs g86)
Teku ta ba da matattun dake cikinta. Mutuwa da hades suka ba da matattun da ke cikinsu, aka yi masu shari'a gwargwadon abin da suka yi. (Hadēs g86)
14 Death and Sheyul were thrown into the lake of fire. This is the second death, the lake of fire. (Hadēs g86, Limnē Pyr g3041 g4442)
Aka jefa mutuwa da hades cikin tafkin wuta. Wannan shine mutuwa ta biyu - tafkin wuta. (Hadēs g86, Limnē Pyr g3041 g4442)
15 If anyone was not found written in the Book of Life, he was cast into the lake of fire. (Limnē Pyr g3041 g4442)
Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce cikin littafin rai ba, aka jefar da shi cikin tafkin wuta. (Limnē Pyr g3041 g4442)

< Revelation 20 >