< Matthew 15 >

1 Then Pharisees and scribes came to Jesus from Jerusalem, saying,
Sai wadansu Farisawa da malamai suka zo wurin Yesu daga Urushalima. Su ka ce,
2 “Why do your disciples disobey the tradition of the elders? For they do not wash their hands when they eat bread.”
“Meyasa almajiranka suke karya al'adar dattawa? Don ba su wanke hannayen su kafin su ci abinci.”
3 He answered them, “Why do you also disobey the commandment of God because of your tradition?
Yesu ya amsa masu ya ce, “Kuma don me ku ke karya dokar Allah saboda al'adunku?
4 For God commanded, ‘Honor your father and your mother,’ and, ‘He who speaks evil of father or mother, let him be put to death.’
Domin Allah ya ce, 'Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka; 'Shi wanda ya yi muguwar magana ga mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lallai zai mutu.
5 But you say, ‘Whoever may tell his father or his mother, “Whatever help you might otherwise have gotten from me is a gift devoted to God,”
Amma kun ce, “Duk wanda ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, “Kowanne taimako da za ka samu daga gare ni yanzu baiko ne ga Allah,'”
6 he shall not honor his father or mother.’ You have made the commandment of God void because of your tradition.
wannan mutum ba ya bukatar ya girmama mahaifinsa. Ta wannan hanya kun maida maganar Allah wofi saboda al'adunku.
7 You hypocrites! Well did Isaiah prophesy of you, saying,
Ku munafukai, daidai ne Ishaya ya yi annabci akan ku da ya ce,
8 ‘These people draw near to me with their mouth, and honor me with their lips; but their heart is far from me.
“Wadannan mutane girmama ni da baki kawai suke yi, amma zukatansu nesa suke da ni.
9 And they worship me in vain, teaching as doctrine rules made by men.’”
Suna mani sujada a banza, domin suna koyar da dokokin mutane a matsayin rukunansu.”
10 He summoned the multitude, and said to them, “Hear, and understand.
Sai ya kira taron mutane zuwa gare shi ya ce masu, “Ku saurara ku fahimta,
11 That which enters into the mouth does not defile the man; but that which proceeds out of the mouth, this defiles the man.”
ba abin da ke shiga baki ke kazantar da mutum ba. Sai dai, abin da ke fitowa daga baki, wannan shi ya ke kazantar da mutum.”
12 Then the disciples came and said to him, “Do you know that the Pharisees were offended when they heard this saying?”
Sai al'majiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisawa ba su ji dadi ba da suka ji maganan nan?”
13 But he answered, “Every plant which my heavenly Father did not plant will be uprooted.
Yesu ya amsa ya ce, “Kowace shuka wadda ba Ubana na sama ya shuka ba za a tuge ta.
14 Leave them alone. They are blind guides of the blind. If the blind guide the blind, both will fall into a pit.”
Ku kyale su kawai, su makafin jagora ne. In makaho ya ja wa wani makaho gora dukan su za su fada rami.”
15 Peter answered him, “Explain the parable to us.”
Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, “Ka bayyana wannan misali a garemu,”
16 So Jesus said, “Do you also still not understand?
Yesu ya ce, “Ku ma har yanzu ba ku da fahimta?
17 Do not you understand that whatever goes into the mouth passes into the belly and then out of the body?
Ko baku gani ba duk abin da ke shiga baki zuwa ciki ta haka yake fita zuwa salga?
18 But the things which proceed out of the mouth come out of the heart, and they defile the man.
Amma abubuwan da ke fita daga baki suna fitowa ne daga zuciya. Su ne abubuwan da ke kazantar da mutum.
19 For out of the heart come evil thoughts, murders, adulteries, sexual sins, thefts, false testimony, and blasphemies.
Domin daga zuciya mugayen tunani suke fitowa, kisan kai, zina, fasikanci, sata, shaidar zur, da zage-zage.
20 These are the things which defile the man; but to eat with unwashed hands does not defile the man.”
Wadannan su ne abubuwan da ke kazantar da mutum. Amma ci da rashin wanke hannu baya kazantar da mutum.”
21 Jesus went out from there and withdrew into the region of Tyre and Sidon.
Sai Yesu ya tafi daga nan ya nufi yankin biranen Taya da Sidon.
22 Behold, a Canaanite woman came out from those borders and cried, saying, “Have mercy on me, Lord, you son of David! My daughter is severely possessed by a demon!”
Sai wata mace Bakan'aniya ta zo daga wannan yanki. Ta daga murya ta ce,” Ka yi mani jinkai, Ubangiji, Dan Dauda; 'yata tana cikin bakar azaba da aljani.”
23 But he answered her not a word. His disciples came and begged him, saying, “Send her away; for she cries after us.”
Amma Yesu bai ce mata kome ba. Almajiransa suka zo suka roke shi, suna cewa, “Ka sallame ta, domin tana bin mu da ihu.”
24 But he answered, “I was not sent to anyone but the lost sheep of the house of Israel.”
Amma Yesu ya amsa ya ce, “Ba a aike ni gun kowa ba sai dai ga batattun tumakin gidan Isra'ila.”
25 But she came and worshiped him, saying, “Lord, help me.”
Amma ta zo ta durkusa a gabansa, tana cewa, “Ubangiji ka taimake ni.”
26 But he answered, “It is not appropriate to take the children’s bread and throw it to the dogs.”
Ya amsa ya ce, “Ba daidai bane a dauki gurasar yara a jefa wa kananan karnuka.
27 But she said, “Yes, Lord, but even the dogs eat the crumbs which fall from their masters’ table.”
Ta ce, “I, Ubangiji, amma ko kananan karnuka suna cin barbashin da ke fadowa daga teburin maigida.”
28 Then Jesus answered her, “Woman, great is your faith! Be it done to you even as you desire.” And her daughter was healed from that hour.
Sai Yesu ya amsa ya ce mata, “Mace, bangaskiyarki tana da girma. Bari ya zamar maki yadda ki ke so.”'Yarta ta warke a lokacin.
29 Jesus departed from there and came near to the sea of Galilee; and he went up on the mountain and sat there.
Yesu ya bar wurin ya tafi kusa da tekun Galili. Sai ya hau tudu ya zauna a can.
30 Great multitudes came to him, having with them the lame, blind, mute, maimed, and many others, and they put them down at his feet. He healed them,
Taro mai yawa suka zo gunsa. Suka kawo masa guragu, makafi, bebaye da nakasassun mutane da yawa, da wadansu marasa lafiya. Suka kawo su gaban Yesu, sai ya warkar da su.
31 so that the multitude wondered when they saw the mute speaking, the injured healed, the lame walking, and the blind seeing—and they glorified the God of Israel.
Don haka mutane da yawa suka yi mamaki a lokacin da suka ga bebaye suna magana, nakasassu sun warke, guragu suna tafiya, makafi suna gani. Sai suka daukaka Allah na Isra'ila.
32 Jesus summoned his disciples and said, “I have compassion on the multitude, because they have continued with me now three days and have nothing to eat. I do not want to send them away fasting, or they might faint on the way.”
Yesu ya kira almajiransa zuwa gun sa sai ya ce, “Ina jin tausayin taron, sun kasance tare da ni kwana uku ke nan kuma ba su da abin da za su ci. Bana so in sallame su ba tare da sun ci abinci ba, domin kada su suma a hanya.”
33 The disciples said to him, “Where could we get so many loaves in a deserted place as to satisfy so great a multitude?”
Almajiran suka ce masa, “A ina zamu sami isasshiyar gurasa a wannan wuri da babu kowa har ta ishi babban taron nan.”
34 Jesus said to them, “How many loaves do you have?” They said, “Seven, and a few small fish.”
Yesu ya ce masu, “Gurasa nawa ku ke da ita?” Suka ce, “Bakwai da 'yan kifi marasa yawa.”
35 He commanded the multitude to sit down on the ground;
Sai Yesu ya umarci taron su zauna a kasa.
36 and he took the seven loaves and the fish. He gave thanks and broke them, and gave to the disciples, and the disciples to the multitudes.
Ya dauki gurasar nan bakwai da kifin, bayan ya yi godiya, ya kakkarya gurasar ya bada ita ga almajiran Sai almajiran suka ba taron.
37 They all ate and were filled. They took up seven baskets full of the broken pieces that were left over.
Jama'a duka suka ci suka koshi. Suka tattara gutsattsarin abincin da ya rage, kwando bakwai cike.
38 Those who ate were four thousand men, in addition to women and children.
Wadanda suka ci su dubu hudu ne maza, banda mata da yara.
39 Then he sent away the multitudes, got into the boat, and came into the borders of Magdala.
Sai Yesu ya sallami taron ya shiga cikin jirgin ruwa ya tafi yankin Magadan.

< Matthew 15 >