< 1 Corinthians 14 >

1 Follow after love and earnestly desire spiritual gifts, but especially that you may prophesy.
Ku bi halin ƙauna kuna kuma marmarin neman baye-bayen ruhaniya, musamman baiwar annabci.
2 For he who speaks in another language speaks not to men, but to God, for no one understands, but in the Spirit he speaks mysteries.
Gama duk wanda yake magana da wani harshe ba da mutane yake magana ba, sai dai da Allah. Tabbatacce, ba wanda yake fahimtarsa; yana faɗin asirai ta wurin ruhu ne.
3 But he who prophesies speaks to men for their edification, exhortation, and consolation.
Amma duk wanda yake annabci, yana magana ne da mutane domin yă gina su, yă ƙarfafa su, yă kuma yi musu ta’aziyya.
4 He who speaks in another language edifies himself, but he who prophesies edifies the assembly.
Wanda yake magana da wani harshe kuwa, kansa yake gina, amma mai annabci, ikkilisiya ce yake gina.
5 Now I desire to have you all speak with other languages, but even more that you would prophesy. For he is greater who prophesies than he who speaks with other languages, unless he interprets, that the assembly may be built up.
Zan so kowannenku yă yi magana da harsuna, sai dai zan fi so ku yi annabci. Wanda yake annabci ya fi wanda yake magana da harsuna, sai dai in ya fassara don ikkilisiya ta ginu.
6 But now, brothers, if I come to you speaking with other languages, what would I profit you unless I speak to you either by way of revelation, or of knowledge, or of prophesying, or of teaching?
To,’yan’uwa, a ce na zo wurinku ina kuma yin magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani ko sani ko annabci, ko kuma kalmar koyarwa ba?
7 Even lifeless things that make a sound, whether pipe or harp, if they did not give a distinction in the sounds, how would it be known what is piped or harped?
Abubuwan nan marasa rai ma da sukan yi ƙara, kamar su algaita ko molo, in muryarsu ba tă fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa?
8 For if the trumpet gave an uncertain sound, who would prepare himself for war?
Haka ma in ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi?
9 So also you, unless you uttered by the tongue words easy to understand, how would it be known what is spoken? For you would be speaking into the air.
Haka yake sa’ad da kuka yi magana da waɗansu harsunan da ba a fahimta. In babu wanda zai san abin da kuke faɗi, za ka dai yi wa iska magana ne kawai.
10 There are, it may be, so many kinds of languages in the world, and none of them is without meaning.
Ba shakka akwai harsuna iri-iri a duniya, duk da haka kowane a cikinsu yana da ma’ana.
11 If then I do not know the meaning of the language, I would be to him who speaks a foreigner, and he who speaks would be a foreigner to me.
To, in ban gane ma’anar abin da wani yake faɗi ba, ni baƙo ne ga mai maganar, shi kuma baƙo ne a gare ni.
12 So also you, since you are zealous for spiritual gifts, seek that you may abound to the building up of the assembly.
Haka yake a gare ku. Da yake kuna marmarin samun baye-bayen ruhaniya, sai ku ba da ƙarfinku ga yin amfani da waɗanda za su gina ikkilisiya.
13 Therefore let him who speaks in another language pray that he may interpret.
Saboda haka, duk wanda yake magana da harshe, sai yă yi addu’a a yi masa baiwar fassara.
14 For if I pray in another language, my spirit prays, but my understanding is unfruitful.
Gama in na yi addu’a da wani harshe, ruhuna ne yake addu’a, amma tunanina bai amfana kome ba.
15 What should I do? I will pray with the spirit, and I will pray with the understanding also. I will sing with the spirit, and I will sing with the understanding also.
To, me zan yi? Akwai lokutan da zan yi addu’a da ruhuna; akwai kuma lokutan da zan yi addu’a da hankalina. Wani lokaci ya kamata in yi waƙa da ruhuna, a wani lokacin kuma in yi waƙa da hankalina.
16 Otherwise, if you bless with the spirit, how will he who fills the place of the unlearned say the “Amen” at your giving of thanks, seeing he does not know what you say?
A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, sa’ad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba?
17 For you most certainly give thanks well, but the other person is not built up.
Ko da yake kuna ba da godiya da kyau, amma wancan mutumin da yake tare da ku bai ginu ba.
18 I thank my God, I speak with other languages more than you all.
Na gode wa Allah, domin ina magana da harsuna fiye da ku duka.
19 However, in the assembly I would rather speak five words with my understanding, that I might instruct others also, than ten thousand words in another language.
Amma a cikin ikkilisiya zan gwammace in yi magana da kalmomi biyar da za a fahimta don in koyar da waɗansu da a ce in yi magana da kalmomi guda dubu goma a wani harshe.
20 Brothers, do not be children in thoughts, yet in malice be babies, but in thoughts be mature.
’Yan’uwa, ku daina tunani kamar yara. Wajen mugunta ku zama jarirai, sai dai wajen tunaninku, ku zama manya.
21 In the law it is written, “By men of strange languages and by the lips of strangers I will speak to this people. They will not even listen to me that way, says the Lord.”
A cikin Doka yana a rubuce cewa, “Ta wurin mutane masu baƙin harsuna da kuma ta leɓunan baƙi zan yi magana da waɗannan mutane, amma duk da haka, ba za su saurare ni ba,” in ji Ubangiji.
22 Therefore other languages are for a sign, not to those who believe, but to the unbelieving; but prophesying is for a sign, not to the unbelieving, but to those who believe.
Harsuna fa alama ce ba ga masu bi ba, sai dai ga marasa bi. Annabci kuwa ga masu bi ne ba ga marasa bi ba.
23 If therefore the whole assembly is assembled together and all speak with other languages, and unlearned or unbelieving people come in, will not they say that you are crazy?
Saboda haka, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da waɗansu harsuna, sai waɗansu jahilai ko waɗansu marasa bi suka shigo, ashe, ba za su ce kuna hauka ba?
24 But if all prophesy, and someone unbelieving or unlearned comes in, he is reproved by all, and he is judged by all.
Amma in wani marar bi, ko jahili ya shigo sa’ad da kowa yana annabci, sai maganar kowa ta ratsa shi, za su shawo kansa yă gane cewa shi mai zunubi ne saboda abin da kowa yake faɗi,
25 And thus the secrets of his heart are revealed. So he will fall down on his face and worship God, declaring that God is among you indeed.
asirin zuciyarsa kuma su bayyana a fili. Don haka, zai fāɗi a ƙasa yă yi wa Allah sujada yana cewa, “Lalle, Allah yana cikinku!”
26 What is it then, brothers? When you come together, each one of you has a psalm, has a teaching, has a revelation, has another language, or has an interpretation. Let all things be done to build each other up.
Me za mu ce ke nan’yan’uwa? Sa’ad da kuka taru, wani yakan yi waƙa, wani koyarwa, wani wahayi, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Dole ne a yi duka don gina ikkilisiya.
27 If any man speaks in another language, let there be two, or at the most three, and in turn; and let one interpret.
In kuwa waɗansu za su yi magana a wani harshe, to, kada su fi mutum biyu ko uku, kuma a yi bi da bi, wani kuma yă fassara.
28 But if there is no interpreter, let him keep silent in the assembly, and let him speak to himself and to God.
In babu mai fassara, sai mai magana yă yi shiru a cikin ikkilisiya, yă yi wa kansa magana da kuma Allah.
29 Let two or three of the prophets speak, and let the others discern.
Annabawa biyu ko uku za su iya yin magana, sauran kuma sai su auna a hankali abin da aka faɗa.
30 But if a revelation is made to another sitting by, let the first keep silent.
In kuma wahayi ya zo wa wani da yake zaune, sai mai magana na farko yă yi shiru.
31 For you all can prophesy one by one, that all may learn and all may be exhorted.
Dukanku kuna iya yin annabci bi da bi, domin kowa yă sami koyarwa da ƙarfafawa.
32 The spirits of the prophets are subject to the prophets,
Ruhohin annabawa kuwa suna ƙarƙashin sarrafawar annabawa.
33 for God is not a God of confusion but of peace, as in all the assemblies of the saints.
Gama Allah, ba Allah mai sa rikicewa ba ne, sai dai mai salama. Kamar yadda yake a dukan ikkilisiyoyi na tsarkaka.
34 Let the wives be quiet in the assemblies, for it has not been permitted for them to be talking except in submission, as the law also says,
Ya kamata mata su zauna shiru a cikin ikkilisiyoyi. Ba su da izinin yin magana, sai dai su yi biyayya yadda Doka ta faɗi.
35 if they desire to learn anything. “Let them ask their own husbands at home, for it is shameful for a wife to be talking in the assembly.”
In suna so su yi tambaya game da wani abu, ya kamata su tambayi mazansu a gida, domin abin kunya ne mace tă yi magana a cikin ikkilisiya.
36 What!? Was it from you that the word of God went out? Or did it come to you alone?
Shin, a kanku ne maganar Allah ta fara? Ko kuma a gare ku ne kaɗai ta iso?
37 If any man thinks himself to be a prophet or spiritual, let him recognize the things which I write to you, that they are the commandment of the Lord.
In wani yana tsammani shi annabi ne, ko yana da baiwar ruhaniya, bari yă gane cewa abin da nake rubuta muku umarnin Ubangiji ne.
38 But if anyone is ignorant, let him be ignorant.
In ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi.
39 Therefore, brothers, desire earnestly to prophesy, and do not forbid speaking with other languages.
Saboda haka’yan’uwana, ku yi marmarin yin annabci, kada kuma ku hana magana da harsuna.
40 Let all things be done decently and in order.
Sai dai a yi kome daidai da kuma cikin tsari.

< 1 Corinthians 14 >