< 1 John 3 >

1 See how great a love the Father has given to us, that we should be called children of God! For this cause the world does not know us, because it did not know him.
Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba.
2 Beloved, now we are children of God. It is not yet revealed what we will be; but we know that when he is revealed, we will be like him, for we will see him just as he is.
Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.
3 Everyone who has this hope set on him purifies himself, even as he is pure.
Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.
4 Everyone who sins also commits lawlessness. Sin is lawlessness.
Duk mai yin zunubi yana karya doka ne; tabbatacce, zunubi, karya doka ne.
5 You know that he was revealed to take away our sins, and no sin is in him.
Sai dai kun san cewa Kiristi ya bayyana ne domin yă ɗauke zunubanmu. A cikinsa kuwa babu zunubi.
6 Whoever remains in him does not sin. Whoever sins has not seen him and does not know him.
Ba mai rayuwa a cikinsa da yake cin gaba da yin zunubi. Kowa da yake aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba.
7 Little children, let no one lead you astray. He who does righteousness is righteous, even as he is righteous.
’Ya’yana ƙaunatattu, kada ku yarda wani yă ruɗe ku. Duk mai yin abin da yake daidai mai adalci ne, yadda Kiristi yake mai adalci.
8 He who sins is of the devil, for the devil has been sinning from the beginning. To this end the Son of God was revealed: that he might destroy the works of the devil.
Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yă rushe aikin Iblis.
9 Whoever is born of God does not commit sin, because his seed remains in him, and he cannot sin, because he is born of God.
Babu haifaffe na Allah da zai ci gaba da yin zunubi, domin iri na Allah yana a cikinsa; ba zai iya ci gaba da yin zunubi ba, domin haifaffe ne na Allah.
10 In this the children of God are revealed, and the children of the devil. Whoever does not do righteousness is not of God, neither is he who does not love his brother.
Ta haka muka san waɗanda suke’ya’yan Allah da kuma waɗanda suke’ya’yan Iblis. Duk wanda ba ya yin abin da yake daidai, ba ɗan Allah ba ne; haka ma wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa.
11 For this is the message which you heard from the beginning, that we should love one another—
Wannan shi ne saƙon da kuka ji tun farko. Ya kamata mu ƙaunaci juna.
12 unlike Cain, who was of the evil one and killed his brother. Why did he kill him? Because his deeds were evil, and his brother’s righteous.
Kada ku zama kamar Kayinu, wanda ya zama na mugun nan, ya kuma kashe ɗan’uwansa. Me ya sa ya kashe shi? Domin ayyukansa mugaye ne, na ɗan’uwansa kuma na adalci ne.
13 Do not be surprised, my brothers, if the world hates you.
Kada ku yi mamaki’yan’uwana, in duniya ta ƙi ku.
14 We know that we have passed out of death into life, because we love the brothers. He who does not love his brother remains in death.
Mun san cewa mun riga mun ratsa daga mutuwa zuwa rai, domin muna ƙaunar’yan’uwanmu. Duk wanda ba ya ƙauna matacce ne har yanzu.
15 Whoever hates his brother is a murderer, and you know that no murderer has consummate (aiōnios g166) life remaining in him.
Duk mai ƙin ɗan’uwansa mai kisankai ne, kun kuma san cewa ba mai kisankan da yake da rai madawwami a cikinsa. (aiōnios g166)
16 By this we know love, because he laid down his life for us. And we ought to lay down our lives for the brothers.
Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin’yan’uwanmu.
17 But whoever has the world’s goods and sees his brother in need, then closes his heart of compassion against him, how does God’s love remain in him?
In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa?
18 My little children, let’s not love in word only, or with the tongue only, but in deed and truth.
’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.
19 And by this we know that we are of the truth and persuade our hearts before him,
Ta haka muka san cewa mu na gaskiya ne, kuma za mu iya tsaya a gaban Allah ba tare da rawar jiki ba.
20 because if our heart condemns us, God is greater than our heart, and knows all things.
Idan zuciyarmu ta nuna mana muna da laifi, mun san cewa Allah ya fi zuciyarmu, ya kuma san dukan kome.
21 Beloved, if our hearts do not condemn us, we have boldness toward God;
Abokaina ƙaunatattu, in zukatanmu ba su ba mu laifi ba, muna da ƙarfin halin tsayawa a gaban Allah ke nan.
22 so whatever we ask, we receive from him, because we keep his commandments and do the things that are pleasing in his sight.
Muna kuma samun dukan abin da muka roƙa daga gare shi, domin muna biyayya da umarnansa, muna kuma yin abin da ya gamshe shi.
23 This is his commandment, that we should believe in the name of his Son, Jesus Christ, and love one another, even as he commanded.
Umarninsa kuwa shi ne, mu gaskata da sunan Ɗansa, Yesu Kiristi, mu kuma ƙaunaci juna kamar yadda ya umarce mu.
24 He who keeps his commandments remains in him, and he in him. By this we know that he remains in us, by the Spirit which he gave us.
Waɗanda suke biyayya da umarnansa kuwa suna rayuwa a cikinsa, shi kuma a cikinsu. Ta haka muka san cewa yana raye a cikinmu. Mun san haka ta wurin Ruhun da ya ba mu.

< 1 John 3 >