< Song of Solomon 2 >

1 I am a rose of Sharon, A lily of the valleys.
Ni furen bi-rana ne na Sharon, furen bi-rana na kwari.
2 As a lily among thorns, So is my love among the daughters.
Kamar furen bi-rana a cikin ƙayayyuwa haka ƙaunatacciyata take a cikin’yan mata.
3 As the apple-tree among the trees of the wood, So is my beloved among the sons. I sat down under his shadow with great delight, And his fruit was sweet to my taste.
Kamar itacen gawasa a cikin itatuwan jeji haka ƙaunataccena yake a cikin samari. Ina farin ciki in zauna a inuwarsa,’ya’yan itacensa suna da daɗin ɗanɗanon da nake so
4 He brought me to the banqueting-house, And his banner over me was love.
Ya kai ni babban zauren da ake liyafa, ƙauna ita ce tutarsa a gare ni.
5 Stay ye me with raisins, refresh me with apples; For I am sick from love.
Ka ƙarfafa ni da zabibi ka wartsake ni da gawasa, gama ina suma don ƙauna.
6 His left hand [is] under my head, And his right hand doth embrace me.
Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina, hannunsa na dama kuma ya rungume ni.
7 I adjure you, O daughters of Jerusalem, By the roes, or by the hinds of the field, That ye stir not up, nor awake [my] love, Until he please.
’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari da bareyi da ƙishimai na jeji. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle.
8 The voice of my beloved! behold, he cometh, Leaping upon the mountains, Skipping upon the hills.
Saurara! Ƙaunataccena! Duba! Ga shi ya iso, yana tsalle a duwatsu, yana rawa a bisa tuddai.
9 My beloved is like a roe or a young hart: Behold, he standeth behind our wall; He looketh in at the windows; He glanceth through the lattice.
Ƙaunataccena yana kama da barewa ko sagarin ƙishimi Duba! Ga shi can tsaye a bayan katangarmu, yana leƙe ta tagogi, yana kallo ta cikin asabari.
10 My beloved spake, and said unto me, Rise up, my love, my fair one, and come away.
Ƙaunataccena ya yi magana ya ce mini, “Tashi, ƙaunatacciyata, kyakkyawata, ki zo tare da ni.
11 For, lo, the winter is past; The rain is over and gone;
Duba! Damina ta wuce; ruwan sama ya ɗauke ya kuma ƙare.
12 The flowers appear on the earth; The time of the singing [of birds] is come, And the voice of the turtle-dove is heard in our land;
Furanni sun hudo a duniya; lokaci yin waƙa ya zo, ana jin kukan kurciyoyi ko’ina a ƙasarmu.
13 The fig-tree ripeneth her green figs, And the vines are in blossom; They give forth their fragrance. Arise, my love, my fair one, and come away.
Itacen ɓaure ya fid da’ya’yansa da sauri; tohon inabi suna ba da ƙanshinsu. Tashi, zo, ƙaunatacciyata; kyakkyawata, zo tare da ni.”
14 O my dove, that art in the clefts of the rock, In the covert of the steep place, Let me see thy countenance, Let me hear thy voice; For sweet is thy voice, and thy countenance is comely.
Kurciyata a kogon dutse, a wuraren ɓuya a gefen dutse, nuna mini fuskarki, bari in ji muryarki; gama muryarki da daɗi take, fuskarki kuma kyakkyawa ce.
15 Take us the foxes, the little foxes, That spoil the vineyards; For our vineyards are in blossom.
Kama mana ɓeraye, ƙananan ɓerayen da suke lalatar da gonakin inabi, gonakin inabinmu da suke cikin yin fure.
16 My beloved is mine, and I am his: He feedeth [his flock] among the lilies.
Ƙaunataccena nawa ne ni kuma tasa ce; yana kiwon garkensa a cikin furannin bi-rana.
17 Until the day be cool, and the shadows flee away, Turn, my beloved, and be thou like a roe or a young hart Upon the mountains of Bether.
Sai gari ya waye inuwa kuma ta watse, ka juye, ƙaunataccena, ka zama kamar barewa ko kamar sagarin ƙishimi a kan tuddai masu ciyawa.

< Song of Solomon 2 >