< Matthew 4 >

1 Then Jesus was carried up into the wilderness by the Spirit to be tempted of the devil:
Sa'an nan Ruhu ya bi da Yesu zuwa cikin jeji, domin Ibilis ya gwada shi.
2 and having fasted forty days and forty nights, afterwards he hungered.
Da ya yi azumi kwana arba'in dare da rana, daga baya yunwa ta kama shi.
3 And the tempter coming up to him said, If thou be Son of God, speak, that these stones may become loaves of bread.
Sai mai jarabtar nan ya zo, ya ce masa, “Idan kai Dan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.”
4 But he answering said, It is written, Man shall not live by bread alone, but by every word which goes out through God's mouth.
Amma Yesu ya amsa ya ce masa, “A rubuce yake cewa, 'Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace magana da ta ke fitowa daga wurin Allah.'''
5 Then the devil takes him to the holy city, and sets him upon the edge of the temple,
Sa'an nan Ibilis ya kai shi tsattsarkan birni ya dora shi can kan kololuwar ginin haikali,
6 and says to him, If thou be Son of God cast thyself down; for it is written, He shall give charge to his angels concerning thee, and on [their] hands shall they bear thee, lest in anywise thou strike thy foot against a stone.
ya ce masa, “In kai Dan Allah ne, to dira kasa. Domin a rubuce yake cewa, 'Zai ba mala'ikunsa umarni game da kai,' kuma, 'Za su daga ka da hannuwansu, domin kada ka yi tuntube da dutse.'''
7 Jesus said to him, It is again written, Thou shalt not tempt [the] Lord thy God.
Yesu ya ce masa, “kuma a rubuce yake, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.'''
8 Again the devil takes him to a very high mountain, and shews him all the kingdoms of the world, and their glory,
Kuma, sai Ibilis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo kwarai, ya nuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu.
9 and says to him, All these things will I give thee if, falling down, thou wilt do me homage.
Ya ce masa, “Dukan wadannan zan baka idan ka rusuna ka yi mani sujada.''
10 Then says Jesus to him, Get thee away, Satan, for it is written, Thou shalt do homage to [the] Lord thy God, and him alone shalt thou serve.
Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.'''
11 Then the devil leaves him, and behold, angels came and ministered to him.
Sa'an nan Ibilis ya rabu da shi, sai kuma mala'iku suka zo suka yi masa hidima.
12 But having heard that John was delivered up, he departed into Galilee:
To, da Yesu ya ji an kama Yahaya, sai ya tashi zuwa kasar Galili.
13 and having left Nazareth, he went and dwelt at Capernaum, which is on the sea-side in the borders of Zabulon and Nepthalim,
Ya bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin tekun Galili, kan iyakar kasar Zabaluna da Naftali.
14 that that might be fulfilled which was spoken through Esaias the prophet, saying,
Wannan ya faru domin a cika fadar annabi Ishaya cewa,
15 Land of Zabulon and land of Nepthalim, way of [the] sea beyond the Jordan, Galilee of the nations:
“Kasar Zabaluna da kasar Naftali, ta bakin teku, da hayin Kogin Urdun, Galili ta al'ummai!
16 — the people sitting in darkness has seen a great light, and to those sitting in [the] country and shadow of death, to them has light sprung up.
Mutane mazauna duhu suka ga babban haske, sannan ga wadanda ke zaune a yankin da inuwar mutuwa, haske ya keto masu.”
17 From that time began Jesus to preach and to say, Repent, for the kingdom of the heavens has drawn nigh.
Daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin mulkin sama ya kusa.”
18 And walking by the sea of Galilee, he saw two brothers, Simon called Peter, and Andrew his brother, casting a net into the sea, for they were fishers;
Yana tafiya a bakin tekun Galili, sai ya ga wadansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, domin su masunta ne.
19 and he says to them, Come after me, and I will make you fishers of men.
Yesu ya ce masu, “Ku zo, ku biyo ni, zan mai da ku masuntan mutane.”
20 And they, having left their trawl-nets, immediately followed him.
Nan da nan sai suka bar tarunsu, suka bi shi.
21 And going on thence he saw other two brothers, James the [son] of Zebedee and John his brother, in the ship with Zebedee their father, mending their trawl-nets, and he called them;
Da Yesu ya ci gaba da tafiya, sai ya ga wadansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da mahaifinsu Zabadi, suna gyaran tarunsu. Sai ya kira su.
22 and they, having left the ship and their father, immediately followed him.
Nan take suka bar mahaifinsu da jirgin, suka bi shi.
23 And [Jesus] went round the whole [of] Galilee, teaching in their synagogues, and preaching the glad tidings of the kingdom, and healing every disease and every bodily weakness among the people.
Yesu ya zazzaga dukan kasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar mulkin, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya a cikin mutane.
24 And his fame went out into the whole [of] Syria, and they brought to him all that were ill, suffering under various diseases and pains, and those possessed by demons, and lunatics, and paralytics; and he healed them.
Labarinsa ya bazu a cikin dukan kasar Suriya, kuma mutanen suka kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farfadiya, da shanyayyu. Yesu ya warkar da su.
25 And great crowds followed him from Galilee, and Decapolis, and Jerusalem, and Judaea, and beyond the Jordan.
Taro masu yawa suka bi shi daga kasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da kasar Yahudiya, har ma daga hayin Urdun.

< Matthew 4 >