< Ezekiel 13 >

1 The LORD’s word came to me, saying,
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2 “Son of man, prophesy against the prophets of Israel who prophesy, and say to those who prophesy out of their own heart, ‘Hear the LORD’s word:
“Ɗan mutum, yi annabci a kan annabawan Isra’ila waɗanda suke annabci yanzu. Ka faɗa wa waɗanda suke annabci bisa ga ra’ayinsu cewa, ‘Ku ji maganar Ubangiji!
3 The Lord GOD says, “Woe to the foolish prophets, who follow their own spirit, and have seen nothing!
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake faɗa, Kaiton wawaye annabawan da suke bin ruhunsu kuma ba su ga kome ba!
4 Israel, your prophets have been like foxes in the waste places.
Annabawanki, ya Isra’ila, suna kama da diloli a kufai.
5 You have not gone up into the gaps or built up the wall for the house of Israel, to stand in the battle in the LORD’s day.
Ba ku haura don ku rushe katanga don ku gyara gidan Isra’ila saboda ya tsaya daram a yaƙi a ranar Ubangiji ba.
6 They have seen falsehood and lying divination, who say, ‘The LORD says;’ but the LORD has not sent them. They have made men to hope that the word would be confirmed.
Wahayoyinsu ƙarya ne suna yin dubansu na ƙarya ne. Sukan ce, Ubangiji ya furta, alhali kuwa Ubangiji bai aike su ba; duk da haka sukan sa zuciya ga cikawar maganarsu.
7 Have not you seen a false vision, and have not you spoken a lying divination, in that you say, ‘The LORD says;’ but I have not spoken?”
Ba ku ga wahayin ƙarya kuka kuma faɗa yin duban ƙarya sa’ad da kuka ce, “Ubangiji ya furta,” ko da yake bai yi magana ba?
8 “‘Therefore the Lord GOD says: “Because you have spoken falsehood and seen lies, therefore, behold, I am against you,” says the Lord GOD.
“‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa saboda maganganunku na ƙarya da wahayinku na ƙarya, ina gāba da ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
9 “My hand will be against the prophets who see false visions and who utter lying divinations. They will not be in the council of my people, neither will they be written in the writing of the house of Israel, neither will they enter into the land of Israel. Then you will know that I am the Lord GOD.”
Hannuna zai yi gāba da annabawan da suke ganin wahayin ƙarya suna kuma yin duban ƙarya. Ba za su kasance cikin taron mutanena ba, ba kuwa za a rubuta su a littafin gidan Isra’ila ba, ba za su shiga ƙasar Isra’ila ba. Ta haka za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.
10 “‘Because, even because they have seduced my people, saying, “Peace;” and there is no peace. When one builds up a wall, behold, they plaster it with whitewash.
“‘Domin sun ɓad da mutanena, suna cewa, “Salama,” sa’ad da ba salama, kuma saboda, sa’ad da ana gina katanga marar ƙarfi, sukan shafe ta da farar ƙasa,
11 Tell those who plaster it with whitewash that it will fall. There will be an overflowing shower; and you, great hailstones, will fall. A stormy wind will tear it.
saboda haka ka faɗa wa waɗanda suka shafe da farar ƙasa cewa za tă fāɗi. Ruwan sama zai sauko da rigyawa, zan kuma aika da ƙanƙara, kuma babbar iska za tă ɓarke.
12 Behold, when the wall has fallen, will not it be said to you, “Where is the plaster with which you have plastered it?”
Sa’ad da katangar ta fāɗi, mutane ba za su tambaye ku ba cewa, “Ina shafen farar ƙasar da kuka yi mata?”
13 “‘Therefore the Lord GOD says: “I will even tear it with a stormy wind in my wrath. There will be an overflowing shower in my anger, and great hailstones in wrath to consume it.
“‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a cikin hasalata zan saki babbar iska, kuma cikin fushina zan tura ƙanƙara kuma rigyawan ruwan sama zai sauko da fushin hallaka.
14 So I will break down the wall that you have plastered with whitewash, and bring it down to the ground, so that its foundation will be uncovered. It will fall, and you will be consumed in the middle of it. Then you will know that I am the LORD.
Zan rushe katangar da kuka shafe da farar ƙasa zan baje ta har ƙasa saboda tushenta zai tsaya tsirara. Sa’ad da ta fāɗi, za a hallaka ku a cikinta; kuma za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.
15 Thus I will accomplish my wrath on the wall, and on those who have plastered it with whitewash. I will tell you, ‘The wall is no more, nor those who plastered it—
Ta haka zan aukar wa katangar da hasalata da kuma a kan waɗanda suka yi shafenta da farar ƙasa. Zan ce muku, “Katangar ta fāɗi haka kuma mutanen da suka shafe ta da farar ƙasa,
16 to wit, the prophets of Israel who prophesy concerning Jerusalem, and who see visions of peace for her, and there is no peace,’” says the Lord GOD.’”
waɗannan annabawan Isra’ila waɗanda suka yi annabci wa Urushalima suka kuma ga mata wahayin salama sa’ad da ba salama, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”’
17 You, son of man, set your face against the daughters of your people, who prophesy out of their own heart; and prophesy against them,
“To, ɗan mutum, ka kafa idonka a kan’yan matan mutanenka waɗanda suke annabci bisa ga ra’ayinsu. Yi annabci a kansu
18 and say, “The Lord GOD says: ‘Woe to the women who sew magic bands on all elbows and make veils for the head of persons of every stature to hunt souls! Will you hunt the souls of my people and save souls alive for yourselves?
ka kuma ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kaiton matan da suke ɗinka kambuna a hannuwansu suna kuma yin gyale masu tsawo dabam-dabam wa kawunansu don su farauci mutane. Za ku farauci rayukan mutanena ku bar naku?
19 You have profaned me among my people for handfuls of barley and for pieces of bread, to kill the souls who should not die and to save the souls alive who should not live, by your lying to my people who listen to lies.’
Kun jawo mini kunya a cikin mutanena don a tafa muku sha’ir da ɗan dunƙulen burodi. Ta wurin yin ƙarya wa mutanena, waɗanda suke jin ƙarairayi, kuka kashe waɗanda bai kamata su mutu ba kuka bar waɗanda ya kamata su mutu.
20 “Therefore the Lord GOD says: ‘Behold, I am against your magic bands, with which you hunt the souls to make them fly, and I will tear them from your arms. I will let the souls fly free, even the souls whom you ensnare like birds.
“‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kambunanku waɗanda kuke farautar mutane da su kamar tsuntsaye don haka zan kuma tsintsinke su daga hannuwanku; zan’yantar da mutanen da kuka farauto kamar tsuntsaye.
21 I will also tear your veils and deliver my people out of your hand; and they will no longer be in your hand to be ensnared. Then you will know that I am the LORD.
Zan kyakketa gyalenku in ceci mutanena daga hannuwanku, ba za su kuma ƙara zama ganima a hannunku ba. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji
22 Because with lies you have grieved the heart of the righteous, whom I have not made sad; and strengthened the hands of the wicked, that he should not return from his wicked way, and be saved alive.
Domin kun karya zuciyar masu adalci da ƙarairayinku, sa’ad da na fitar da su babu damuwa, kuma domin kun ƙarfafa mugaye kada su juye daga mugayen hanyoyinsu su ceci rayukansu,
23 Therefore you shall no more see false visions nor practice divination. I will deliver my people out of your hand. Then you will know that I am the LORD.’”
saboda haka ba za ku ƙara ganin wahayin ƙarya ba, ko ku yi duba. Zan ceci mutanena daga hannuwanku. A sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’”

< Ezekiel 13 >