< 列王纪下 1 >

1 亚哈死后,摩押背叛以色列。
Bayan mutuwar Ahab, Mowab ta yi wa Isra’ila tawaye.
2 亚哈谢在撒马利亚,一日从楼上的栏杆里掉下来,就病了;于是差遣使者说:“你们去问以革伦的神巴力·西卜,我这病能好不能好。”
Ahaziya fa ya fāɗo daga tagar ɗakin samansa a Samariya ya ji rauni. Saboda haka ya aiki masinjoji, yana cewa, “Ku je ku tuntuɓi Ba’al-Zebub, allahn Ekron, ku ga ko zan warke daga wannan rauni.”
3 但耶和华的使者对提斯比人以利亚说:“你起来,去迎着撒马利亚王的使者,对他们说:‘你们去问以革伦神巴力·西卜,岂因以色列中没有 神吗?’
Amma mala’ikan Ubangiji ya ce wa Iliya mutumin Tishbe, “Ka haura ka taryi masinjojin sarkin Samariya, ka tambaye su, ‘Don babu Allah ne a Isra’ila da za ku tafi ku tuntuɓi Ba’al-Zebub allahn Ekron?’
4 所以耶和华如此说:‘你必不下你所上的床,必定要死!’”以利亚就去了。
Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ba za ka tashi daga inda kake kwance ba, ba shakka za ka mutu!’” Iliya ya yi kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, sai ya tafi.
5 使者回来见王,王问他们说:“你们为什么回来呢?”
Da masinjojin suka koma wurin sarki, sai sarki ya ce da su, “Don me kuka komo?”
6 使者回答说:“有一个人迎着我们来,对我们说:‘你们回去见差你们来的王,对他说:耶和华如此说,你差人去问以革伦神巴力·西卜,岂因以色列中没有 神吗?所以你必不下所上的床,必定要死。’”
Sai suka amsa, “Wani mutum ya sadu da mu ya ce mana, ‘Ku koma wurin sarkin da ya aike ku, ku ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, don babu Allah ne a Isra’ila da ka aika a tuntuɓi Ba’al-Zebub allahn Ekron? Saboda haka ba za ka tashi daga gadon da kake kwance ba. Ba shakka za ka mutu!”’”
7 王问他们说:“迎着你们来告诉你们这话的,是怎样的人?”
Sai Sarkin ya tambaye su ya ce, “Wanda irin mutum ne ya yi muku wannan magana?”
8 回答说:“他身穿毛衣,腰束皮带。”王说:“这必是提斯比人以利亚。”
Sai suka ce, “Mutumin ya sa riga mai gashi, ya kuma yi ɗamara da fata.” Sarkin ya ce, “Ai, Iliya mutumin Tishbe nan ne.”
9 于是,王差遣五十夫长,带领五十人去见以利亚,他就上到以利亚那里;以利亚正坐在山顶上。五十夫长对他说:“神人哪,王吩咐你下来!”
Sai sarki ya aiki kaftin da sojojin hamsin wurin Iliya. Kaftin ya haura wajen Iliya, wanda yake zaune a kan tudu, ya ce masa, “Mutumin Allah, sarki ya ce, ‘Ka sauko, ka zo!’”
10 以利亚回答说:“我若是神人,愿火从天上降下来,烧灭你和你那五十人!”于是有火从天上降下来,烧灭五十夫长和他那五十人。
Iliya ya ce masa, “In ni mutumin Allah ne, bari wuta tă sauko daga sama tă cinye ka da sojojinka hamsin!” Sai wuta ta sauko daga sama ta cinye kaftin tare da sojojinsa hamsin.
11 王第二次差遣一个五十夫长,带领五十人去见以利亚。五十夫长对以利亚说:“神人哪,王吩咐你快快下来!”
Da jin haka sai sarki ya sāke aiken wani kaftin tare da waɗansu sojojinsa hamsin wurin Iliya. Kaftin ya ce wa Iliya, “Mutumin Allah, ga abin da sarki ya ce, ‘Ka sauko, nan take ka zo!’”
12 以利亚回答说:“我若是神人,愿火从天上降下来,烧灭你和你那五十人!”于是 神的火从天上降下来,烧灭五十夫长和他那五十人。
Sai Iliya ya amsa, “In ni mutumin Allah ne, bari wuta ta sauko daga sama ta cinye ka da sojojinka hamsin!” Sai wutar Allah ta sauko daga sama ta cinye shi da sojojinsa hamsin.
13 王第三次差遣一个五十夫长,带领五十人去。这五十夫长上去,双膝跪在以利亚面前,哀求他说:“神人哪,愿我的性命和你这五十个仆人的性命在你眼前看为宝贵!
Saboda haka sai sarki ya aiki kaftin na uku da sojojinsa hamsin. Wannan kaftin na ukun ya haura ya durƙusa a gaban Iliya, ya roƙe shi ya ce, “Mutumin Allah, ina roƙonka ka dubi darajar raina da na waɗannan sojoji hamsin, bayinka!
14 已经有火从天上降下来,烧灭前两次来的五十夫长和他们各自带的五十人;现在愿我的性命在你眼前看为宝贵!”
Duba, wuta ta sauko daga sama ta cinye su kaftin nan biyu waɗanda suka zo da farko da dukan sojojinsu. To, yanzu dai, ka daraja raina!”
15 耶和华的使者对以利亚说:“你同着他下去,不要怕他!”以利亚就起来,同着他下去见王,
Sai mala’ikan Ubangiji ya ce wa Iliya, “Sauka, ka tafi tare da shi; kada ka ji tsoro.” Saboda haka Iliya ya tashi ya sauko, ya tafi tare da shi wajen sarki.
16 对王说:“耶和华如此说:‘你差人去问以革伦神巴力·西卜,岂因以色列中没有 神可以求问吗?所以你必不下所上的床,必定要死!’”
Iliya ya ce wa sarki, “Ga abin da Ubangiji ya ce, don babu Allah a Isra’ila ne wanda za ka tuntuɓa da ka aika a tuntuɓi Ba’al-Zebub, allahn Ekron? Domin ka yi haka, ba za ka tashi daga gadon da kake kwance ba, ba shakka za ka mutu!”
17 亚哈谢果然死了,正如耶和华借以利亚所说的话。因他没有儿子,他兄弟约兰接续他作王,正在犹大王约沙法的儿子约兰第二年。
Ya kuwa mutu yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya. Da yake Ahaziya ba shi da ɗa, sai Yoram ya gāje shi, ya zama sarki a shekara ta biyu ta mulkin Yehoram, ɗan Yehoshafat, sarkin Yahuda.
18 亚哈谢其余所行的事都写在以色列诸王记上。
Game da dukan sauran abubuwan da suka faru a zamani Ahaziya, da abin da ya yi, ba a rubuce suke a littattafan tarihin sarakuna Isra’ila ba?

< 列王纪下 1 >