< 尼希米记 11 >

1 百姓的首领住在耶路撒冷。其余的百姓掣签,每十人中使一人来住在圣城耶路撒冷,那九人住在别的城邑。
To, fa, shugabannin mutane suka zauna a Urushalima, sauran mutanen kuma suka jefa ƙuri’a don su kawo mutum ɗaya daga kowane mutum goma don su zauna a Urushalima, birni mai tsarki, yayinda sauran tara suka zauna a garuruwansu.
2 凡甘心乐意住在耶路撒冷的,百姓都为他们祝福。
Sai mutane suka yaba wa dukan mutanen da suka ba da kansu da yardar rai su zauna a Urushalima.
3 以色列人、祭司、利未人、尼提宁,和所罗门仆人的后裔都住在犹大城邑,各在自己的地业中。本省的首领住在耶路撒冷的记在下面:
Waɗannan su ne shugabannin yankuna waɗanda suka zauna a Urushalima (ko da yake waɗansu Isra’ilawa, da firistoci, da Lawiyawa, da ma’aikatan haikali, da zuriyar bayin Solomon, suka yi zama a cikin garuruwan Yahuda, kowanne a mallakarsa cikin garuruwa dabam-dabam,
4 其中有些犹大人和便雅悯人。犹大人中有法勒斯的子孙、乌西雅的儿子亚他雅。乌西雅是撒迦利雅的儿子;撒迦利雅是亚玛利雅的儿子;亚玛利雅是示法提雅的儿子;示法提雅是玛勒列的儿子。
yayinda sauran mutane daga Yahuda da Benyamin suka zauna a Urushalima). Daga zuriyar Yahuda akwai, Atahiya ɗan Uzziya, ɗan Zakariya, ɗan Amariya, ɗan Shefatiya, ɗan Mahalalel, wani zuriyar Ferez;
5 又有巴录的儿子玛西雅。巴录是谷何西的儿子;谷何西是哈赛雅的儿子;哈赛雅是亚大雅的儿子;亚大雅是约雅立的儿子;约雅立是撒迦利雅的儿子;撒迦利雅是示罗尼的儿子。
da Ma’asehiya ɗan Baruk, ɗan Kol-Hoze, ɗan Hazahiya, ɗan Adahiya, ɗan Yohiyarib, ɗan Zakariya, zuriyar Shela.
6 住在耶路撒冷、法勒斯的子孙共四百六十八名,都是勇士。
Zuriyar Ferez waɗanda suka zauna a Urushalima sun kai ɗari huɗu da sittin da takwas, dukansu kuwa muhimman mutane ne.
7 便雅悯人中有米书兰的儿子撒路。米书兰是约叶的儿子;约叶是毗大雅的儿子;毗大雅是哥赖雅的儿子;哥赖雅是玛西雅的儿子;玛西雅是以铁的儿子;以铁是耶筛亚的儿子。
Daga zuriyar Benyamin akwai, Sallu ɗan Meshullam, ɗan Yowed, ɗan Fedahiya, ɗan Kolahiya, ɗan Ma’asehiya, ɗan Itiyel, ɗan Yeshahiya,
8 其次有迦拜、撒来的子孙,共九百二十八名。
da mabiyansa, Gabbai da Sallai, mutum 928.
9 细基利的儿子约珥是他们的长官。哈西努亚的儿子犹大是耶路撒冷的副官。
Yowel ɗan Zikri ne babban shugabansu, Yahuda kuma ɗan Hassenuwa, ya shugabanci Yanki na Biyu na birni.
10 祭司中有雅斤,又有约雅立的儿子耶大雅;
Daga firistoci akwai, Yedahiya ɗan Yohiyarib, da Yakin,
11 还有管理 神殿的西莱雅。西莱雅是希勒家的儿子;希勒家是米书兰的儿子;米书兰是撒督的儿子;撒督是米拉约的儿子;米拉约是亚希突的儿子。
da Serahiya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, mai lura da abubuwa a cikin gidan Allah,
12 还有他们的弟兄在殿里供职的,共八百二十二名;又有耶罗罕的儿子亚大雅。耶罗罕是毗拉利的儿子;毗拉利是暗洗的儿子;暗洗是撒迦利亚的儿子;撒迦利亚是巴施户珥的儿子;巴施户珥是玛基雅的儿子。
tare da’yan’uwansu waɗanda suke aiki domin haikali, su 822 ne. Akwai kuma Adahiya ɗan Yeroham, ɗan Felaliya, ɗan Amzi, ɗan Zakariya, ɗan Fashhur, ɗan Malkiya,
13 还有他的弟兄作族长的,二百四十二名;又有亚萨列的儿子亚玛帅。亚萨列是亚哈赛的儿子;亚哈赛是米实利末的儿子;米实利末是音麦的儿子。
da’yan’uwansa waɗanda suke shugabannin iyalai, su 242. Sai kuma Amashsai ɗan Azarel, ɗan Ahzai, ɗan Meshillemot, ɗan Immer,
14 还有他们弟兄、大能的勇士共一百二十八名。哈基多琳的儿子撒巴第业是他们的长官。
da’yan’uwansa, su 128 ne muhimman mutane. Babban shugabansu shi ne Zabdiyel ɗan Haggedolim.
15 利未人中有哈述的儿子示玛雅。哈述是押利甘的儿子;押利甘是哈沙比雅的儿子;哈沙比雅是布尼的儿子。
Daga Lawiyawa kuwa akwai, Shemahiya ɗan Hasshub, ɗan Azrikam, ɗan Hashabiya, ɗan Bunni,
16 又有利未人的族长沙比太和约撒拔管理 神殿的外事。
da Shabbetai, da kuma Yozabad, biyu cikin shugabanni Lawiyawa waɗanda suke da nawayar aiki waje da gidan Allah.
17 祈祷的时候,为称谢领首的是米迦的儿子玛他尼。米迦是撒底的儿子;撒底是亚萨的儿子;又有玛他尼弟兄中的八布迦为副。还有沙母亚的儿子押大。沙母亚是加拉的儿子;加拉是耶杜顿的儿子。
Sai kuma Mattaniya ɗan Mika, ɗan Zabdi, ɗan Asaf, shugaban da yake bi da hidimar godiya da kuma addu’a. Sai Bakbukiya, na biyu a cikin’yan’uwansa; da Abda ɗan Shammuwa, ɗan Galal, ɗan Yedutun.
18 在圣城的利未人共二百八十四名。
Lawiyawan da suke cikin birni mai tsarki sun kai 284.
19 守门的是亚谷和达们,并守门的弟兄,共一百七十二名。
Matsaran ƙofofi kuwa su ne, Akkub, da Talmon, da’yan’uwansu waɗanda suke tsaron ƙofofi, su 172 ne.
20 其余的以色列人、祭司、利未人都住在犹大的一切城邑,各在自己的地业中。
Sauran Isra’ilawa tare da firistoci, da Lawiyawa sun kasance a dukan garuruwan Yahuda, kowanne a mallakar kakansa.
21 尼提宁却住在俄斐勒;西哈和基斯帕管理他们。
Ma’aikatan haikali sun zauna a kan tudun Ofel. Ziha, da Gishfa ne suke lura da su.
22 在耶路撒冷、利未人的长官,管理 神殿事务的是歌唱者亚萨的子孙、巴尼的儿子乌西。巴尼是哈沙比雅的儿子;哈沙比雅是玛他尼的儿子;玛他尼是米迦的儿子。
Babban shugaban Lawiyawa a Urushalima shi ne Uzzi ɗan Bani, ɗan Hashabiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mika. Uzzi yana ɗaya daga zuriyar Asaf, waɗanda suke mawaƙan da suke da nawayar hidima a gidan Allah.
23 王为歌唱的出命令,每日供给他们必有一定之粮。
Mawaƙa sun bi umarnan sarki, a kan abin da za su yi kowace rana.
24 犹大儿子谢拉的子孙、米示萨别的儿子毗他希雅辅助王办理犹大民的事。
Fetahahiya ɗan Meshezabel, ɗaya daga zuriyar Zera ɗan Yahuda ne, wakilin sarki cikin dukan al’amuran da suka shafi mutane.
25 至于村庄和属村庄的田地,有犹大人住在基列·亚巴和属基列·亚巴的乡村;底本和属底本的乡村;叶甲薛和属叶甲薛的村庄;
Game da ƙauyukan da filayensu, waɗansu mutanen Yahuda suka zauna a Kiriyat Arba da ƙauyukanta, da Dibon da ƙauyukanta, da Yekabzeyel da ƙauyukanta.
26 耶书亚、摩拉大、伯·帕列、
Akwai su kuma a Yeshuwa, da Molada, da Bet-Felet,
27 哈萨·书亚、别是巴,和属别是巴的乡村;
da Hazar Shuwal, da Beyersheba da ƙauyukanta.
28 洗革拉、米哥拿,和属米哥拿的乡村;
Akwai su a Ziklag, da Mekona da ƙauyukanta.
29 音·临门、琐拉、耶末、
Suna nan kuma a En Rimmon, da Zora, da Yarmut,
30 撒挪亚、亚杜兰,和属这两处的村庄;拉吉和属拉吉的田地;亚西加和属亚西加的乡村。他们所住的地方是从别是巴直到欣嫩谷。
da Zanowa, da Adullam da ƙauyukansu, da Lakish da gonakinta, da kuma Azeka da ƙauyukanta. Saboda haka sun yi zama tun daga Beyersheba har zuwa Kwarin Hinnom.
31 便雅悯人从迦巴起,住在密抹、亚雅、伯特利和属伯特利的乡村。
Zuriyar mutanen Benyamin daga Geba sun zauna a Mikmash, da Aiya, da Betel da ƙauyukanta,
32 亚拿突、挪伯、亚难雅、
da Anatot, da Nob, da Ananiya,
33 夏琐、拉玛、基他音、
da Hazor, da Rama, da Gittayim,
34 哈叠、洗编、尼八拉、
da Hadid, da Zeboyim, da Neballat,
35 罗德、阿挪、匠人之谷。
da Lod, da Ono, da kuma a Kwarin Masu sana’a.
36 利未人中有几班曾住在犹大地归于便雅悯的。
Waɗansu gundumomin Lawiyawan Yahuda sun zauna a Benyamin.

< 尼希米记 11 >