< 마가복음 7 >

1 바리새인들과 또 서기관 중 몇이 예루살렘에서 와서 예수께 모였다가
Farisawa suka taru wurin Yesu tare da wadansu marubuta wadda suka zo daga Urushalima.
2 그의 제자 중 몇 사람의 부정한 손 곧 씻지 아니한 손으로 떡 먹는 것을 보았더라
Sun ga cewa wasu daga cikin almajiransa sun ci gurasa da hannuwa marasa tsabta, wato, basu wanke hannu ba,
3 (바리새인들과 모든 유대인들이 장로들의 유전을 지키어 손을 부지런히 씻지 않으면 먹지 아니하며
(Domin Farisawa da dukan Yahudawa ba su cin abinci sai dole sun wanke hannu da kyau domin suna kiyaye al'adun dattawa.
4 또 시장에서 돌아와서는 물을 뿌리지 않으면 먹지 아니하며 그 외에도 여러가지를 지키어 오는 것이 있으니 잔과 주발과 놋그릇을 씻음이러라)
Idan Farisawa suka dawo daga kasuwa, wajibi ne su yi wanka kamin su ci abinci. Akwai sauran al'adun da suke kiyayewa, kamar wanke moda, tukwane, da wasu santula na dalma, har da dakin cin abinci.)
5 이에 바리새인들과 서기관들이 예수께 묻되 어찌하여 당신의 제자들은 장로들의 유전을 준행치 아니하고 부정한 손으로 떡을 먹나이까
Farisawa da Marubuta suka tambaye Yesu, “Don me almajiran ka basu kiyaye al'adun dattawa, domin suna cin abinci ba tare da sun wanke hannu ba?”
6 가라사대 이사야가 너희 외식하는 자에 대하여 잘 예언하였도다 기록하였으되 이 백성이 입술로는 나를 존경하되 마음은 내게서 멀도다
Amma ya amsa masu cewa, “Ishaya ya yi anabci akan ku masu bautan ganin ido, da ya rubuta cewa 'wadanan mutane suna girmama ni a baka amma zuciyar su tana nesa da ni.
7 사람의 계명으로 교훈을 삼아 가르치니 나를 헛되이 경배하는도다 하였느니라
Sujadar wofi suke mani suna koyar da ka'idodi na mutane a matsayin rukunansu'”.
8 너희가 하나님의 계명은 버리고 사람의 유전을 지키느니라
Kun watsar da dokar Allah sai kuka rungumi al'adun mutane.
9 또 가라사대 너희가 너희 유전을 지키려고 하나님의 계명을 잘 저버리는도다
Sai yace masu, kun yi nasara wurin kau da dokokin Allah domin ku kiyaye al'adun ku na mutane.
10 모세는 네 부모를 공경하라 하고 또 아비나 어미를 훼방하는 자는 반드시 죽으리라 하였거늘
Koda shike Musa ya rubuta cewa, “ka girmama Ubanka da Uwarka”, kuma, “duk wanda ya zagi Ubansa ko Uwatasa, ya cancanci mutuwa nan take”.
11 너희는 가로되 사람이 아비에게나 어미에게나 말하기를 내가 드려 유익하게 할 것이 고르반 곧 하나님께 드림이 되었다고 하기만 하면 그만이라 하고
Amma kun ce, 'idan mutum ya ce wa iyayensa, “duk taimakon da ya cacanci ku samu daga guna ya zama kebabbe (wato, 'na mika wa Allah)”'.
12 제 아비나 어미에게 다시 아무 것이라도 하여 드리기를 허하지 아니하여
Sabo da haka, kun ba shi izini kada ya yi wa Ubansa ko Uwatasa wani abu.
13 너희의 전한 유전으로 하나님의 말씀을 폐하며 또 이같은 일을 많이 행하느니라 하시고
Kuna mayar da dokan Allah abin banza, sabili da al'adun ku da kuka mika masu. Wannan, da wasu abubuwa kamar haka kuke yi.”
14 무리를 다시 불러 이르시되 너희는 다 내 말을 듣고 깨달으라
Ya kara kiran taron jama'ar yace masu, “ku kasa kunne gareni, kuma ku gane.
15 무엇이든지 밖에서 사람에게로 들어가는 것은 능히 사람을 더럽게 하지 못하되
Babu wani abu daga wajen mutum da zai iya gurbatar da shi har idan ya shiga cikinsa. Amma, abinda ya fita daga cikinsa shike gurbatar da shi”
16 사람 안에서 나오는 것이 사람을 더럽게 하는 것이니라 하시고
Bari mai kunnen ji, ya ji.
17 무리를 떠나 집으로 들어가시니 제자들이 그 비유를 묻자온대
Da Yesu ya bar taron jama'ar, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma'anar wannan misali.
18 예수께서 이르시되 너희도 이렇게 깨달음이 없느냐 무엇이든지 밖에서 들어가는 것이 능히 사람을 더럽게 하지 못함을 알지 못하느냐
Sai Yesu yace, 'ashe baku da ganewa? ko baku sani cewa abin da ya shiga cikin mutum daga waje ba zai iya gurbatar da shi ba,
19 이는 마음에 들어가지 아니하고 배에 들어가 뒤로 나감이니라 하심으로 모든 식물을 깨끗하다 하셨느니라
domin ba zai iya kai wa cikin zuciyarsa ba, sai dai ya shiga cikin sa ya kuma fita a matsayin bayan gari a salga”. Da wannan magana, Yesu ya mayar da dukan abinci ya zama da tsabta.
20 또 가라사대 사람에게서 나오는 그것이 사람을 더럽게 하느니라
Ya ce, abinda ke cikin mutum shike gurbatar da shi
21 속에서 곧 사람의 마음에서 나오는 것은 악한 생각 곧 음란과 도적질과 살인과
Domin daga cikin mutum, kuma daga cikin zuciyarsa ne, mugun tunani, lalata, sata, kisa,
22 간음과 탐욕과 악독과 속임과 음탕과 흘기는 눈과 훼방과 교만과 광패니
zina, kwadayi, mugunta, hai'inci, mugun guri, kishi, zargi, girmankai, wawanci.
23 이 모든 악한 것이 다 속에서 나와서 사람을 더럽게 하느니라
Duk wadannan miyagun abubuwa suna fitowa ne daga cikin mutum, kuma suke gurbatar da shi.”
24 예수께서 일어나사 거기를 떠나 두로 지경으로 가서 한 집에 들어가 아무도 모르게 하시려하나 숨길 수 없더라
Ya tashi daga nan ya tafi shiyyar Sur da Sida. Ya shiga wani gida don baya son wani ya sani cewa yana nan, amma bai iya boyuwa ba.
25 이에 더러운 귀신 들린 어린 딸을 둔 한 여자가 예수의 소문을 듣고 곧 와서 그 발 아래 엎드리니
Amma nan da nan wata mace, wadda diyarta ke da mugun ruhu-wannan mace kuwa ta ji game da Yesu sai ta zo ta durkusa a gabansa.
26 그 여자는 헬라인이요 수로보니게 족속이라 자기 딸에게서 귀신 쫓아 주시기를 간구하거늘
Matar yar kasar Girka ce, kuma asalinta daga Fonishiya take. Ta roke shi da ya fitar da mugun ruhun nan daga diyarta.
27 예수께서 이르시되 자녀로 먼저 배불리 먹게 할지니 자녀의 떡을 취하여 개들에게 던짐이 마땅치 아니하니라
Sai ya ce mata, “Bari a ciyar da 'ya'ya tukuna. Domin bai kamata a dauki abincin yaya a ba karnuka ba”.
28 여자가 대답하여 가로되 주여 옳소이다마는 상 아래 개들도 아이들의 먹던 부스러기를 먹나이다
Sai ta amsa masa cewa, “I, Ubangiji, Karnukan ma sukan ci abincin da ke fadowa daga teburin 'ya'yan.”
29 예수께서 가라사대 이 말을 하였으니 돌아가라 귀신이 네 딸에게서 나갔느니라 하시매
Ya ce mata, “domin kin fadi haka, kina iya ki tafi domin aljani ya fita daga diyarki.”
30 여자가 집에 돌아가 본즉 아이가 침상에 누웠고 귀신이 나갔더라
Ta koma gida sai ta iske diyarta na kwance akan gado, aljanin ya fice daga jikinta.
31 예수께서 다시 두로 지경에서 나와 시돈을 지나고 데가볼리 지경을 통과하여 갈릴리 호수에 이르시매
Ya sake fita daga shiyar Sur, ya biyo ta Sidon, har zuwa tekun Galili a shiyar Dikafolis.
32 사람들이 귀먹고 어눌한 자를 데리고 예수께 나아와 안수하여 주시기를 간구하거늘
Sun kawo masa wani kurma, kuma bebe ne shi, suna rokansa ya dora hanuwansa a bisansa.
33 예수께서 그 사람을 따로 데리고 무리를 떠나사 손가락을 그의 양 귀에 넣고 침뱉아 그의 혀에 손을 대시며
Sai ya jawo shi daga taron jama'ar, zuwa gefe, sai ya sa hanunsa a kunuwan beben bayan ya tufa yawunsa, sannan ya taba harshensa.
34 하늘을 우러러 탄식하시며 그에게 이르시되 에바다 하시니 이는 열리라는 뜻이라
Ya dubi sama, ya ja numfashi ya ce masa, “Ifatha”, wato, “bude!”
35 그의 귀가 열리고 혀의 맺힌 것이 곧 풀려 말이 분명하더라
Nan da nan ya mayar masa da jinsa. abinda ya daure harshensa ya sake shi, sai ya fara magana da kyau.
36 예수께서 저희에게 경계하사 아무에게라도 이르지 말라 하시되 경계하실수록 저희가 더욱 널리 전파하니
Ya umarce su da kada su gaya wa wani. Amma duk da umarnin da yake basu, suna ta shaida shi ko'ina.
37 사람들이 심히 놀라 가로되 그가 다 잘 하였도다 귀머거리도 듣게 하고 벙어리도 말하게 한다 하니라
kuma suna ta mamaki cewa, “Yayi kowanne abu da kyau, har ya sa kurame suna jin magana, da kuma bebaye na magana.”

< 마가복음 7 >