< Exodus 6 >

1 But the Lord told Moses, “Now you'll see what I'm going to do to Pharaoh. Using my great strength I will force him to let them go; because of my power he will send them out from his country.”
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu za ka gan abin da zan yi da Fir’auna. Zan sa shi dole yă bar su su tafi, har ma yă iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!”
2 God spoke to Moses and told him, “I am Yahweh!
Allah ya kuma ce wa Musa, “Ni ne Ubangiji.
3 I revealed myself as God Almighty to Abraham, to Isaac, and to Jacob, but they didn't know my name, ‘Yahweh.’
Na bayyana ga Ibrahim, ga Ishaku da kuma ga Yaƙub a matsayin Allah Maɗaukaki, amma sunan nan nawa Ubangiji, ban bayyana kaina a gare su ba.
4 I also confirmed my solemn agreement with them to give them the land of Canaan, the country where they were living as foreigners.
Na kuma kafa alkawari da su don in ba su ƙasar Kan’ana, inda suka yi zaman baƙunci.
5 In addition I've heard the groans of the Israelites that the Egyptians are treating as slaves, and I haven't forgotten the agreement I promised them.
Ban da haka ma, na ji nishe-nishen Isra’ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuma tuna da alkawarina.
6 So tell the Israelites, ‘I am the Lord and I will save you from the forced labor the Egyptians are making you do; I will set you free from being their slaves. I will rescue you using my power and imposing heavy punishments.
“Saboda haka, ka ce wa Isra’ilawa, ‘Ni ne Ubangiji, zan kuma fitar da ku daga bauta ta Masarawa. Zan’yantar da ku daga zama bayinsu, da ƙarfina zan fanshe ku, in kawo hukunci mai zafi a kansu, don in cece ku.
7 I will make you my own people. Then you will know that I am the Lord your God, who rescued you from slavery in Egypt.
Zan ɗauke ku tamƙar mutanena, in kuma zama Allahnku. Sa’an nan za ku sani Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga wahalar Masarawa.
8 I will take you to the land that I solemnly promised to give to Abraham, Isaac, and Jacob. I will give it to you to own. I am the Lord!’”
Zan kuwa kawo ku a ƙasar da na rantse da hannun da na ɗaga sama, cewa zan ba wa Ibrahim, wa Ishaku, da kuma wa Yaƙub. Zan ba da ita gare ku gādo. Ni ne Ubangiji.’”
9 Moses explained this to the Israelites but they did not listen to him, because they were so discouraged and because of the hard labor they were forced to do.
Musa ya faɗa wa Isra’ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne a gare shi ba, don ɓacin rai saboda tsananin aikin bauta.
10 Then the Lord said to Moses,
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,
11 “Go and speak to Pharaoh, king of Egypt. Tell him to let the Israelites leave his country.”
“Koma ka ce wa Fir’auna sarkin Masar, yă bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa.”
12 But Moses replied, “Even my own people don't listen to me. Why would Pharaoh listen to me, especially since I'm such a poor speaker?”
Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “In Isra’ilawa ba su ji ni ba, yaya Fir’auna zai ji ni, da yake ina magana da ƙyar?”
13 But the Lord spoke to Moses and Aaron, and told them what to do regarding the people of Israel and Pharaoh, king of Egypt, in order to bring the Israelites out of Egypt.
Ubangiji ya yi magana da Musa da Haruna game da Isra’ilawa da Fir’auna sarkin Masar, ya umarce su su fitar da Isra’ilawa daga Masar.
14 These were the Israelite family heads. The sons of Reuben, the firstborn son of Israel, were Hanok and Pallu, Hezron and Karmi. These were the families of Reuben.
Waɗannan su ne shugabannin iyalansu.’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila su ne, Hanok da Fallu, Hezron da Karmi. Waɗannan su ne dangin Ruben.
15 The sons of Simeon were Jemuel, Jamin, Ohad, Jachin, Zohar, and Shaul, (the son of a Canaanite woman). These were the families of Simeon.
’Ya’yan Simeyon maza su ne, Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar da Sha’ul ɗan mutuniyar Kan’ana. Waɗannan su ne dangin Simeyon.
16 These were the names of the sons of Levi according to their genealogical records: Gershon, Kohath, and Merari. Levi lived for 137 years.
Waɗannan su ne sunayen’ya’yan Lawi maza bisa ga abin da aka rubuta, Gershon, Kohat da Merari. Lawi ya yi shekara 137.
17 The sons of Gershon, by families, were Libni and Shimei.
’Ya’yan Gershon maza, bisa ga dangi su ne, Libni da Shimeyi.
18 The sons of Kohath were Amram, Izhar, Hebron, and Uzziel. Kohath lived for 133 years.
’Ya’yan Kohat maza, su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel. Kohat ya yi shekara 133.
19 The sons of Merari were Mahli and Mushi. These were the families of the Levites according to their genealogical records.
’Ya’yan Merari maza, su ne, Mali da Mushi. Waɗannan su ne dangin Lawi bisa ga abin da aka rubuta.
20 Amram married his father's sister Jochebed, and she had their sons Aaron and Moses. Amram lived for 137 years.
Amram ya auri’yar’uwar mahaifinsa Yokebed, wadda ta haifa masa Haruna da Musa. Amram ya yi shekara 137.
21 The sons of Izhar were Korah, Nepheg, and Zichri.
’Ya’yan Izhar maza, su ne, Kora, Nefeg da Zikri.
22 The sons of Uzziel were Mishael, Elzaphan, and Sithri.
’Ya’yan Uzziyel maza, su ne, Mishayel, Elzafan da Sitri.
23 Aaron married Elisheba, daughter of Amminadab and sister of Nahshon. She had their sons Nadab and Abihu, Eleazar and Ithamar.
Haruna ya auri Elisheba,’yar Amminadab,’yar’uwar Nashon, sai ta haifa masa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar.
24 The sons of Korah were Assir, Elkanah, and Abiasaph. These were the Korahite families.
’Ya’yan Kora maza, su ne, Assir, Elkana da Abiyasaf. Waɗannan su ne dangin Kora.
25 Eleazar, son of Aaron, married one of the daughters of Putiel, and she had their son Phinehas. These are the ancestors of the Levite families, listed according to their clans. Eleazar son of Aaron married one of the daughters of Putiel, and she gave birth to his son, Phinehas. These are the heads of the Levite families, listed by family.
Eleyazar ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin’yan matan Futiyel, sai ta haifa masa Finehas. Waɗannan su ne shugabannin iyalan Lawi, dangi, dangi.
26 Aaron and Moses mentioned here are the ones the Lord told, “Lead the Israelites out of Egypt, divided up in their respective tribes.”
Wannan Haruna da Musa ne, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana ya ce, “Ku fitar da Isra’ilawa daga Masar ɓangare-ɓangare.”
27 Moses and Aaron were also the ones who went to speak with Pharaoh, king of Egypt, about the Israelites leaving Egypt.
Su ne suka yi magana da Fir’auna sarkin Masar game da fitar da Isra’ilawa daga Masar, wannan Musa da Haruna.
28 When the Lord spoke to Moses in Egypt,
Ana nan, sa’ad da Ubangiji ya yi magana da Musa a Masar,
29 he said to him, “I am the Lord. Tell Pharaoh, king of Egypt, all that I tell you.”
ya ce masa, “Ni ne Ubangiji. Sai ka faɗa wa Fir’auna sarkin Masar kome da na faɗa maka.”
30 But Moses replied, “I'm not a good speaker—why would Pharaoh listen to me?”
Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ni mai nauyin baki ne, ina magana da ƙyar, ƙaƙa Fir’auna zai kasa kunne gare ni?”

< Exodus 6 >