< Hebrews 3 >

1 Therefore, holy brothers, partakers of a heavenly calling, consider the Apostle and High Priest of our confession: Jesus,
Saboda haka,’yan’uwa tsarkaka, waɗanda suke da rabo a kiran nan na sama, ku kafa tunaninku a kan Yesu, manzo da kuma babban firist wanda muke shaidawa.
2 who was faithful to him who appointed him, as also Moses was in all his house.
Ya yi aminci ga wanda ya naɗa shi, kamar yadda Musa ya yi aminci ga dukan gidan Allah.
3 For he has been counted worthy of more glory than Moses, because he who built the house has more honor than the house.
An ga Yesu ya cancanci girma fiye da Musa, kamar yadda mai ginin gida ya fi gidan daraja.
4 For every house is built by someone; but he who built all things is God.
Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abu Allah ne.
5 Moses indeed was faithful in all his house as a servant, for a testimony of those things which were afterward to be spoken,
Musa ya yi aminci a matsayin bawa cikin dukan gidan Allah, yana ba da shaida a kan abubuwan da za a faɗa nan gaba.
6 but Christ is faithful as a Son over his house. We are his house, if we hold fast our confidence and the glorying of our hope firm to the end.
Amma Kiristi mai aminci ne kamar ɗa a gidan Allah. Mu kuwa gidansa ne, in muka tsaya gabanmu gadi da kuma begen da muke taƙama a kai.
7 Therefore, even as the Holy Spirit says, “Today if you will hear his voice,
Kamar dai yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Yau, in kuka ji muryarsa,
8 do not harden your hearts as in the rebellion, in the day of the trial in the wilderness,
kada ku taurare zukatanku, yadda kuka yi a tawayen nan, a lokacin gwaji a hamada,
9 where your fathers tested me and tried me, and saw my deeds for forty years.
inda kakanninku suka gwada ni, suka kuma gwada ni, ko da yake a cikin shekaru arba’in sun ga abin da na yi.
10 Therefore I was displeased with that generation, and said, ‘They always err in their heart, but they did not know my ways.’
Shi ya sa na yi fushi da wancan zamani, na kuma ce, ‘Kullum zukatansu a karkace suke, ba su kuma san hanyoyina ba.’
11 As I swore in my wrath, ‘They will not enter into my rest.’”
Saboda haka na yi rantsuwa a cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’”
12 Beware, brothers, lest perhaps there might be in any one of you an evil heart of unbelief, in falling away from the living God;
Ku lura fa,’yan’uwa, cewa kada waninku yă kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai.
13 but exhort one another day by day, so long as it is called “today”, lest any one of you be hardened by the deceitfulness of sin.
Sai dai ku ƙarfafa juna kullum, muddin akwai lokacin da ana ce da shi Yau, don kada waninku yă zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗun zunubi.
14 For we have become partakers of Christ, if we hold the beginning of our confidence firm to the end,
Mu masu tarayya ne da Kiristi idan mun riƙe bangaskiyarmu da ƙarfi daga farko har zuwa ƙarshe.
15 while it is said, “Today if you will hear his voice, do not harden your hearts, as in the rebellion.”
Kamar yadda aka faɗa cewa, “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a tawayen nan.”
16 For who, when they heard, rebelled? Was not it all those who came out of Egypt led by Moses?
Su wane ne suka ji suka kuma yi tawaye? Ba su ne duk waɗanda Musa ya bi da su daga Masar ba?
17 With whom was he displeased forty years? Was not it with those who sinned, whose bodies fell in the wilderness?
Da su wane ne kuwa ya yi fushi har shekaru arba’in? Ba da waɗanda suka yi zunubi, waɗanda suka mutu a hamada ba?
18 To whom did he swear that they would not enter into his rest, but to those who were disobedient?
Kuma ga su wane ne Allah ya rantse cewa ba za su taɓa shiga hutunsa ba, in ba ga marasa biyayyan nan ba?
19 We see that they were not able to enter in because of unbelief.
Saboda haka mun ga cewa ba su iya shiga ba, saboda rashin bangaskiyarsu ne.

< Hebrews 3 >