< 1 Samuel 12 >

1 Samuel said to all Israel, “Behold, I have listened to your voice in all that you said to me, and have made a king over you.
Sama’ila ya ce wa Isra’ilawa duka, “Na saurari abubuwan da kuka faɗa mini, na kuma naɗa muku sarki.
2 Now, behold, the king walks before you. I am old and gray-headed. Behold, my sons are with you. I have walked before you from my youth to this day.
Yanzu kuna da sarki a matsayin shugaba, ni kuwa na tsufa har da furfura, yarana maza kuma suna tare da ku. Na yi shugabancinku tun ina yaro.
3 Here I am. Witness against me before the LORD and before his anointed. Whose ox have I taken? Whose donkey have I taken? Whom have I defrauded? Whom have I oppressed? Of whose hand have I taken a bribe to make me blind my eyes? I will restore it to you.”
Ga ni a gabanku. Idan na yi wani abin da ba daidai ba sai ku faɗa a gaban Ubangiji, da gaban sarkin da ya keɓe. Ko na taɓa ƙwace saniya ko jakin wani? Ko na taɓa cuce wani, ko in danne hakkinsa? Ko na taɓa cin hanci daga hannun ɗayanku? Idan na taɓa yi ɗaya daga cikin waɗannan, sai ku faɗa mini, zan kuwa mayar masa.”
4 They said, “You have not defrauded us, nor oppressed us, neither have you taken anything from anyone’s hand.”
Suka ce, “Ba ka cuci ko danne hakkin kowa ba, ba ka ƙwace kome daga hannun kowa ba.”
5 He said to them, “The LORD is witness against you, and his anointed is witness today, that you have not found anything in my hand.” They said, “He is witness.”
Sama’ila ya ce musu, “Ubangiji yă zama shaida a kanku, shafaffensa kuma yă zama shaida a wannan rana cewa ba ku same ni da wani laifin kome ba.” Suka ce, “I, shi ne shaida.”
6 Samuel said to the people, “It is the LORD who appointed Moses and Aaron, and that brought your fathers up out of the land of Egypt.
Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutane, Ubangiji ne ya naɗa Musa da Haruna suka fitar da kakanninku daga Masar.
7 Now therefore stand still, that I may plead with you before the LORD concerning all the righteous acts of the LORD, which he did to you and to your fathers.
Yanzu ku tsaya nan zan yi fito-na-fito da ku da shaida a gaban Ubangiji kan dukan ayyuka masu alherin da Ubangiji ya aikata saboda ku da kakanninku.
8 “When Jacob had come into Egypt, and your fathers cried to the LORD, then the LORD sent Moses and Aaron, who brought your fathers out of Egypt, and made them to dwell in this place.
Bayan da Yaƙub da’ya’yansa suka shiga Masar suka yi kukan neman taimako daga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya aika musu da Musa da Haruna. Su ne suka kawo kakanni-kakanninku daga Masar suka zauna a nan.
9 But they forgot the LORD their God; and he sold them into the hand of Sisera, captain of the army of Hazor, and into the hand of the Philistines, and into the hand of the king of Moab; and they fought against them.
Amma suka manta da Ubangiji Allahnsu, shi kuma ya bashe su a hannun Sisera shugaban rundunar Hazor da kuma hannun Filistiyawa da sarkin Mowab wanda suka yi yaƙi da su.
10 They cried to the LORD, and said, ‘We have sinned, because we have forsaken the LORD and have served the Baals and the Ashtaroth; but now deliver us out of the hand of our enemies, and we will serve you.’
Suka yi kuka a gaban Ubangiji suka ce, “Mun yi zunubi mun bar Ubangiji, muka bauta wa Ba’al da Ashtarot. Amma ka cece mu yanzu daga hannun abokan gābanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”
11 The LORD sent Jerubbaal, Bedan, Jephthah, and Samuel, and delivered you out of the hand of your enemies on every side; and you lived in safety.
Sai Ubangiji ya aiki Yerub-Ba’al da Bedan da Yefta da Sama’ila, ya cece ku daga hannun abokan gābanku a kowane gefe domin ku sami cikakken zaman lafiya.
12 “When you saw that Nahash the king of the children of Ammon came against you, you said to me, ‘No, but a king shall reign over us,’ when the LORD your God was your king.
Amma da kuka ga Nahash sarkin Ammonawa yana matsowa yă yaƙe, sai kuka ce mini, “Sam, muna so sarki yă shugabance mu.” Ko da yake Ubangiji Allahnku ne yake mulkinku.
13 Now therefore see the king whom you have chosen and whom you have asked for. Behold, the LORD has set a king over you.
Yanzu ga sarkinku da kuka zaɓa wanda kuka nema, ga shi Ubangiji ya naɗa muku sarki.
14 If you will fear the LORD, and serve him, and listen to his voice, and not rebel against the commandment of the LORD, then both you and also the king who reigns over you are followers of the LORD your God.
In kuka ji tsoron Ubangiji, kuka bauta masa, kuka yi masa biyayya, ba ku kuwa ƙi bin umarninsa ba, in kuma ku da sarkin da yake mulkinku kun bi Ubangiji Allahnku, to, za ku zauna lafiya.
15 But if you will not listen to the LORD’s voice, but rebel against the commandment of the LORD, then the LORD’s hand will be against you, as it was against your fathers.
Amma in ba ku yi biyayya ga Ubangiji ba, in kuma kuka ƙi bin umarnansa, fushinsa zai zauna a kanku.
16 “Now therefore stand still and see this great thing, which the LORD will do before your eyes.
Yanzu ku tsaya tsit ku ga abin da Ubangiji ke dab da yi a gabanku.
17 Is not it wheat harvest today? I will call to the LORD, that he may send thunder and rain; and you will know and see that your wickedness is great, which you have done in the LORD’s sight, in asking for a king.”
Ba lokacin yankan alkama ke nan ba? Zan roƙi Ubangiji yă aiko da tsawa da ruwan sama, za ku kuwa gane wace irin mugunta kuka yi a gaban Ubangiji sa’ad da kuka roƙa a ba ku sarki.
18 So Samuel called to the LORD, and the LORD sent thunder and rain that day. Then all the people greatly feared the LORD and Samuel.
Sai Sama’ila ya roƙi Ubangiji, a ranar kuwa Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama. Dukan mutane suka ji tsoron Ubangiji da kuma Sama’ila.
19 All the people said to Samuel, “Pray for your servants to the LORD your God, that we not die; for we have added to all our sins this evil, to ask for a king.”
Dukan mutane suka ce wa Sama’ila, “Ka yi addu’a ga Ubangiji Allahnka saboda bayinka, domin kada mu mutu, gama mun ƙara wa kanmu zunubi da muka roƙa a yi mana sarki.”
20 Samuel said to the people, “Do not be afraid. You have indeed done all this evil; yet do not turn away from following the LORD, but serve the LORD with all your heart.
Sama’ila ya ce, “Kada ku ji tsoro.” Kun yi waɗannan mugunta duk da haka kada ku bar bin Ubangiji, amma ku bauta wa Ubangiji da dukan zuciyarku.
21 Do not turn away to go after vain things which cannot profit or deliver, for they are vain.
Kada ku bi alloli marasa amfani. Ba za su iya yi muku kome nagari ba, ba kuwa za su iya cece ku ba, gama ba su da amfani.
22 For the LORD will not forsake his people for his great name’s sake, because it has pleased the LORD to make you a people for himself.
Saboda suna mai girma da Ubangiji yake da shi, ba zai taɓa ƙin mutanensa ba. Gama Ubangiji ya ji daɗi da ya yi ku mutanensa.
23 Moreover, as for me, far be it from me that I should sin against the LORD in ceasing to pray for you; but I will instruct you in the good and the right way.
Ni kam ba zai taɓa yiwu in yi wa Ubangiji zunubi ta wurin ƙin yin addu’a dominku ba. Zan koya muku hanyar da tana da kyau da ta kuma cancanta.
24 Only fear the LORD, and serve him in truth with all your heart; for consider what great things he has done for you.
Amma ku amince za ku ji tsoron Ubangiji, ku bauta masa da aniya da dukan zuciyarku, kuna da manyan abubuwan da ya yi muku.
25 But if you keep doing evil, you will be consumed, both you and your king.”
Amma in kuka duƙufa cikin aikin mugunta da ku da sarkinku za a hallaka ku.

< 1 Samuel 12 >