< 以赛亚书 38 >

1 那时希西家病得要死,亚摩斯的儿子先知以赛亚去见他,对他说:“耶和华如此说:你当留遗命与你的家,因为你必死不能活了。”
A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da ciwo ya kuma kusa ya mutu. Annabi Ishaya ɗan Amoz ya tafi wurinsa ya kuma ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce ka shirya gidanka, domin za ka mutu; ba za ka warke ba.”
2 希西家就转脸朝墙,祷告耶和华说:
Hezekiya ya juye fuskarsa wajen bango ya kuma yi addu’a ga Ubangiji,
3 “耶和华啊,求你记念我在你面前怎样存完全的心,按诚实行事,又做你眼中所看为善的。”希西家就痛哭了。
“Ka tuna, ya Ubangiji, yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da dukan zuciya na kuma yi abin da yake nagari a idanunka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi.
4 耶和华的话临到以赛亚说:
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Ishaya cewa,
5 “你去告诉希西家说,耶和华—你祖大卫的 神如此说:我听见了你的祷告,看见了你的眼泪。我必加增你十五年的寿数;
“Ka tafi ka faɗa wa Hezekiya, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, ya ce na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan ƙara maka shekaru goma sha biyar ga rayuwarka.
6 并且我要救你和这城脱离亚述王的手,也要保护这城。
Zan kuwa cece ka da wannan birni daga hannun sarkin Assuriya. Zan kiyaye wannan birni.
7 “我—耶和华必成就我所说的。我先给你一个兆头,
“‘Ga alamar Ubangiji gare ka cewa Ubangiji zai aikata kamar yadda ya yi alkawari.
8 就是叫亚哈斯的日晷,向前进的日影往后退十度。”于是,前进的日影果然在日晷上往后退了十度。
Zan sa inuwar da rana ta yi a kan matakalar Ahaz ta koma baya da taki goma.’” Saboda haka inuwar ta koma da baya daga fuskar rana har taki goma.
9 犹大王希西家患病已经痊愈,就作诗说:
Rubutun Hezekiya sarkin Yahuda bayan ciwonsa da kuma warkarwarsa.
10 我说:正在我中年之日 必进入阴间的门; 我余剩的年岁不得享受。 (Sheol h7585)
Na ce, “Cikin tsakiyar rayuwata dole in bi ta ƙofofin mutuwa a kuma raba ni da sauran shekaruna?” (Sheol h7585)
11 我说:我必不得见耶和华, 就是在活人之地不见耶和华; 我与世上的居民不再见面。
Na ce, “Ba zan ƙara ganin Ubangiji ba, Ubangiji a ƙasa ta masu rai; ba zan ƙara ga wani mutum, ko in kasance tare da waɗanda suke zama a wannan duniya ba.
12 我的住处被迁去离开我, 好像牧人的帐棚一样; 我将性命卷起, 像织布的卷布一样。 耶和华必将我从机头剪断, 从早到晚,他要使我完结。
Kamar tentin makiyayi an rushe gidana aka kuma ƙwace ta daga gare ni. Kamar mai saƙa, na nannaɗe rayuwata, ya kuma yanke ni daga sandar saƙa; dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.
13 我使自己安静直到天亮; 他像狮子折断我一切的骨头, 从早到晚,他要使我完结。
Na yi jira da haƙuri har safiya, amma kamar zaki ya kakkarya ƙasusuwana duka; dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.
14 我像燕子呢喃, 像白鹤鸣叫, 又像鸽子哀鸣; 我因仰观,眼睛困倦。 耶和华啊,我受欺压, 求你为我作保。
Na yi kuka kamar mashirare ko zalɓe, na yi kuka kamar kurciya mai makoki. Idanuna suka rasa ƙarfi yayinda na duba sammai. Na damu; Ya Ubangiji, ka taimake ni!”
15 我可说什么呢? 他应许我的,也给我成就了。 我因心里的苦楚, 在一生的年日必悄悄而行。
Amma me zan ce? Ya riga ya yi mini magana, shi kansa ne kuma ya aikata. Zan yi tafiya da tawali’u dukan kwanakina saboda wahalar raina.
16 主啊,人得存活乃在乎此。 我灵存活也全在此。 所以求你使我痊愈,仍然存活。
Ubangiji, ta waɗannan abubuwa ne mutane suke rayuwa; ruhuna kuma yana samun rai a cikinsu shi ma. Ka maido mini da lafiya ka kuma sa na rayu.
17 看哪,我受大苦,本为使我得平安; 你因爱我的灵魂便救我脱离败坏的坑, 因为你将我一切的罪扔在你的背后。
Tabbatacce wannan kuwa saboda ribata ne cewa in sha irin wahalan nan. Cikin ƙaunarka ka kiyaye ni daga ramin hallaka; ka sa dukan zunubaina a bayanka.
18 原来,阴间不能称谢你, 死亡不能颂扬你; 下坑的人不能盼望你的诚实。 (Sheol h7585)
Gama kabari ba zai yabe ka ba, matattu ba za su rera yabonka ba; waɗanda suka gangara zuwa rami ba za su sa zuciya ga amincinka ba. (Sheol h7585)
19 只有活人,活人必称谢你, 像我今日称谢你一样。 为父的,必使儿女知道你的诚实。
Masu rai, masu rai, su suke yabonka, kamar yadda nake yi a yau; iyaye za su faɗa wa’ya’yansu game da amincinka.
20 耶和华肯救我, 所以,我们要一生一世 在耶和华殿中 用丝弦的乐器唱我的诗歌。
Ubangiji zai cece ni, za mu kuma rera da kayan kiɗi masu tsirkiya dukan kwanakinmu a cikin haikalin Ubangiji.
21 以赛亚说:“当取一块无花果饼来,贴在疮上,王必痊愈。”
Ishaya ya riga ya ce, “Ku shirya curin da aka yi da’ya’yan ɓaure ku kuma shafa a marurun, zai kuwa warke.”
22 希西家问说:“我能上耶和华的殿,有什么兆头呢?”
Hezekiya ya riga ya yi tambaya ya ce, “Me zai zama alama ta cewa zan haura zuwa haikalin Ubangiji?”

< 以赛亚书 38 >