< Leviticus 11 >

1 The LORD spoke to Moses and to Aaron, saying to them,
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
2 “Speak to the children of Israel, saying, ‘These are the living things which you may eat among all the animals that are on the earth.
“Ku ce wa Isra’ilawa, ‘Cikin dabbobin da suke a doron ƙasa, waɗannan ne za ku ci.
3 Whatever parts the hoof, and is cloven-footed, and chews the cud among the animals, that you may eat.
Za ku iya cin dabbobin da suke da rababben kofato, waɗanda suke kuma tuƙa.
4 “‘Nevertheless these you shall not eat of those that chew the cud, or of those who part the hoof: the camel, because it chews the cud but does not have a parted hoof, is unclean to you.
“‘Akwai waɗanda suke tuƙa ko kuwa suna da rababben kofato kawai, duk da haka ba za ku ci su ba. Waɗannan kuwa su ne, raƙumi, ko da yake yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato; saboda haka cin namansa haram ne gare ku.
5 The hyrax, because it chews the cud but does not have a parted hoof, is unclean to you.
Rema, ko da yake tana tuƙa, duk da haka ba ta da rababben kofato; saboda haka namanta haram ne gare ku.
6 The hare, because it chews the cud but does not have a parted hoof, is unclean to you.
Zomo, ko da yake yana tuƙa, duk da haka ba shi da rababben kofato; saboda haka namansa haram ne gare ku.
7 The pig, because it has a split hoof, and is cloven-footed, but does not chew the cud, is unclean to you.
Alade, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa, saboda haka namansa haram ne gare ku.
8 You shall not eat their meat. You shall not touch their carcasses. They are unclean to you.
Ba za ku ci namansu ba, ko ku taɓa gawawwakinsu, gama haram ne gare ku.
9 “‘You may eat of all these that are in the waters: whatever has fins and scales in the waters, in the seas, and in the rivers, that you may eat.
“‘Cikin dukan halittu masu rai da suke a cikin ruwan tekuna da rafuffuka, za ku iya cin kowane da yake da ƙege da kamɓori.
10 All that do not have fins and scales in the seas and rivers, all that move in the waters, and all the living creatures that are in the waters, they are an abomination to you,
Amma kowace halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, ko cikin dukan abubuwa masu rai a ruwa ko kuma sauran halittu a cikin ruwa za ku ɗauka su marasa tsaki ne gare ku.
11 and you shall detest them. You shall not eat of their meat, and you shall detest their carcasses.
Da yake abubuwan ƙyama ne a gare ku, ba za ku ci namansu ba, kuma dole ku yi ƙyamar gawawwakinsu.
12 Whatever has no fins nor scales in the waters is an abomination to you.
Duk abin da yake a ruwa amma ba shi da ƙege ko kamɓori, za ku yi ƙyamarsa.
13 “‘You shall detest these among the birds; they shall not be eaten because they are an abomination: the eagle, the vulture, the black vulture,
“‘Waɗannan su ne tsuntsayen da za ku yi ƙyamarsu, ba za ku ci su ba domin sun zama abin ƙyama. Tsuntsayen kuwa su ne, gaggafa, ungulu, baƙin ungulu,
14 the red kite, any kind of black kite,
shirwa, da duk wani irin baƙin shirwa,
15 any kind of raven,
kowane irin hankaka,
16 the horned owl, the screech owl, the gull, any kind of hawk,
mujiya mai ƙaho, jimina, shaho, da kowane irin shaho,
17 the little owl, the cormorant, the great owl,
ƙaramin ƙururu, babba da jaka, zalɓe,
18 the white owl, the desert owl, the osprey,
kazar ruwa, kwasakwasa, da ungulu,
19 the stork, any kind of heron, the hoopoe, and the bat.
shamuwa, kowane irin jinjimi, katutu da kuma jamage.
20 “‘All flying insects that walk on all fours are an abomination to you.
“‘Dukan ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu abin ƙyama ne gare ku.
21 Yet you may eat these: of all winged creeping things that go on all fours, which have long, jointed legs for hopping on the earth.
Sai dai akwai ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu da za ku ci; waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle.
22 Even of these you may eat: any kind of locust, any kind of katydid, any kind of cricket, and any kind of grasshopper.
Za ku iya cin kowane irin fāra, gyare, ƙwanso da danginsu.
23 But all winged creeping things which have four feet are an abomination to you.
Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, suna kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku.
24 “‘By these you will become unclean: whoever touches their carcass shall be unclean until the evening.
“‘Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har fāɗuwar rana.
25 Whoever carries any part of their carcass shall wash his clothes, and be unclean until the evening.
Duk wanda ya ɗauki ɗaya daga cikin gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har zuwa yamma.
26 “‘Every animal which has a split hoof that is not completely divided, or does not chew the cud, is unclean to you. Everyone who touches them shall be unclean.
“‘Kowace dabbar da ba ta da rababben kofato ko ba ta tuƙa, haram ce gare ku; duk wanda ya taɓa gawarsu zai ƙazantu.
27 Whatever goes on its paws, among all animals that go on all fours, they are unclean to you. Whoever touches their carcass shall be unclean until the evening.
Duk abin da yake tafiya a kan dāginsa cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa yamma.
28 He who carries their carcass shall wash his clothes, and be unclean until the evening. They are unclean to you.
Duk wanda ya ɗauki gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har yamma. Waɗannan dabbobi za su zama marasa tsabta a gare ku.
29 “‘These are they which are unclean to you among the creeping things that creep on the earth: the weasel, the rat, any kind of great lizard,
“‘Waɗannan ƙananan dabbobi da suke rarrafe a ƙasa, haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa,
30 the gecko, and the monitor lizard, the wall lizard, the skink, and the chameleon.
da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo.
31 These are they which are unclean to you among all that creep. Whoever touches them when they are dead shall be unclean until the evening.
Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma.
32 Anything they fall on when they are dead shall be unclean; whether it is any vessel of wood, or clothing, or skin, or sack, whatever vessel it is, with which any work is done, it must be put into water, and it shall be unclean until the evening. Then it will be clean.
Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai, zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma, sa’an nan zai tsarkaka.
33 Every earthen vessel into which any of them falls and all that is in it shall be unclean. You shall break it.
In waninsu ya fāɗi a cikin tukunyar laka, kome da yake a tukunyar zai ƙazantu, kuma dole a fashe tukunyar.
34 All food which may be eaten which is soaked in water shall be unclean. All drink that may be drunk in every such vessel shall be unclean.
Duk abincin da aka yarda a ci, wanda ya taɓa ruwa daga irin tukunyan nan zai zama marar tsabta, kuma duk ruwan da za a sha daga irin tukunyan nan ƙazantacce ne.
35 Everything whereupon part of their carcass falls shall be unclean; whether oven, or range for pots, it shall be broken in pieces. They are unclean, and shall be unclean to you.
Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai ya ƙazantu ke nan; ko a kan murhu, ko a tukunyar dahuwa, dole a farfashe su. Su haramtattu ne kuma dole ku ɗauke su haramtattu.
36 Nevertheless a spring or a cistern in which water is gathered shall be clean, but that which touches their carcass shall be unclean.
Maɓuɓɓuga ko tafki na tarin ruwa zai ci gaba da zauna mai tsabta, amma duk wanda ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan gawawwakin ya haramtu.
37 If part of their carcass falls on any sowing seed which is to be sown, it is clean.
In gawa ta fāɗi a irin da za a shuka, irin zai ci gaba da zama mai tsabta.
38 But if water is put on the seed, and part of their carcass falls on it, it is unclean to you.
Amma in an sa ruwa a irin sai kuma gawar ta fāɗi a kai, to, irin ya zama haram gare ku.
39 “‘If any animal of which you may eat dies, he who touches its carcass shall be unclean until the evening.
“‘In dabbar aka yarda a ci ta mutu, duk wanda ya taɓa gawarta zai ƙazantu har yamma.
40 He who eats of its carcass shall wash his clothes, and be unclean until the evening. He also who carries its carcass shall wash his clothes, and be unclean until the evening.
Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma.
41 “‘Every creeping thing that creeps on the earth is an abomination. It shall not be eaten.
“‘Duk dabba mai rarrafe a ƙasa abin ƙyama ne; ba kuwa za a ci shi ba.
42 Whatever goes on its belly, and whatever goes on all fours, or whatever has many feet, even all creeping things that creep on the earth, them you shall not eat; for they are an abomination.
Ba za ku ci wani halittar da take rarrafe a ƙasa, ko tana jan ciki, ko tana tafiya a kan ƙafafu huɗu, ko a kan ƙafafu da yawa ba; abin ƙyama ne.
43 You shall not make yourselves abominable with any creeping thing that creeps. You shall not make yourselves unclean with them, that you should be defiled by them.
Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani daga waɗannan halittu. Kada ku ƙazantar da kanku ta dalilinsu, ko a mai da ku haramtattu ta wurinsu.
44 For I am the LORD your God. Sanctify yourselves therefore, and be holy; for I am holy. You shall not defile yourselves with any kind of creeping thing that moves on the earth.
Ni ne Ubangiji Allahnku; ku tsarkake kanku ku kuma zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani halittar da take rarrafe a ƙasa.
45 For I am the LORD who brought you up out of the land of Egypt, to be your God. You shall therefore be holy, for I am holy.
Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku; saboda haka ku zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne.
46 “‘This is the law of the animal, and of the bird, and of every living creature that moves in the waters, and of every creature that creeps on the earth,
“‘Waɗannan ne ƙa’idodi game da dabbobi, tsuntsaye, da kowane abu mai rai da yake motsi a cikin ruwa, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa.
47 to make a distinction between the unclean and the clean, and between the living thing that may be eaten and the living thing that may not be eaten.’”
Dole ku bambanta tsakanin haramtacce da halaltacce, tsakanin halittu masu ran da za a iya ci da waɗanda ba za a iya ci ba.’”

< Leviticus 11 >