< 1 Kings 12 >

1 Rehoboam went to Shechem because that is where the whole of Israel had gone to make him king.
Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra’ila sun je can don su naɗa shi sarki.
2 Jeroboam, son of Nebat, was still in Egypt when he heard about this. (He had run away to Egypt to escape from King Solomon and was living there.)
Sa’ad da Yerobowam ɗan Nebat ya ji labari (gama har yanzu yana a Masar, inda ya gudu daga Sarki Solomon), sai ya dawo daga Masar.
3 The Israelite leaders sent for him. Jeroboam and the whole assembly of Israelites went to talk with Rehoboam.
Saboda haka mutane suka aika Yerobowam yă zo, sai shi da dukan taron Isra’ila suka tafi wurin Rehobowam, suka ce masa,
4 “Your father placed a heavy burden on us,” they told him. “But now if you lighten the load when we served your father and the heavy demands he put on us, we will serve you.”
“Mahaifinka ya sa mana kaya mai nauyin gaske, amma yanzu ka sassauta wannan aiki mai zafi, da kuma kaya masu nauyin da ya sa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”
5 Rehoboam answered, “Go away and come back in three days time.” So the people left.
Rehobowam ya amsa, “Ku tafi, bayan kwana uku, ku dawo.” Sai mutane suka watse.
6 King Rehoboam asked for advice from the elders who had served his father Solomon when he was alive. “How do you advise me to reply to these people about this?” he asked.
Sai Sarki Rehobowam ya nemi shawarar dattawa waɗanda suka yi wa mahaifinsa Solomon, hidima a kwanakinsa. Ya ce, “Wace shawara ce za ku ba ni don in amsa wa waɗannan mutane?”
7 They replied, “If you are a servant to these people today, if you serve them and answer them, by speaking kindly to them, they will always serve you.”
Suka amsa, “In a yau za ka zama bawan waɗannan mutane, ka kuma yi musu hidima, ka ba su amsa mai kyau, kullum za su kasance bayinka.”
8 But Rehoboam dismissed the advice of the elders. He instead asked advice from the young men who he had grown up with, and who were close to him.
Amma Rehobowam ya ƙi shawarar da dattawan suka ba shi, sai ya nemi shawarar matasa waɗanda suka yi girma tare, waɗanda kuma suke masa hidima.
9 He asked them, “What response do you advise that we send back to these people who have told me, ‘Lighten the burden your father put on us’?”
Ya tambaye su, “Mece ce shawararku? Yaya za mu amsa wa waɗannan mutane masu cewa, ‘Ka sassauta nauyin da mahaifinka ya sa a kanmu’?”
10 The young men who he had grown up with told him, “This is what you have to tell these people who said to you, ‘Your father made our burden heavy, but you should make it lighter.’ This is what you should answer them: ‘My little finger is thicker than my father's waist!
Matasan, waɗanda suka yi girma tare da shi, suka amsa, “Faɗa wa waɗannan mutanen da suka ce maka, ‘Mahaifinka ya sa kaya masu nauyi a kanmu, amma ka sassauta kayanka.’ Ka ce musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun tsohona kauri.
11 My father placed a heavy burden on you, and I will make it even heavier. My father punished you with whips; I will punish you with scorpions.’”
Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; ni zan ma sa su fi haka nauyi. Mahaifina ya hore ku da bulala; ni kuwa zan hore ku da kunamai.’”
12 Three days later, Jeroboam and all the people returned to Rehoboam, because the king had told them, “Come back in three days time.”
Bayan kwana uku, Yerobowam da dukan mutane suka dawo wurin Rehobowam yadda sarki ya faɗa, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.”
13 The king answered the people sharply. Dismissing the advice of the elders,
Sai Sarki ya amsa wa mutane da zafi. Yana ƙin shawarar da dattawa suka ba shi.
14 he replied using the advice of the young men. He said, “My father placed a heavy burden on you, and I will make it even heavier. My father punished you with whips; I will punish you with scorpions.”
Ya bi shawarar matasa, ya ce, “Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; ni zan ma sa su fi haka nauyi. Mahaifina ya hore ku da bulala; ni kuwa zan hore ku da kunamai.”
15 The king did not listen to what the people said, for this change in circumstances was from the Lord, to fulfill what the Lord had told Jeroboam son of Nebat through Ahijah the Shilonite.
Saboda haka sarki bai saurare mutane ba, gama wannan abin da ya faru daga wurin Ubangiji ne, don a cika maganar Ubangiji da ya yi wa Yerobowam ɗan Nebat ta wurin Ahiya, mutumin Shilo.
16 When all the Israelites saw that the king wasn't listening to them, they told the king: “What share do we have in David, and what part do we have in the son of Jesse? Go home, Israel! You're on your own, house of David!” So all the Israelites went home.
Da dukan Isra’ila suka ga sarki ya ƙi yă saurare su, sai suka amsa wa sarki, “Ina ruwanmu da Dawuda! Ai! Ba mu da gādo wurin ɗan Yesse. Ya Isra’ila, kowa yă koma tentinsa! Dawuda, sai ka lura da gidanka!” Saboda haka Isra’ilawa suka watse zuwa gida.
17 However, Rehoboam still ruled over the Israelites who lived in Judah.
Amma ga Isra’ilawan da suke zama a garuruwan Yahuda kuwa, Rehobowam ya ci gaba da mulki a kansu.
18 Then King Rehoboam sent out Hadoram, who was in charge of forced labor, but the Israelites stoned him to death. King Rehoboam quickly jumped into his chariot and raced back to Jerusalem.
Sarki Rehobowam ya aiki Adoniram wanda yake shugaban aikin gandu, amma Isra’ila suka jajjefe shi da dutse har ya mutu. Sarki Rehobowam, ya sullale ya hau keken yaƙinsa ya tsere zuwa Urushalima.
19 As a result, Israel has been in rebellion against the house of David to this day.
Tun daga wannan ranar ne mutanen Isra’ila suka shiga gāba da gidan Dawuda har wa yau.
20 When all the Israelites heard that Jeroboam had returned, they sent for him, summoning him to the assembly and made him king over all Israel. Only the tribe of Judah was left to the house of David.
Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ji Yerobowam ya dawo, sai suka aika, suka kira shi zuwa taro, suka kuma naɗa shi sarki bisa dukan Isra’ila. Kabila Yahuda kaɗai ta kasance mai biyayya ga gidan Dawuda.
21 When Rehoboam arrived in Jerusalem, he gathered the men from the households of Judah and Benjamin— 180,000 chosen warriors—to go and fight against Israel to bring the kingdom back to Rehoboam, son of Solomon.
Da Rehobowam ya isa Urushalima, ya tattara dukan gidan Yahuda da kabilar Benyamin, ya sami sun kai mayaƙa dubu da tamanin. Sai aka shirya don su yaƙi gidan Isra’ila, su kuma mayar da masarautar wa Rehobowam ɗan Solomon.
22 But a message from the Lord came to Shemaiah the man of God that said,
Amma waɗannan kalmomin Allah suka zo wa Shemahiya, mutumin Allah, cewa,
23 “Tell Rehoboam, son of Solomon, king of Judah, to Judah and Benjamin, and to the rest of the people:
“Faɗa wa Rehobowam ɗan Solomon, sarkin Yahuda, ka faɗa wa dukan gidan Yahuda da Benyamin, da kuma dukan sauran mutane,
24 ‘This is what the Lord says. Don't fight against your Israelite relatives. Every one of you, go home! For it was me that made this happen.’” So they obeyed what the Lord told them and went home, as the Lord had said.
‘Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kada ku haura don ku yi yaƙi da’yan’uwanku, Isra’ilawa. Ku koma gida, kowannenku, gama wannan aikina ne.”’” Saboda haka suka yi biyayya da maganar Ubangiji, suka sāke watse zuwa gida, yadda Ubangiji ya umarta.
25 Jeroboam strengthened the town of Shechem in the hill country of Ephraim and lived there. From there he went and built Penuel.
Sai Yerobowam ya ƙara gina Shekem a ƙasar tudu ta Efraim, ya zauna a can. Daga can ya tafi ya gina Fenuwel.
26 Jeroboam said to himself, “The kingdom could easily return to the house of David.
Yerobowam ya yi tunani a ransa ya ce, “Mai yiwuwa mulkin yă koma gidan Dawuda.
27 When people from here go to offer sacrifices at the Lord's Temple in Jerusalem, they will transfer their loyalty back to Rehoboam, king of Judah. Then they will kill me and go back to King Rehoboam.”
In waɗannan mutane sun riƙa haurawa don su miƙa hadayu a haikalin Ubangiji a Urushalima. Za su sāke nuna biyayya ga mai girma, Rehobowam, sarkin Yahuda. Za su kashe ni su kuma koma ga Sarki Rehobowam.”
28 So after taking advice, the king had two golden calves made, and he told the people, “Don't bother going to Jerusalem any more. Look, Israel, here are your gods who led you out of the land of Egypt.”
Bayan ya nemi shawara, sai sarki ya yi siffofin’yan maruƙa biyu na zinariya. Ya ce wa mutane, “Kun daɗe kuna haurawa zuwa can Urushalima. Ga allolinku, ya Isra’ila, waɗanda suka fitar da ku daga ƙasar Masar.”
29 He placed one in Bethel, and the other in Dan.
Sai ya kafa ɗaya a Betel, ɗaya kuma a Dan.
30 This action brought about sin, because the people went as far north as Dan to worship the idol there.
Wannan ya zama zunubi, gama mutane suna tafiya yin wa wannan da yake a Betel sujada, su kuma je har Dan don su yi wa ɗayan sujada.
31 In addition Jeroboam had shrines built on high places and appointed as priests all kinds of people who were not Levites.
Yerobowam ya gina masujadai da suke kan tuddai, ya kuma naɗa firistoci barkatai daga cikin mutanen da ba na zuriyar Lawi ba.
32 Jeroboam initiated a festival on the fifteenth day of the eighth month, just like the festival held in Judah, and he offered sacrifices on the altar. He made this offering in Bethel, sacrificing to the calves he had made, and appointed priests in Bethel for the high places he had built.
Ya kafa biki a rana ta goma sha biyar ta watan takwas, kamar bikin da ake yi a Yahuda, ya kuma miƙa hadayu a bisa bagade. Ya yi haka a Betel, yana miƙa wa siffofin maruƙan da ya yi hadayu. A Betel kuma ya naɗa firistoci a wuraren tudun da ya yi.
33 So on the fifteenth day of the eighth month, a month he had chosen himself, Jeroboam offered sacrifices on the altar he had set up in Bethel. In this way he instituted a festival for the Israelites, offering sacrifices on the altar and burning incense.
A rana ta goma sha biyar ta watan takwas, watan da ya zaɓa, ya miƙa hadayu a bisa bagaden da ya gina a Betel. Saboda haka ya kafa biki don Isra’ilawa, ya kuma haura zuwa bagade don yă miƙa hadayu.

< 1 Kings 12 >