< 1 Ukorintiyawa 4 >

1 Nene na unit yenje ari nafo ne, iba yenju ari a cin Kristi nin na nan katuwa nliru Kutellẹ ulinyeshin.
Saboda haka, ya kamata mutane su ɗauke mu a matsayin bayin Kiristi, da kuma a matsayin waɗanda aka ba su amanar asirin abubuwan Allah.
2 Vat nene ile imon na idin piziru usẹ unare na iyinin ninghe.
Yanzu fa, ana bukatar waɗanda aka ba su riƙon amana, dole su zama masu aminci.
3 Bara nani kitining imon icing ghari anung su usharia, sa ushariya nanit asurne. Bara meng wang na nsu litinin ushariya ba.
Ƙaramin abu ne a gare ni a ce ku ne za ku gwada ni, ko kuwa a gwada ni a wata kotun mutane, ai, ko ni kaina ba na yanka wa kaina hukunci.
4 Na meng yiru imomon ile na idin belle litinighe ba, bara nani na uso unan ndiru ba. Chikilari unan su nsharia.
Lamirina bai ba ni laifi ba, sai dai wannan bai mai da ni marar laifi ba. Ubangiji ne mai hukunta ni.
5 Bara nani na iwabọ usharia kitenne nimomon a kube dutu, na ame Chikilare nsa ba. Aba damun nin nimon ikanang na inyeshin nan nya nsirti, a puun kibinai. Nanere kogha ba seru uru me kiti Kutellẹ.
Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.
6 Nene, nuwana nilime nan nishono, inna su ile imone meg litinighe nin Apollos bara anughe, bara kiti bite anun yinno ile imon na idin bellu, “Na iwa kata ille imon na ina nyertu ba bellin.” Bara nin nani na umon nan nya mine wan ghantin litime kitene nmon ba.
To, fa’yan’uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afollos saboda ku, don ku yi koyi da mu a kan abin da ake nufi da cewa, “Kada ku zarce abin da yake a rubuce.” Ta haka, ba za ku yi taƙama da wani mutum fiye da wani ba.
7 Ghari di yenju umon di ugang kitin na mong? Iyaghari idumun ile na ina filinfiyari ba, andi ina filinferi, iyari udin nfo figiri nafo na usu nane ba?
Wa ya ce ka fi sauran mutane? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? In kuma karɓa ka yi, me ya sa kake taƙama kamar ba karɓa ba ne ka yi?
8 Una malu use vat nile imon na udin nin suwe! Una mallu use imon nachara! Nenere uma su tigoh, bara tinanse tisu tigowe nanghinu.
Kun riga kun sami duk abin da kuke nema! Kun riga kun yi arziki! Kun zama sarakuna, kun kuma zama haka ɗin ba tare da mu ba! Da a ce kun riga kun zama sarakuna mana da sai mu zama sarakuna tare da ku!
9 Meng ndin nkpilizu Kutellẹ na cheu ari nono kadura nafo anit alle na idin nca nkul. Tiso uyii imon yenju udu nono nanan kadura Kutellẹ nin nanit asurne.
Gama a ganina fa, Allah ya baje mu manzanni a ƙarshen jerin gwanon, a matsayin mutanen da aka hukunta ga mutuwa a filin wasanni. Mun zama abin kallo ga dukan duniya, ga mala’iku da kuma mutane.
10 Arik allalag bara Kristi, annug ajinjinghari nanyan Kristi, arik ana nsali nakara, anug anan nakara, ina ghantin anunku, ina toltin arik ku.
Mun zama masu wauta saboda Kiristi, ku kuwa kuna da hikima sosai a cikin Kiristi! Ba mu da ƙarfi, amma ku kuna da ƙarfi! Ana girmama ku, mu kuwa ana ƙasƙantar da mu!
11 Udak ko kube nene tidin kukpong ayin nin kotu nayi mmen sa imon kidowo icine ina fo ari kang na tidumun nilari ba.
Har yă zuwa wannan sa’a, yunwa da ƙishirwa muke ciki, muna sanye da tsummoki, ana wulaƙanta mu, ba mu kuma da gida.
12 Tidinsuu katuwa kaag, katuwe nin nachara bite, iwa yassu ari asa tise mmari, ti kuru tineu assa ti tere nibinai.
Muna aiki da gaske da hannuwanmu. In aka la’anta mu, mukan sa albarka. In aka tsananta mana, mukan jimre;
13 Iwa nanza nari lissa, assa tilira nin mang. Har tina so tisso, ina dun yenje ari nafo likinkin nyi nin nimon izemzem vat.
in aka ɓata mana suna, mukan mayar da alheri. Har yă zuwa wannan lokaci, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.
14 Na ndin nyertu ille imone nti minu iso imon ncin ba bara nkelle munu nafo nono nayi nigh.
Ba don in kunyata ku ba ne na rubuta wannan, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa ku’ya’yana ne, ƙaunatattu.
15 Assa idumun nanan ndursuzu minu nimon amui likureri nan nya Kristi, na idumun nacif gbardang ba, bara meng naso ucif mine nan nya Kristi Yisa nan nya liru Kutellẹ.
Ko da kuna da iyayen riƙo dubu goma cikin Kiristi, ba ku da ubanni da yawa, gama a cikin Kiristi Yesu, na zama mahaifi a gare ku, ta wurin bishara.
16 Bara nani sun nafo menghe.
Saboda haka, ina roƙonku ku yi koyi da ni.
17 Unare nati nto minu Timoti ku, kitimine gonni na nya yinnu sa uyenu gono nya Nchikilari, aba lizinmunu tiba nighe nan nya Kristi, nafo na ndin dursuzu nani vat natii Kutellẹ.
Saboda wannan dalili ina aika muku Timoti, ɗana, wanda nake ƙauna, mai aminci kuma a cikin Ubangiji. Zai tunashe ku game da yadda za ku bi Kiristi Yesu da kuma yadda ya yi daidai da yadda nake koyarwa a ko’ina, a kowace ikkilisiya.
18 Nene among mine dumin nghantinu, insu nafo na mba dak kitimine ba.
Waɗansunku suna tsammani ba zan zo wurinku ba har suna ɗagankai.
19 Nba dak kitimine nene nin nyinnu Kutellẹ. Kikaneri mba nin yennu ligan nliru na nan nghantinu nati, Vat nani yinnọ akara mine.
Amma in Ubangiji ya yarda zan zo wurinku ba da daɗewa ba. Sa’an nan zan bincike ko masu wannan yawan ɗagan kan nan suna da wani iko.
20 Bara na kilari tigoh Kutellẹ na ligan nlirari ba, likara ri.
Gama mulkin Allah ba cika baki ba ne, sai dai ga iko.
21 Iyaghari idumun suwe? Ndak kitimine nin lishonna sa usu nan nya nfip mishau?
Wanne kuka fi so in na zo? Kuna so in tsananta muku ko in zama mai hankali da kuma sauƙinkai?

< 1 Ukorintiyawa 4 >