< 路加福音 10 >

1 这之后,主又另外指派了七十名门徒,派他们两人一组先行一步,去往他计划造访的所有城邦。
Bayan wadannan abubuwa, Ubangiji ya sake nada wadansu saba'in ya aike su biyu biyu, domin su tafi kowanne birni da wurin da yake niyyan zuwa.
2 耶稣对他们说:“需要收割的庄稼很多,但工人太少,这时候就要向收获之主祈祷,让他派工人去他的农田收割庄稼。
Ya ce da su, “Girbin yana da yawa, amma ma'aikatan sun yi kadan. Saboda haka kuyi addu'a sosai ga Ubangijin girbin, domin ya aiko da ma'aikata cikin gonarsa.
3 所以去吧,我派你们出去,就像羊羔走进狼群。
Ku tafi, duba na aike ku kamar 'yan raguna cikin kyarkyetai.
4 不要带钱袋、口袋和鞋,遇见其他人也不要闲聊。
Kada ku dauki jakan kudi, ko jakar matafiyi, ko takalma, kada ku gai da kowa a kan hanya.
5 无论走进哪一栋房子,先说:‘愿平安降临这里!’
Dukan gidan da ku ka shiga, ku fara cewa, 'Bari salama ta kasance a wannan gida.'
6 那里若有平安之人,你们的平安就会降临于他们,否则,这平安仍为你们所有。
Idan akwai mutum mai salama a gidan, salamar ku za ta kasance a kansa, amma idan babu, salamar ku za ta dawo wurinku.
7 你们要住在那人的家中,他们给你吃喝,因为工人就应该获得报酬,不必在各家之间搬来搬去。
Ku zauna a wannan gidan, ku ci ku sha abin da suka tanada maku. Gama ma'aikaci ya wajibci ladansa. Kada ku bi gida gida.
8 无论你走进哪座城中,那里的人若欢迎你们,他们送上什么食物就吃什么。
Dukan birnin da ku ka shiga kuma sun karbe ku, ku ci abin da suka sa a gabanku.
9 然后医治城中的病人,告诉他们:‘上帝之国已经降临。’
Ku warkar da marasa lafiyar da ke wurin. Ku ce da su, 'Mulkin Allah ya zo kusa da ku.'
10 但无论你们进入哪座城,那里的人若不接待你们,就穿街过巷地告诉他们:
Amma dukan birnin da ku ka shiga, idan ba su karbe ku ba, ku tafi cikin titunansu, ku ce,
11 ‘我们会把这城里沾在我们脚上的尘土拂去,以此表达对你们的失望。但你们应该意识到:上帝之国已经降临。’
'Ko kurar birninku da ta like a kafafunmu, mun karkabe maku ita a matsayin shaida a kanku! Amma ku sani mulkin Allah ya zo kusa da ku.'
12 我告诉你们,到了审判日那天,索多玛甚至都要比这座城更好。
Na gaya maku, a ranar shari'a Saduma za ta fi wannan birni samun sauki.
13 哥拉逊啊,你有祸了!伯赛大啊,你有祸了!因为在你们那里显化的神迹,如果换做是在推罗和西顿,城里的人早就披上粗布衣,坐在地上悔改了。
Kaiton ki, Korasinu! Kaiton ki, Baitsaida! Ayyuka masu girma da aka yi a cikinku, da an yi su a cikin Taya da Sidon, da sun tuba tuntuni a zaune cikin toka da tufafin makoki.
14 所以到了审判日那天,你们所受的苦,要比推罗和西顿还重。
Amma a ranar shari'a Taya da Sidon za su fi ku samun sauki.
15 还有你,迦百农!你不会被高举到天堂,而是会坠入阴府。 (Hadēs g86)
Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani har zuwa sama za a daukaka ki? Babu, za a gangarar dake har zuwa hadas. (Hadēs g86)
16 听从你们的人就是听从于我,拒绝你们的人就是拒绝我。但拒绝我,就是拒绝那派我来此之人。”
Wanda ya saurare ku ya saurare ni, wanda ya ki ku, ya ki ni, kuma wanda ya ki ni, ya ki wanda ya aiko ni.”
17 那七十名门徒回来的时候兴奋地说:“主啊,因你之名,即使是魔鬼也听从我们!”
Su saba'in din suka dawo da murna, suna cewa, “Ubangiji, har ma aljanu suna yi mana biyayya, a cikin sunanka.”
18 耶稣说:“我看见撒旦像闪电一样从天空坠落。
Sai Yesu ya ce masu, “Na ga Shaidan yana fadowa daga sama kamar walkiya.
19 是的,我给了你们力量去毁灭蛇和蝎子,去战胜所有实力强大的仇敌。没有什么能伤害你们了。
Duba, na ba ku iko ku taka macizai da kunamai, da kuma kan dukan ikon magabci, kuma ba zai iya yin illa a gareku ba ko kadan.
20 但不要因鬼怪听从你们就欢喜。你们欢喜,应该是因为你们的名字被记录在天堂。”
Amma duk da haka kada ku yi murna a kan wannan kadai cewa ruhohi suna yi maku biyayya, amma ku yi murna domin an rubuta sunayenku a cikin sama.”
21 就在这时,耶稣心中充满圣灵的喜悦。他说:“父啊,天地之主,我感谢你,因为你在智慧和聪明人面前隐藏起这一切,却将其显现给孩童。父啊,是的,这样做会让你感到欢喜。
Cikin wannan lokacin, ya yi farin ciki kwarai cikin Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na ba ka girma, ya Uba, Ubangijin sama da kasa. Domin ka rufe wadannan abubuwa daga masu hikima da ganewa, ka bayyana su ga wadanda ba koyayyu ba ne, kamar kananan yara. I, Uba gama haka ne ya gamshe ka.”
22 我父已经把一切交给我,除了我父没有人能理解人子。除了人子以及人子愿意向其显示之人,没有人能理解我父。”
Dukan abu, Ubana ya damka su gare ni, kuma babu wanda ya san Dan, sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Dan. Sai kuma wanda Dan ya yi niyyar ya bayyana Uban a gareshi.”
23 当周围没有其他人时,耶稣转过身来对门徒说:“那些能见你们所见之人,真的是有福了!
Ya juya wajen almajiran, ya ce da su a kadaice, “Masu albarka ne su wadanda suka ga abin da kuke gani.
24 我告诉你们,曾有许多先知和君王,想看到你们所见的一切,却无法看到,想听你们所听的一切,却无法听到。”
Na fada maku, annabawa da yawa, da sarakuna da yawa sun so da sun ga abubuwan da kuke gani, amma ba su gani ba. Kuma sun so da sun ji abubuwan da kuke ji, amma ba su ji su ba.”
25 曾有一个研究法律的专家站起来,试图用问题为难耶稣。他说:“老师,我要怎么做才可以获得永生呢?” (aiōnios g166)
Sai ga wani malamin shari'ar Yahudawa, ya zo ya gwada shi da cewa, “Malam, me zan yi domin in gaji rai na har abada?” (aiōnios g166)
26 耶稣问他:“律法上是怎么写的?你看到了什么?”
Sai Yesu ya ce masa, “Yaya kake karanta abin da aka rubuta cikin shari'a?”
27 那人回答:“你要全心、全性、全力、全意爱你的主上帝,要爱邻居如爱自己。”
Ya amsa ya ce,”Dole ne ka kaunaci Ubangiji Allah da dukan zuciyarka, da dukan ranka da dukan karfinka, da dukan lamirinka. Ka kuma kaunaci makwabcinka kamar kanka.”
28 耶稣说:“你说对了。这样做就会获得永生。”
Yesu ya ce ma sa, “Ka amsa daidai, idan ka yi haka za ka rayu.”
29 但那人还想为自己的想法辩护,就问耶稣:“那么谁是我的邻居呢?”
Amma, malamin ya na so ya 'yantar da kansa, sai ya ce da Yesu, “To, wanene makwabcina?”
30 耶稣回答:“一个人从耶路撒冷去往耶利哥,途中遇到强盗,他们剥去他的衣服,殴打他,然后把他丢在那里,让他等死。
Ya amsa ya ce, “Wani mutum yana tafiya daga Urushalima za shi Yariko. Sai ya fada hannun mafasa, suka tube shi, suka kwace dukan abin da ya ke da shi, suka yi masa duka, suka bar shi kamar matacce.
31 正好有一名祭司走过那条路,但看见他后,却绕道走开了。
Ya zama sai ga wani firist ya na bin wannan hanya, da ya gan shi sai ya bi ta gefe daya ya wuce.
32 有一个利未人也路过,但走到这里看到这个男人,也绕道走开了。
Haka kuma sai ga wani Balawi, sa'adda ya zo wurin, ya gan shi sai ya bi ta wani gefe ya wuce shi.
33 最后一个撒玛利亚人走来路过此地,看见这个男人,心生怜悯。
Amma wani Basamariye, ya na tafiya sa'adda ya zo wurin da mutumin yake, sa'adda ya ga mutumin sai tausayi ya kama shi.
34 于是走上前,用油和酒处理他的伤口,将他包扎好,扶上自己的驴子,带他住进一个客店,照顾他。
Ya zo inda mutumin yake, ya daure masa raunukan da aka ji masa, yana shafa masu mai da ruwan inabi. Ya dora shi a kan dabbarsa ya kawo shi wurin kwana, ya kula da shi
35 第二天,这个撒玛利亚人拿出两个银币交给店主,说:‘请你照顾他,如果有额外的花销,等我回来的时候会还给你。’
Washegari ya kawo dinari biyu, ya ba mai wurin kwanan ya ce 'Ka kula da shi, idan ma ka kashe fiye da haka, idan na dawo zan biya ka.'
36 那么你认为,对于这个被强盗抢劫的人而言,这三个人中谁是他的邻居呢?”
A cikinsu ukun nan, wanene kake tsammani makwabcin wannan mutum da ya fada hannun 'yan fashi?”
37 研究法律的专家说:“就是那个表达善意的人。” 耶稣说:“那就去做同样的事情吧。”
Sai malamin ya ce, “Wannan da ya nuna masa jinkai” Sai Yesu yace masa, “Ka je kai ma ka yi haka.”
38 耶稣和众人继续赶路,走进一个村庄。有一个名叫马大的女人,请耶稣到自己家里。
Sa'adda suke tafiya, sai ya shiga cikin wani kauye, sai wata mata mai suna Marta ta marabce shi a gidanta.
39 她有一个妹妹名叫玛利亚,坐在主的面前听道。
Tana da 'yar'uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a kafafun Ubangiji tana jin abin da yake fadi.
40 马大当时忙着准备饭菜,有很多需要做的事情,感到有些不快。于是就上前来说:“主人,我妹妹让我一个人做这些事情,请让她来帮帮我。”
Amma ita Marta ta na ta kokari ta shirya abinci. Sai ta zo wurin Yesu ta ce, “Ubangiji, ba ka damu ba 'yar'uwata ta bar ni ina ta yin aiki ni kadai? Ka ce da ita ta taya ni.”
41 主回答她:“马大啊,马大,你为所有这些事操心忙碌,
Amma Ubangiji ya amsa ya ce da ita, “Marta, Marta, kin damu a kan abubuwa da yawa,
42 但只有一件事是必做的,玛利亚选择了正确之事,这不能从她那里剥夺。”
amma abu daya ne ya zama dole. Maryamu ta zabi abu mafi kyau, wanda ba za a iya kwace mata ba.”

< 路加福音 10 >