< 1 Samuel 4 >

1 And it came to pass in those days, that the Philistines gathered themselves together to fight: and Israel went out to war against the Philistines, and camped by the Stone of help. And the Philistines came to Aphec,
Duk sa’ad da Sama’ila ya yi magana dukan Isra’ila sukan saurare shi. Isra’ilawa suka fita yaƙi da Filistiyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani a Ebenezer, Filistiyawa kuma a Afek.
2 And put their army in array against Israel. And when they had joined battle, Israel turned their backs to the Philistines, and there was slain in that fight here and there in the fields about four thousand men.
Filistiyawa suka tunƙuro mayaƙansu domin su sadu da Isra’ilawa, yaƙi kuwa ya yi tsanani har Isra’ilawa suka sha kashi a hannun Filistiyawa. Filistiyawa suka kashe Isra’ilawa kusan mutum dubu huɗu a bakin dāgā.
3 And the people returned to the camp: and the ancients of Israel said: Why hath the Lord defeated us today before the Philistines? Let us fetch unto us the ark of the covenant of the Lord from Silo, and let it come in the midst of us, that it may save us from the hand of our enemies.
Lokacin da mayaƙan suka komo sansani, dattawan Isra’ilawa suka yi tambaya suka ce, “Me ya sa Ubangiji ya sa muka sha ɗibga a hannun Filistiyawa? Bari mu kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Shilo. Domin yă tafi tare da mu yă ba mu nasara kan abokan gābanmu.”
4 So the people sent to Silo, and they brought from thence the ark of the covenant of the Lord of hosts sitting upon the cherubims: and the two sons of Heli, Ophni and Phinees, were with the ark of the covenant of God.
Saboda haka mutanen suka aika waɗansu maza zuwa Shilo, suka kuwa tafi suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Maɗaukaki wanda yake zaune tsakanin Kerubobi.’Ya’yan Eli biyun nan Hofni da Finehas suna wurin tare da akwatin alkawarin Ubangiji.
5 And when the ark of the covenant of the Lord was come into the camp, all Israel shouted with a great shout, and the earth rang again.
Da aka shigo da akwatin alkawarin Ubangiji a cikin sansani, sai Isra’ilawa suka tā da babbar murya har ƙasa ta jijjiga.
6 And the Philistines heard the noise of the shout, and they said: What is this noise of a great shout in the camp of the Hebrews? And they understood that the ark of the Lord was come into the camp.
Da jin wannan, Filistiyawa suka yi tambaya suka ce, “Me ke kawo wannan ihu mai ƙarfi haka a sansanin Isra’ilawa?” Da suka gane cewa akwatin alkawarin Ubangiji ne ya shiga sansanin,
7 And the Philistines were afraid, saying: God is come into the camp. And sighing, they said:
sai Filistiyawa suka ji tsoro, suka ce, “Wani allah ya shiga cikin sansanin. Mun shiga uku! Ba a taɓa yin wani abu haka ba.
8 Woe to us: for there was no such great joy yesterday and the day before: Woe to us. Who shall deliver us from the hand of these high gods? these are the gods that struck Egypt with all the plagues in the desert.
Kaiton mu! Wa zai kuɓutar da mu daga hannun waɗannan manyan alloli? Su ne allolin da suka buga Masarawa da irin annoba masu yawa a jeji.
9 Take courage and behave like men, ye Philistines: lest you come to be servants to the Hebrews, as they have served you: take courage and fight.
Ku yi ƙarfin hali, ku yi mazantaka, ku Filistiyawa, domin kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suke a gare ku. Ku yi mazantaka, ku yi yaƙi.”
10 So the Philistines fought, and Israel was overthrown, and every man fled to his own dwelling: and there was an exceeding great slaughter; for there fell of Israel thirty thousand footmen.
Saboda haka Filistiyawa suka yi yaƙi, Isra’ilawa kuwa suka sha ɗibga, kowane mutum kuwa ya gudu zuwa tentinsa. Kisan kuwa ya yi muni ƙwarai. Isra’ilawa sun rasa mayaƙa dubu talatin.
11 And the ark of God was taken: and the two sons of Heli, Ophni and Phinees, were slain.
Aka ƙwace akwatin alkawarin Ubangiji. Aka kuma kashe’ya’yan Eli biyu, Hofni da Finehas.
12 And there ran a man of Benjamin out of the army, and came to Silo the same day, with his clothes rent, and his head strewed with dust.
A wannan rana wani mutumin Benyamin ya ruga da bakin dāgā ya shigo Shilo, taguwarsa a yage, kansa kuma a rufe da ƙasa.
13 And when he was come, Heli sat upon a stool over against the way watching. For his heart was fearful for the ark of God. And when the man was come into the city, he told it: and all the city cried out.
Da ya iso sai ga Eli zaune a kujera kusa da hanya yana kallo, domin tsoron da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Da mutumin ya shigo a garin ya ba da labarin abin da ya faru sai dukan gari ya ruɗe da ihu.
14 And Heli heard the noise of the cry, and he said: What meaneth the noise of this uproar? But he made haste, and came, and told Heli.
Eli ya ji ihun ya yi tambaya ya ce, mene ne dalilin wannan ihu? Mutumin ya rugo wurin Eli,
15 Now Heli was ninety and eight years old, and his eyes were dim, and he could not see.
wanda yake da shekaru tasa’in da takwas da haihuwa, idanunsa kuma ƙarfi ya ƙare, baya iya gani.
16 And he said to Heli: I am he that came from the battle, and have fled out of the field this day. And he said to him: What is there done, my son?
Mutumin ya gaya wa Eli cewa, “Shigowata ke nan daga bakin dāgā. Na kuɓuce daga can yau ɗin nan.” Eli ya ce, “Me ya faru da’ya’yana?”
17 And he that brought the news answered, and said: Israel has fled before the Philistines, and there has been a great slaughter of the people: moreover thy two sons, Ophni and Phinees, are dead: and the ark of God is taken.
Mutumin da ya kawo labarin ya ce, “Isra’ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, mayaƙan kuma sun sha mummunar ɗibga.’Ya’yanka Hofni da Finehas su ma sun mutu. Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”
18 And when he had named the ark of God, he fell from his stool backwards by the door, and broke his neck, and died. For he was an old man, and far advanced in years: and he judged Israel forty years.
Da ya ambaci akwatin alkawarin Allah, sai Eli ya fāɗi da baya daga kujeransa kusa da ƙofa, wuyarsa ta karye, ya kuma mutu domin ya tsufa ƙwarai. Ya yi shugabancin Isra’ila shekaru arba’in.
19 And his daughter in law the wife of Phinees, was big with child, and near her time: and hearing the news that the ark of God was taken, and her father in law, and her husband, were dead, she bowed herself and fell in labour: for her pains came upon her on a sudden.
Matar Finehas, ɗansa tana da ciki a lokacin ta kuma kusa haihuwa. Sa’ad da ta ji labari cewa an ƙwace akwatin alkawarin Allah, ta kuma labarin surukinta da mijinta sun mutu, sai ta shiga naƙuda, ta kuma haihu. Amma naƙuda ta sha ƙarfinta.
20 And when she was upon the point of death, they that stood about her said to her: Fear not, for thou hast borne a son. She answered them not, nor gave heed to them.
Da tana mutuwa, matan da suke lura da ita suka ce, “Kada ki karaya kin haifi ɗa namiji.” Amma ba tă ba da amsa ko tă kula ba.
21 And she called the child Ichabod, saying: The glory is gone from Israel, because the ark of God was taken, and for her father in law, and her husband:
Ta ba wa yaron suna Ikabod, ma’ana “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila”, domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma mutuwar surukinta da na mijinta.
22 And she said: The glory is departed from Israel, because the ark of God was taken.
Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”

< 1 Samuel 4 >