< John 4 >

1 When therefore the Lord knew that the Pharisees had heard that Jesus was making and baptizing more disciples than John
Da Yesu ya sani cewa Farisawa sun ji cewa yana samun almajirai yana kuma yi masu baftisma fiye da Yahaya
2 (although Jesus himself baptized not, but his disciples),
(ko da shike ba Yesu da kansa ke yin baftismar ba, amma almajiransa ne),
3 he left Judæa, and departed again into Galilee.
ya bar Yahudiya ya koma Galili.
4 And he must needs pass through Samaria.
Amma ya zamar masa dole ya ratsa ta Samariya.
5 So he cometh to a city of Samaria, called Sychar, near to the parcel of ground that Jacob gave to his son Joseph:
Ya zo wani birnin Samariya, mai suna Sika, kusa da filin da Yakubu ya ba dansa Yusufu.
6 and Jacob’s well was there. Jesus therefore, being wearied with his journey, sat thus by the well. It was about the sixth hour.
Rijiyar Yakubu na wurin. Da Yesu ya gaji da tafiyarsa sai ya zauna gefen rijiyar. Kusan karfe goma sha biyu na rana ne.
7 There cometh a woman of Samaria to draw water: Jesus saith unto her, Give me to drink.
Wata mace, Ba-Samariya ta zo domin ta dibi ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha.”
8 For his disciples were gone away into the city to buy food.
Gama almajiransa sun tafi cikin gari don sayen abinci.
9 The Samaritan woman therefore saith unto him, How is it that thou, being a Jew, askest drink of me, who am a Samaritan woman? (For Jews have no dealings with Samaritans.)
Sai ba-Samariyar tace masa, “Yaya kai da kake Bayahude kake tambaya ta ruwan sha, ni da nike 'yar Samariya?” Domin Yahudawa ba su harka da Samariyawa.
10 Jesus answered and said unto her, If thou knewest the gift of God, and who it is that saith to thee, Give me to drink; thou wouldest have asked of him, and he would have given thee living water.
Sai Yesu ya amsa yace mata, “In da kin san kyautar Allah, da shi wanda yake ce da ke, 'Ba ni ruwan sha,' da kin roke shi, sai kuma ya ba ki ruwan rai.”
11 The woman saith unto him, Sir, thou hast nothing to draw with, and the well is deep: whence then hast thou that living water?
Matar tace masa, “Mallam, ga shi ba ka da guga, kuma rijiyar tana da zurfi. Ina za ka samu ruwan rai?
12 Art thou greater than our father Jacob, who gave us the well, and drank thereof himself, and his sons, and his cattle?
Ai ba ka fi Ubanmu Yakubu ba, ko ka fi shi, shi wanda ya ba mu rijiyar, shi kansa kuma ya sha daga cikin ta, haka kuma 'ya'yansa da shanunsa?”
13 Jesus answered and said unto her, Every one that drinketh of this water shall thirst again:
Yesu ya amsa yace mata, “duk wanda ya sha daga wannan ruwan zai sake jin kishi,
14 but whosoever drinketh of the water that I shall give him shall never thirst; but the water that I shall give him shall become in him a well of water springing up unto eternal life. (aiōn g165, aiōnios g166)
amma duk wanda ya sha daga ruwa da zan ba shi ba zai sake jin kishi ba. Maimakon haka, ruwan da zan bashi zai zama mabulbular ruwa a cikinsa wanda ke bulbula zuwa rai madawwami.” (aiōn g165, aiōnios g166)
15 The woman saith unto him, Sir, give me this water, that I thirst not, neither come all the way hither to draw.
Matar tace masa, “Mallam, ka ba ni wannan ruwa yadda ba zan kara jin kishi ba ba kuma sai na zo nan don in dibi ruwa ba.”
16 Jesus saith unto her, Go, call thy husband, and come hither.
Yesu ya ce mata, “Je, ki kira maigidanki ku zo nan tare.”
17 The woman answered and said unto him, I have no husband. Jesus saith unto her, Thou saidst well, I have no husband:
Matar ta amsa tace masa, “Ba ni da miji.” Yesu yace, “Kin fadi daidai da kika ce, 'ba ni da miji,'
18 for thou hast had five husbands; and he whom thou now hast is not thy husband: this hast thou said truly.
domin kin auri mazaje har biyar, kuma wanda kike da shi yanzu ba mijin ki bane. Abinda kika fada gaskiya ne.”
19 The woman saith unto him, Sir, I perceive that thou art a prophet.
Matar tace masa, “Mallam, Na ga kai annabi ne.
20 Our fathers worshipped in this mountain; and ye say, that in Jerusalem is the place where men ought to worship.
Ubaninmu sun yi sujada a wannan dutse, amma kun ce Urushalima ce wurin da ya kamata mutane su yi sujada.”
21 Jesus saith unto her, Woman, believe me, the hour cometh, when neither in this mountain, nor in Jerusalem, shall ye worship the Father.
Yesu ya ce mata, “Mace, ki gaskata ni, cewa lokaci na zuwa wanda ba za ku yi wa Uban sujada ba ko akan wannan dutse ko a Urushalima.
22 Ye worship that which ye know not: we worship that which we know; for salvation is from the Jews.
Ku kuna bauta wa abinda ba ku sani ba. Mu muna bauta wa abinda muka sani, gama ceto daga Yahudawa yake.
23 But the hour cometh, and now is, when the true worshippers shall worship the Father in spirit and truth: for such doth the Father seek to be his worshippers.
Sai dai, sa'a tana zuwa, har ma ta yi, wadda masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a cikin ruhu da gaskiya, domin irin wadannan ne Uban ke nema su zama masu yi masa sujada.
24 God is a Spirit: and they that worship him must worship in spirit and truth.
Allah Ruhu ne, kuma mutanen da ke yi masa sujada, dole su yi sujada cikin ruhu da gaskiya.”
25 The woman saith unto him, I know that Messiah cometh (he that is called Christ): when he is come, he will declare unto us all things.
Matar ta ce masa, “Na san Almasihu na zuwa (wanda ake kira Kristi). Sa'adda ya zo, zai bayyana mana kowane abu.
26 Jesus saith unto her, I that speak unto thee am [he].
Yesu ya ce mata, “Ni ne shi, wanda ke yi maki magana.”
27 And upon this came his disciples; and they marvelled that he was speaking with a woman; yet no man said, What seekest thou? or, Why speakest thou with her?
A daidai wannan lokaci, almajiransa suka dawo. Suna ta mamakin dalilin da yasa yake magana da mace, amma babu wanda yace, “Me kake so?” Ko kuma, “Don me ka ke magana da ita?”
28 So the woman left her waterpot, and went away into the city, and saith to the people,
Sai matar ta bar tulunta, ta koma cikin gari, tace wa mutanen,
29 Come, see a man, who told me all things that [ever] I did: can this be the Christ?
“Ku zo ku ga wani mutum wanda ya gaya mani duk wani abu da na taba yi. Wannan dai ba Almasihun bane, ko kuwa?”
30 They went out of the city, and were coming to him.
Suka bar garin suka zo wurinsa.
31 In the mean while the disciples prayed him, saying, Rabbi, eat.
A wannan lokacin, almajiransa suna rokansa, cewa, “Mallam, ka ci.”
32 But he said unto them, I have meat to eat that ye know not.
Amma ya ce masu, “ina da abinci da ba ku san komai akai ba.”
33 The disciples therefore said one to another, Hath any man brought him [aught] to eat?
Sai almajiran suka ce da junansu, “Babu wanda ya kawo masa wani abu ya ci, ko akwai ne?”
34 Jesus saith unto them, My meat is to do the will of him that sent me, and to accomplish his work.
Yesu ya ce masu, “Abincina shine in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.
35 Say not ye, There are yet four months, and [then] cometh the harvest? behold, I say unto you, Lift up your eyes, and look on the fields, that they are white already unto harvest.
Ba ku kan ce, 'akwai wata hudu tukuna kafin girbi ya zo ba?' Ina gaya maku, daga idanunku ku ga gonakin, sun rigaya sun isa girbi.
36 He that reapeth receiveth wages, and gathereth fruit unto life eternal; that he that soweth and he that reapeth may rejoice together. (aiōnios g166)
Shi wanda ke girbi yakan karbi sakamako ya kuma tattara amfanin gona zuwa rai na har abada, ta haka shi mai shuka da shi mai girbi za su yi farinciki tare. (aiōnios g166)
37 For herein is the saying true, One soweth, and another reapeth.
Gama cikin wannan maganar take, 'Wani na shuka, wani kuma na girbi.'
38 I sent you to reap that whereon ye have not labored: others have labored, and ye are entered into their labor.
Na aike ku ku yi girbin abinda ba ku yi aiki a kai ba. Wandansu sun yi aiki, ku kuma kun shiga cikin wahalarsu.
39 And from that city many of the Samaritans believed on him because of the word of the woman, who testified, He told me all things that [ever] I did.
Yawancin Samariyawan da ke wannan birni suka gaskata da shi sabili da labarin matar data bada shaida, “Ya gaya mani duk abinda na taba yi.”
40 So when the Samaritans came unto him, they besought him to abide with them: and he abode there two days.
To sa'adda Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roke shi ya zauna tare da su, ya kuwa zauna wurin kwana biyu.
41 And many more believed because of his word;
Wasu da dama kuma suka gaskata domin maganarsa.
42 and they said to the woman, Now we believe, not because of thy speaking: for we have heard for ourselves, and know that this is indeed the Saviour of the world.
Suka cewa matar, “Mun bada gaskiya, ba saboda maganar ki kadai ba, amma mu kanmu munji, yanzu kuma mun sani cewa wannan lallai shine mai ceton duniya.”
43 And after the two days he went forth from thence into Galilee.
Bayan wadannan kwana biyu, ya bar wurin zuwa Galili.
44 For Jesus himself testified, that a prophet hath no honor in his own country.
Domin Yesu da kansa yace, ba a girmama annabi a kasarsa.
45 So when he came into Galilee, the Galilæans received him, having seen all the things that he did in Jerusalem at the feast: for they also went unto the feast.
Da ya zo Galili, Galiliyawan suka marabce shi. Sun ga dukan abubuwan da ya yi a Urushalima wurin idin, domin su ma sun je idin.
46 He came therefore again unto Cana of Galilee, where he made the water wine. And there was a certain nobleman, whose son was sick at Capernaum.
Kuma ya koma Kana ta Galili inda ya mayar da ruwa zuwa ruwan inabi. Akwai wani ma'aikacin fada wanda dansa na rashin lafiya a Kafarnahum.
47 When he heard that Jesus was come out of Judæa into Galilee, he went unto him, and besought [him] that he would come down, and heal his son; for he was at the point of death.
Da ya ji cewa Yesu ya bar Yahudiya ya koma Galili, sai ya tafi wurin Yesu ya roke shi ya sauko ya warka da dansa wanda ke bakin mutuwa.
48 Jesus therefore said unto him, Except ye see signs and wonders, ye will in no wise believe.
Yesu yace masa, “Idan ba ku ga alamu da mu'ujizai ba, ba za ku gaskata ba.”
49 The nobleman saith unto him, Sir, come down ere my child die.
Ma'aikacin ya ce masa, “Mallam, ka sauko kafin da na ya mutu.”
50 Jesus saith unto him, Go thy way; thy son liveth. The man believed the word that Jesus spake unto him, and he went his way.
Yesu yace masa, “Je ka. Dan ka ya rayu.” Mutumin ya gaskata maganar da Yesu ya gaya masa, Sai yayi tafiyarsa.
51 And as he was now going down, his servants met him, saying, that his son lived.
Yayin da yake sauka kasa, bayinsa suka same shi, suna cewa, danka yana raye.
52 So he inquired of them the hour when he began to amend. They said therefore unto him, Yesterday at the seventh hour the fever left him.
Sai ya tambaye su sa'ar da ya fara samun sauki. Suka amsa masa, “Jiya a sa'a ta bakwai zazabin ya bar shi.”
53 So the father knew that [it was] at that hour in which Jesus said unto him, Thy son liveth: and himself believed, and his whole house.
Sai Uban ya gane cewa wannan sa'a ce Yesu ya ce masa, “Jeka, danka na raye.” Sabili da haka, shi da dukan gidansa suka bada gaskiya.
54 This is again the second sign that Jesus did, having come out of Judæa into Galilee.
Wannan ce alama ta biyu da Yesu ya yi bayan da ya bar Yahudiya zuwa Galili.

< John 4 >