< Exodus 11 >

1 And the Lord said to Moses: “I will touch Pharaoh and Egypt with one more plague, and after these things he will release you, and he will compel you to go out.
To, fa, sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan ƙara kawo annoba guda a kan Fir’auna da kan Masar. Bayan haka, zai bar ku, ku fita daga nan. Sa’ad da ya yi haka kuwa, zai kore ku gaba ɗaya.
2 Therefore, you will tell all the people to ask, a man of his friend, and a woman of her neighbor, for vessels of silver and of gold.
Ka faɗa wa mutane cewa dukan maza da mata, su roƙi maƙwabtansu kayan azurfa da na zinariya.”
3 Then the Lord will grant favor to his people in the sight of the Egyptians.” And Moses was a very great man in the land of Egypt, in the sight of the servants of Pharaoh and of all the people.
(Ubangiji ya sa mutane suka sami tagomashi a idon Masarawa, Musa kuwa ya sami girma sosai a cikin ƙasar Masar a gaban fadawan Fir’auna da kuma a gaban jama’ar.)
4 And he said: “Thus says the Lord: ‘In the middle of the night I will enter into Egypt.
Saboda haka Musa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Wajen tsakar dare, zan ratsa dukan Masar.
5 And every firstborn in the land of the Egyptians shall die, from the firstborn of Pharaoh, who sits on his throne, even to the firstborn of the handmaid, who is at the millstone, and all the firstborn of the beasts of burden.
Kowane ɗan fari, namiji, a Masar zai mutu, daga kan ɗan fari na Fir’auna wanda zai ci gadon sarauta, har zuwa kan ɗan fari na baiwa, wadda take niƙa, da kuma dukan’yan farin shanu.
6 And there will be a great outcry throughout the entire land of Egypt, such as has not been before, nor ever will be afterward.
Za a yi kuka mai zafi ko’ina a Masar, irin wadda ba a taɓa yi ba, ba kuwa za a ƙara yi ba.
7 But among all the sons of Israel there shall not be even a mutter from a dog, from man, even to cattle, so that you may know how miraculously the Lord divides the Egyptians from Israel.’
Amma a cikin Isra’ilawa, ba karen da zai yi haushi wa mutum ko dabba.’ Ta haka za ku sani Ubangiji zai bambanta tsakanin Masar da Isra’ila.
8 And all these, your servants, shall descend to me and shall reverence me, by saying: ‘Depart, you and all the people who are subject to you.’ After these things, we will depart.”
Dukan fadawan nan naka za su zo wurina, suna fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama’arka!’ Sa’an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir’auna a husace.
9 And he went out from Pharaoh exceedingly angry. Then the Lord said to Moses: “Pharaoh will not listen to you, so that many signs may be accomplished in the land of Egypt.”
Ubangiji ya ce wa Musa, “Fir’auna zai ƙi kasa kunne gare ka, sai na ƙara aikata waɗansu mu’ujizai cikin Masar.”
10 Now Moses and Aaron did all the wonders that are written, in the sight of Pharaoh. And the Lord hardened the heart of Pharaoh; neither did he release the sons of Israel from his land.
Musa da Haruna suka aikata dukan waɗannan mu’ujizai a gaban Fir’auna, amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa bar Isra’ilawa su fita daga ƙasarsa ba.

< Exodus 11 >