< 以西结书 23 >

1 耶和华的话又临到我说:
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2 “人子啊,有两个女子,是一母所生,
“Ɗan mutum, an yi mata biyu,’yan matan mahaifiya guda.
3 她们在埃及行邪淫,在幼年时行邪淫。她们在那里作处女的时候,有人拥抱她们的怀,抚摸她们的乳。
Suka zama karuwai a Masar, suka yi karuwanci tun daga ƙuruciyarsu. A wancan ƙasar an rungumi mamansu da ƙirjinsu na budurwanci.
4 她们的名字,姊姊名叫阿荷拉,妹妹名叫阿荷利巴。她们都归于我,生了儿女。论到她们的名字,阿荷拉就是撒马利亚,阿荷利巴就是耶路撒冷。
Sunan babbar Ohola, ƙanuwarta kuwa Oholiba. Sun zama nawa suka kuma haifi’ya’ya maza da mata. Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima.
5 “阿荷拉归我之后行邪淫,贪恋所爱的人,就是她的邻邦亚述人。
“Ohola ta shiga karuwanci yayinda take zamana; ta kuwa yi ta kai da kawowa da kwartayenta, Assuriyawa, mayaƙa
6 这些人都穿蓝衣,作省长、副省长,都骑着马,是可爱的少年人。
waɗanda suke saye da shunayya, gwamnoni da manyan sojoji, dukansu samari ne masu bansha’awa, suna bisa kan dawakai.
7 阿荷拉就与亚述人中最美的男子放纵淫行,她因所恋爱之人的一切偶像,玷污自己。
Ta ba da kanta ga duk waɗanda suke masu ilimin Assuriya ta kuma ƙazantar da kanta da dukan gumaka na kowa da take kai da kawowa a cikinsu.
8 自从在埃及的时候,她就没有离开淫乱,因为她年幼作处女的时候,埃及人与她行淫,抚摸她的乳,纵欲与她行淫。
Ba ta bar karuwancin da ta fara a Masar ba, sa’ad da take budurwa maza sun kwana da ita, suka rungumi ƙirjinta suka kuma biya kwaɗayinsu a kanta.
9 因此,我将她交在她所爱的人手中,就是她所恋爱的亚述人手中。
“Saboda haka na bashe ta ga kwartayenta, Assuriyawa, waɗanda ta yi ta kai da kawowa a cikinsu.
10 他们就露了她的下体,掳掠她的儿女,用刀杀了她,使她在妇女中留下臭名,因他们向她施行审判。
Suka tuɓe ta tsirara, suka kwashe’ya’yanta maza da mata suka kuma kashe ta da takobi. Ta kuwa zama abin karin magana a cikin mata, aka kuma yi mata hukunci.
11 “她妹妹阿荷利巴虽然看见了,却还贪恋,比她姊姊更丑;行淫乱比她姊姊更多。
“Ƙanuwarta Oholiba kuwa ta ga wannan, duk da haka cikin kai da kawowarta da karuwancinta ta fi’yar’uwar lalacewa.
12 她贪恋邻邦的亚述人,就是穿极华美的衣服,骑着马的省长、副省长,都是可爱的少年人。
Ita ma ta yi ta kai da kawowa cikin Assuriyawa, gwamnoni da manyan sojoji; mayaƙa masu saye da kayan yaƙi, suna bisa dawakai, dukansu samari ne masu bansha’awa.
13 我看见她被玷污了,她姊妹二人同行一路。
Na ga cewa ita ma ta ƙazantar da kanta; dukansu biyu sun bi hanya guda.
14 阿荷利巴又加增淫行,因她看见人像画在墙上,就是用丹色所画迦勒底人的像,
“Amma karuwancinta ya zarce. Ta ga an zāna mutane a kan bango, siffofin sojojin Kaldiyawa suna cikin jajjayen riguna,
15 腰间系着带子,头上有下垂的裹头巾,都是军长的形状,仿照巴比伦人的形象;他们的故土就是迦勒底。
da ɗamara a gindinsu da rawuna a kansu suna kaɗawa falfal; dukansu sun yi kamar jarumawan kekunan yaƙin Babiloniyawa’yan Kaldiya.
16 阿荷利巴一看见就贪恋他们,打发使者往迦勒底去见他们。
Nan da nan da ta gan su, sai ta yi sha’awarsu ta aika da’yan aika zuwa wurinsu a Kaldiya.
17 巴比伦人就来登她爱情的床,与她行淫玷污她。她被玷污,随后心里与他们生疏。
Sai Babiloniyawan suka zo wurinta, zuwa gadon soyayya, cikin kai da kawowarsu suka ƙazantar da ita. Bayan sun ƙazantar da ita, sai ta ji ƙyamarsu, ta rabu da su.
18 这样,她显露淫行,又显露下体;我心就与她生疏,像先前与她姊姊生疏一样。
Sa’ad da ta ci gaba da yin karuwancinta a fili ta kuma nuna tsiraicinta, sai na ji ƙyamarta, na rabu da ita, kamar dai yadda na rabu da’yar’uwarta.
19 她还加增她的淫行,追念她幼年在埃及地行邪淫的日子,
Duk da haka sai ta yi ta ƙara fasikanci tana tuna da kwanakin budurcinta, sa’ad da take karuwa a Masar.
20 贪恋情人身壮精足,如驴如马。
A can ta yi ta kai da kawowa da kwartayenta, waɗanda al’auransu kamar na jakuna ne waɗanda maniyyinsu kuwa kamar na dawakai ne.
21 这样,你就想起你幼年的淫行。那时,埃及人拥抱你的怀,抚摸你的乳。”
Haka kika yi ta lalacin budurcinki, sa’ad da a Masar aka rungumi ƙirjinta aka tattaɓa nononta.
22 阿荷利巴啊,主耶和华如此说:“我必激动你先爱而后生疏的人来攻击你。我必使他们来,在你四围攻击你。
“Saboda haka, Oholiba, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan zuga kwartayenki su yi gāba da ke, su waɗanda kika ji ƙyamarsu, zan kuma kawo su su yi gāba da ke daga kowane gefe,
23 所来的就是巴比伦人、迦勒底的众人、比割人、书亚人、哥亚人,同着他们的还有亚述众人,乃是作省长、副省长、作军长有名声的,都骑着马,是可爱的少年人。
Babiloniyawa da dukan Kaldiyawa, mutanen Fekod da Showa da Kowa, da dukan Assuriyawa, samari masu bansha’awa, dukan gwamnoni da manyan sojoji, hafsoshin keken yaƙin da mutane masu manyan matsayi, dukansu a bisa dawakai.
24 他们必带兵器、战车、辎重车,率领大众来攻击你。他们要拿大小盾牌,顶盔摆阵,在你四围攻击你。我要将审判的事交给他们,他们必按着自己的条例审判你。
Za su yi gāba da ke da kayan yaƙi, kekunan yaƙi da kekunan doki da mutane masu yawa; za su ja dāgā a kanki a kowane gefe da garkuwoyi manya da ƙanana da kuma hulunan kwano. Zan miƙa ke gare su don hukunci, za su kuma hukunta ki bisa ga shari’arsu.
25 我必以忌恨攻击你;他们必以忿怒办你。他们必割去你的鼻子和耳朵;你遗留的人必倒在刀下。他们必掳去你的儿女;你所遗留的必被火焚烧。
Zan nuna fushin kishina a kanki, za su kuwa wulaƙanta ki da fushi. Za su yanke hancinki da kunnuwanki, waɗanda suka rage miki kuma za a kashe su da takobi. Za su kama’ya’yanki maza da mata, waɗanda suka rage miki kuwa za a ƙone su da wuta.
26 他们必剥去你的衣服,夺取你华美的宝器。
Za su tuɓe tufafinki su kuma kwashe kayan adonki masu kyau.
27 这样,我必使你的淫行和你从埃及地染来的淫乱止息了,使你不再仰望亚述,也不再追念埃及。
Ta haka zan tsai da marmari da kuma karuwancin da kika fara a Masar. Ba za ki dubi waɗannan abubuwa da marmari ko ki ƙara tuna da Masar ba.
28 主耶和华如此说:我必将你交在你所恨恶的人手中,就是你心与他生疏的人手中。
“Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina shirin miƙa ki ga waɗanda suke ƙinki, ga waɗanda kika ji ƙyamarsu kika rabu da su.
29 他们必以恨恶办你,夺取你一切劳碌得来的,留下你赤身露体。你淫乱的下体,连你的淫行,带你的淫乱,都被显露。
Za su hukunta ki da ƙiyayya su kuma kwashe kome da kika yi wahalarsa. Za su bar ki tsirara tik, kunyan karuwancinki kuma zai tonu. Marmarinki da fasikancinki
30 人必向你行这些事;因为你随从外邦人行邪淫,被他们的偶像玷污了。
sun jawo miki wannan, domin ki yi ta kai da kawowa cikin ƙasashe kina ƙazantar da kanki da gumakansu.
31 你走了你姊姊所走的路,所以我必将她的杯交在你手中。”
Kin bi hanyar’yar’uwarki; saboda haka zan sa kwaf nata a hannunki.
32 主耶和华如此说: 你必喝你姊姊所喝的杯; 那杯又深又广,盛得甚多, 使你被人嗤笑讥刺。
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Za ki sha kwaf na’yar’uwarki, kwaf wanda yake da girma da kuma zurfi; zai jawo dariya da kuma reni gama yana ɗauke da abubuwa da yawa.
33 你必酩酊大醉,满有愁苦, 喝干你姊姊撒马利亚的杯, 就是令人惊骇凄凉的杯。
Za ki cika da buguwa da baƙin ciki, kwaf lalaci da kaɗaici, kwaf na’yar’uwarki Samariya.
34 你必喝这杯,以致喝尽。 杯破又啃杯片, 撕裂自己的乳; 因为这事我曾说过。 这是主耶和华说的。
Za ki sha shi ki kuma lashe shi ƙaf; za ki buga shi da ƙasa ya yi rugu-rugu ki tsattsage nononki. Ni Ubangiji Mai Iko Duka na faɗa.
35 主耶和华如此说:“因你忘记我,将我丢在背后,所以你要担当你淫行和淫乱的报应。”
“Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa da yake kin manta da ni kika tura ni bayanki, dole ki sha sakamakon marmarinki da karuwancinki.”
36 耶和华又对我说:“人子啊,你要审问阿荷拉与阿荷利巴吗?当指出她们所行可憎的事。
Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, za ka shari’anta Ohola da Oholiba? To, sai ka kalubalance su da ayyukansu masu banƙyama,
37 她们行淫,手中有杀人的血,又与偶像行淫,并使她们为我所生的儿女经火烧给偶像。
gama sun yi zina kuma jinin yana a hannuwansu. Sun yi zina da gumakansu; har suka miƙa’ya’yansu da suka haifa mini, su zama musu abinci.
38 此外,她们还有向我所行的,就是同日玷污我的圣所,干犯我的安息日。
Sun kuma yi mini wannan. A lokaci guda sun ƙazantar da wuri mai tsarkina suka ɓata Asabbataina.
39 她们杀了儿女献与偶像,当天又入我的圣所,将圣所亵渎了。她们在我殿中所行的乃是如此。
A ranar da suka miƙa’ya’yansu ga gumakansu, sai suka shiga wuri mai tsarkina suka kuma ƙazantar da shi. Abin da suka yi a gidana ke nan.
40 “况且你们二妇打发使者去请远方人。使者到他们那里,他们就来了。你们为他们沐浴己身,粉饰眼目,佩戴妆饰,
“Sun ma aiki manzanni wa mutanen da suka zo daga nesa, kuma da suka iso kun yi wanka dominsu, kuka yi shafe-shafen idanunku, kuka kuma sa kayan adonku.
41 坐在华美的床上,前面摆设桌案,将我的香料膏油摆在其上。
Kuka zauna a gado mai daraja, da tebur a shirye a gabanku wanda kun ajiye turare da maina.
42 在那里有群众安逸欢乐的声音,并有粗俗的人和酒徒从旷野同来,把镯子戴在二妇的手上,把华冠戴在她们的头上。
“Surutun taron mutane marasa kula suna kewaye da ita; aka kawo Sabenawa daga hamada tare da mutane daga mashaya, suka sa mundaye a hannuwan macen da kuma’yar’uwarta suka kuma sa rawani masu kyau a kawunansu.
43 “我论这行淫衰老的妇人说:现在人还要与她行淫,她也要与人行淫。
Sai na yi magana a kan wadda ta ƙare ƙarfi ta wurin karuwanci na ce, ‘Yanzu bari su yi amfani da ita kamar karuwa, gama abin da take ke nan.’
44 人与阿荷拉,并阿荷利巴二淫妇苟合,好像与妓女苟合。
Suka kuwa kwana da ita. Kamar yadda maza suke kwana ta karuwa, haka suka kwana da waɗannan lalatattun mata, Ohola da Oholiba.
45 必有义人,照审判淫妇和流人血的妇人之例,审判她们;因为她们是淫妇,手中有杀人的血。”
Amma masu adalci za su hukunta su irin da akan yi wa matan da suka yi zina suka kuma yi kisa, domin su mazinata ne kuma jini yana a hannuwansu.
46 主耶和华如此说:“我必使多人来攻击她们,使她们抛来抛去,被人抢夺。
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kawo taron mutane a kansu a kuma miƙa su don a firgitar da su a kuma washe su.
47 这些人必用石头打死她们,用刀剑杀害她们,又杀戮她们的儿女,用火焚烧她们的房屋。
Taron mutanen za su jajjefe su, su kuma sassare su da takuba; za su kashe’ya’yansu maza da mata su kuma ƙone gidajensu.
48 这样,我必使淫行从境内止息,好叫一切妇人都受警戒,不效法你们的淫行。
“Ta haka zan kawo ƙarshe ga lalaci a ƙasar, don dukan mata su ji gargaɗi kada kuma su kwaikwaye ku
49 人必照着你们的淫行报应你们;你们要担当拜偶像的罪,就知道我是主耶和华。”
Za ku sha hukuncin lalacinku ku kuma ɗauki hakkin zunuban bautar gumaka. Sa’an nan za ku san cewa Ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.”

< 以西结书 23 >