< Romans 13 >

1 Let every soul be subject to higher powers: for there is no power but from God: and those that are, are ordained of God.
Dole kowa yă yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne.
2 Therefore he that resisteth the power, resisteth the ordinance of God. And they that resist, purchase to themselves damnation.
Saboda haka, duk wanda ya yi tawaye ga hukuma yana yin tawaye da abin da Allah ya naɗa ne, waɗanda kuwa suke aikata haka, za su jawo wa kansu hukunci.
3 For princes are not a terror to the good work, but to the evil. Wilt thou then not be afraid of the power? Do that which is good: and thou shalt have praise from the same.
Gama masu mulki ba abin tsoro ba ne ga waɗanda suke yin abin da yake daidai, sai dai ga waɗanda suke aikata laifi. Kana so ka rabu da jin tsoron wanda yake mulki? To, sai ka aikata abin da yake daidai, zai kuwa yabe ka.
4 For he is God’s minister to thee, for good. But if thou do that which is evil, fear: for he beareth not the sword in vain. For he is God’s minister: an avenger to execute wrath upon him that doth evil.
Gama shi bawan Allah ne don kyautata rayuwarka. Amma in ka aikata mugunta, to, sai ka ji tsoro, don ba a banza ne shugaba yake ɗaukan takobinsa ba. Shi fa bawan Allah ne, ta wurinsa ne fushin Allah yakan hukunta masu laifi.
5 Wherefore be subject of necessity, not only for wrath, but also for conscience’ sake.
Saboda haka, dole a yi biyayya ga hukumomi, ba don gudun horo kawai ba amma don lamirinku.
6 For therefore also you pay tribute. For they are the ministers of God, serving unto this purpose.
Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci.
7 Render therefore to all men their dues. Tribute, to whom tribute is due: custom, to whom custom: fear, to whom fear: honour, to whom honour.
Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma.
8 Owe no man any thing, but to love one another. For he that loveth his neighbour, hath fulfilled the law.
Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan.
9 For Thou shalt not commit adultery: Thou shalt not kill: Thou shalt not steal, Thou shalt not bear false witness: Thou shalt not covet: and if there be any other commandment, it is comprised in this word, Thou shalt love thy neighbour as thyself.
Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
10 The love of our neighbour worketh no evil. Love therefore is the fulfilling of the law.
Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.
11 And that knowing the season; that it is now the hour for us to rise from sleep. For now our salvation is nearer than when we believed.
Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku farka daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya.
12 The night is passed, and the day is at hand. Let us therefore cast off the works of darkness, and put on the armour of light.
Dare fa ya kusan ƙarewa; gari kuma yana gab da wayewa. Saboda haka bari mu kawar da ayyukan duhu mu kuma yafa kayan yaƙi na haske.
13 Let us walk honestly, as in the day: not in rioting and drunkenness, not in chambering and impurities, not in contention and envy:
Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba.
14 But put ye on the Lord Jesus Christ, and make not provision for the flesh in its concupiscences.
A maimakon haka, ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuma ku yi tunani game da yadda za ku gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka.

< Romans 13 >