< Uruyan Yuhana 20 >

1 Inyene gono kadura Kutelle ntolo unuze kitene kani, amiin imon mpunu kuu kune kuchan hom sa ligang anin miin nyan nachara me. (Abyssos g12)
Na kuma ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da mabuɗin Abis yana kuma riƙe da ƙaton sarƙa a hannunsa. (Abyssos g12)
2 A kifo kumunche, fiyii fikuse, ule na idin yichi ngne ugo kinuu-shaitan, itere ngne udu akus limui.
Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu.
3 Ato ngne nya kuu ku chanchom kun sali ligang, na ayacha ngne ata likari ku. Bar a wa rusuzu anit sei akus limui nkata, nkata na ne iba da sun ngne nya kubi baat. (Abyssos g12)
Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci. (Abyssos g12)
4 Nya nane nyene atet-atet, iyacha ale na inani likaran sun sharaa, nkuru nyene tilai na le na imolsu anin bara lisan Yisa nin ligbulan Kutelle. Ale na inari uzazinu nchilme nin kuyelime, ale na inaru useru kulap me nitin mine sa na chara mine. ikpillai fita, iso nin Yisa udu akus limui.
Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.
5 Kagisin na nan kulle wa fita ba uduru ligang na kus limui Ulele unnare uchizinun fitu.
(Sauran matattu ba su sāke rayuwa ba, sai da shekaru dubun nan suka cika.) Wannan fa shi ne tashin matattu na farko.
6 Unan seru ngongon Kutelle ule na ata yitu unan fitun chizinu. ukul unbe ba yitu nin likaran kifuani ba iba yitu apirist Kutelle nin Yisa iso nan ngne udu akus limui ye.
Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu.
7 Kubi ko na akus limui ye da ligang, shaitan ngne iba nutun ngne nya kilari lichin.
Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake,
8 Aba nuzu arusuzu nmin-nmin na sari anas nye-e mog nin magog ba yiruani amunu bara likume mgbardan mine yitu nofo i chin chin kurawa.
zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku.
9 Na inuzu nya kanang nye-e na anit Kutelle duku, mmin nsu nayi Kutelle, ula nuzu kitene Kutelle uda jujuani vat.
Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su.
10 ibilis, ule na wa rusuzu ani, a me iturum ngne nya nla ujujuzu, ki ka na iturno kumunche ku na nan kadura kinuu me-e, kikane kitik nin lirin udun malun yi. (aiōn g165, Limnē Pyr g3041 g4442)
Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin. (aiōn g165, Limnē Pyr g3041 g4442)
11 Nnin yene ki ti lisosin libo-o nin le na asosin kitene, uye-e nin kitekane cho niyizime na kiti wa duku nworu ido-o ba.
Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu.
12 In yene abi-na didya nin na bebene-iyin nbun kiti lisosin ne, ipuzuno titagarda. In nin puno umon utargarda-utagardan lai. Abe-ale, usu ani usharaa nya nile imon na iyertine nya tigarda, iyerte dursu ile imon na ina su.
Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai.
13 Kurawa kudyawe nutu no ale na ina kuzu nya kunin, ukule nin Hades nun tuno ana kule na iwa din nan ngginu, anan kule isuani usharaa nile imon na ina suzu. (Hadēs g86)
Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. (Hadēs g86)
14 Ukule nin Hades imunu anin ito nya la, ulelere unnare ukul umba-lilem nla. (Hadēs g86, Limnē Pyr g3041 g4442)
Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. (Hadēs g86, Limnē Pyr g3041 g4442)
15 Andi na umon wa se lisa me nya tagarda nlai ba uso iwa turun ngne nya lilem nla une. (Limnē Pyr g3041 g4442)
Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan. (Limnē Pyr g3041 g4442)

< Uruyan Yuhana 20 >