< Yahuda 1 >

1 Yahuda kucin Yesu Kristi nin gwana Yakubu udu ale na iyicila linwana nanya Kutelle ucif nin ciyu Yesu Kreisti.
Yahuza, bawan Yesu Almasihu kuma dan'uwan Yakubu, zuwa ga kirayayyu, kaunatattu a cikin Allah Uba, kebabbu domin Yesu Kristi:
2 Na ayi akunekune udu kitimine nin sheu nibinai nin suu tigbardan
bari jinkai da salama da kauna su ribabanya a gare ku.
3 Linwana in wadin shuu liti kang inyerti minu mbelen nlirunse nla, imile na nyertin minu in zazin minu ikpiyin ushu natin nyinu sa uyenu ule na iwa nakpa anit alau.
Kaunatattu, ina iyakar kokari in rubuta maku game da ceton mu duka, ya zama dole in gargade ku sosai game da bangaskiya wadda aka mika wa masu bi sau daya tak ba kari.
4 Bara naamong anit wadak likire ale na uchankuulobmine iyertine uwoeru anan sali fiu Kutelle ale na ina saka alheri Kutelle bit udu nuzu nanm nawani ahhe, nin nale na ita amusu nchikilari nin nan bunbite Yesu Kristi.
Don wasu mutane sun sadado sun shigo da sanda a asirce wadanda an rubuta game da hukuncin su tun da dadewa-mutane marasa imani, wanda suka canza alherin Allah zuwa lalata, kuma sun karyata makadaicin Shugaba da Ubangijinmu, Yesu Almasihu.
5 Nene ndin wuru inlizin minu kodashike iyiru vat niming au cikilari wa nutun anit nanya unuzu myin Mmasar bara nani amolu ale na iyina ba.
Ina so in tunashe ku-ko da shike kun rigaya kun san abin, da cewa Allah ya ceci wasu mutane daga kasar masar, amma daga baya ya hallaka wadanda basu ba da gaskiya ba.
6 Nin nnono kadura Kutelle ale na iwa cin katwa mine, i suna kiti lisosin mine kicine Kutelle na ce nani nanya nisarka nsirtin sa ligan udu udiya lirulole. (aïdios g126)
Kuma mala'iku wadanda ba su rike matsayin ikon su ba, amma suka bar wurin zaman su na ainihi-Allah ya tsare su a sarka na har'abada a cikin bakin duhu domin babban ranar shari'a. (aïdios g126)
7 I masin nafo Usodom nin Gomora nin nigbiri naa na niea di nkiline, ale na iwa libaw lirume na awa ni atimine ni mon inanzang ndurtu kuna nizi kuhem. I wa suu anan gbaduzu na iwa neu un nnla unsa ligang. (aiōnios g166)
Suna nan kamar Saduma da Gwamrata da kuma biranen da ke kewaye da su, wadanda suka ba da kansu ga fasikanci suna bin sha'awoyi wanda ba na dabi'a ba. Aka mai da su abin misalin wadanda suka sha wuta mara matuka. (aiōnios g166)
8 Nin nani libau lirume alele nanza nidowo mine nanya namoro, inarsi anan natet tigo, nani ibele inun inanzan kusari nanan natt udia.
Haka kuma, wadannan masu mafarkan suna lalatar da jikinsu. Suna raina masu mulki, kuma suna fadar miyagun abubuwa a kan masu daukaka.
9 Bara ame Makailu unan kadura Kutelle udiya na awadi ugon nsirti mayardan kitene liben Musa, na awa yinin ada ni mabucubucu sa ti gbulan tizogo ba inworonani aworo, ''Na ucife kpada fi.''
Amma ko Mika'ilu babban mala'ika, a lokacin da yake jayyaya da muhawara da shaidan a kan gawar Musa, bai kuskura ya fadi wata kalmar hukunci a kansa ba. Maimakon haka ya ce, “Bari Ubangiji ya tsauta maka!''
10 Bara nani anit alena vat zoguzo imonle na iyino ba vat ni lemong na iyino makeke Kutelle nafo makeke insali nibinai nile imuwne inanza mminu.
Amma waddannan mutane suna kawo batanci game da dukan abin da ba su gane ba. Wadannan mutane masu halin dabbobi ne, suna kwa jawo wa kansu hallaka kenan.
11 Kash mine! bara na ina cina nanya libau kainu, inanin pira ndina ntanu Balam nsu nikurfun, inani diku zemzamlibau Kora unan mayardan.
Kaiton su! Domin sun bi hanyar Kayinu, kuma sun tsunduma cikin kuskuren Bal'amu domin samun riba. Suka hallaka cikin husuma irin ta Kora.
12 Alelere ale na i yeshin nagilitin nsufe na ina lii ninfi, sancin idin pillu ma atiminere mung iso a wut sa wuru ale na ufunu asu uyira aca akune sa kumat, ukul tiba, tijiye martiza.
Wadannan hatsari ne a boye cikin bukukuwan ku na kauna. Suna shagali ba kunya ba tsoro, suna ciyar da kansu kadai. Su holokon hadari ne marar ruwa, wanda iska ke korar sa. Su itatuwa ne shirim ba yaya, mattatu ribi biyu, tumbukakku tun daga saiwa.
13 Ufunu nanya kurawa, anutuzuno kupunjetnceen mine, iyinin galu bara inunye usiriu nanya insirti na na yashe nani se saligan. (aiōn g165)
Su rakuman teku ne masu hauka, suna fahariya cikin kumfar kunyar su. Su kamar taurari ne masu tartsatsi. Wadanda aka tanada wa duhu baki kirin na har abada. (aiōn g165)
14 Nin bara anit alele nan Enok unan zur unuzu Adamu iwa beling aworo, ' Yene! Ucif bit nda nin namiu m likure nanit alau,
Ahnuhu, mutum na bakwai daga Adamu, ya yi anabci game da su cewa, “Duba, Ubangiji zai zo da tsarkakan sa dubun dubbai.
15 inin suu ma wucuwucu udu kin kogha, anin tecu anan sali ncin dert nin nitwa ninanzan mine nanya na isu nanya nibinai ni nanzan nin nimun ididya ile na ann kulapi na malu belinghe.
Domin ya zartar da hukunci a kan dukan kowa, ya kuma cakune dukan marasa da'a a cikin dukan ayyukan su na rashin da'a wanda suka aikata a hanyar da bata cancanta ba, da kuma kalmomi masu kaifi da masu zunubi suka fada game da shi.”
16 Alelere anan tibula na idin su mun ile na nibinai mere taa usuwe, anan foo figiri ruu namong inan se ulin bun.
Wadannan masu cecekuce ne, masu gunaguni, wadanda ke bin sha'awar su ta mugunta, masu tinkaho da fahariya, masu bambadanci domin ribar kansu.
17 Bara nani anum linwa na lizinong tigbulan too na iwa belu nin burne na nann lirinu ncif bite Yesu Kristi.
Amma ku, kaunatattu, ku tuna da kalmomin da manzannin Yesu Almasihunmu suka gaya maku tun da.
18 Iwa woro minu nayiri nimalinghe anan sissuu ma dak, ima dofunu kata kanazan ka nibinai mine.
Sun ce maku, “A cikin kwanaki na karshe, za a samu masu ba'a, wadanda ke bin sha'awoyin su na rashin ibada,”
19 Ale anite di nin suu nanti, na idinin nfip milauwa ba.
Wadannan mutane masu haddasa tsatsaguwa ne, kuma su yan duniya ne, ba su kuma da Ruhu.
20 Bara nani anu n linwana, bara na ina kee atimine ketene u yinu sa u yenu udya nin nlira muu na idin tizu nanya infep milau.
Amma ku, kaunatattu, ku gina kanku a cikin mafificiyar bangaskiyar ku mai daraja, kuma kuna addu'a a cikin Ruhu Mai Tsarki.
21 Ceu atimine nanya nsu Kutelle, Iyerje ikunekunwe ncef bite Yesu Kristi unan lai sa ligang. (aiōnios g166)
Ku rike kanku a cikin kaunar Allah, kuna kuma jiran jinkan Ubangijinmu Yesu Almasihu wanda ke kawo rai na har abada. (aiōnios g166)
22 Nin yerju nkunekune nati na mong anit ale na idi nin nibinai nibaba
Ku nuna jinkai ga masu shakku. Ceci wadansu ta wurin fizge su daga wuta.
23 Nin tucu na mo, ikpalizin nani nanya nla nin namong lanzan nkunekune nin fiu nafo na inari kultuk koo na indinong kidowo nnanza.
Ga wadansu kuma ku nuna jinkai da rawar jiki, kuyi kyamar koda tufafin jikinsu ma.
24 Nene udu ule na ama kesu fi utirzu a ceu fi nbun nle na ama yantifi sa kulapi nanya mmang sa ligan,
Yanzu, zuwa ga wanda yake da iko ya hana ku tuntube, ya kuma sa ku tsaya a gaban madaukakiyar kasancewarsa, marasa abin zargi da kuma murna mai yawa,
25 udu iti Kutelle cas unan tucubite nanya Yesu Kristi Ucif bite, liru, tigo nin likara uburnu nin nene, nin salingang. Usonani. (aiōn g165)
zuwa ga Allah makadaici mai ceton mu ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu, daukaka, da girma, da mulki, da iko su kasance, kamin dukan lokuta, yanzu, da har abada. Amin. (aiōn g165)

< Yahuda 1 >