< 诗篇 47 >

1 可拉后裔的诗,交与伶长。 万民哪,你们都要拍掌! 要用夸胜的声音向 神呼喊!
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki.
2 因为耶和华至高者是可畏的; 他是治理全地的大君王。
Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya!
3 他叫万民服在我们以下, 又叫列邦服在我们脚下。
Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu.
4 他为我们选择产业, 就是他所爱之雅各的荣耀。 (细拉)
Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. (Sela)
5 神上升,有喊声相送; 耶和华上升,有角声相送。
Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni.
6 你们要向 神歌颂,歌颂! 向我们王歌颂,歌颂!
Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai.
7 因为 神是全地的王; 你们要用悟性歌颂。
Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi.
8 神作王治理万国; 神坐在他的圣宝座上。
Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki.
9 列邦的君王聚集要作亚伯拉罕之 神的民。 因为世界的盾牌是属 神的; 他为至高!
Manyan mutanen al’ummai sun taru a matsayin mutanen Allah na Ibrahim, gama sarkunan duniya na Allah ne; ana ɗaukaka shi ƙwarai.

< 诗篇 47 >