< Ru’uya ta Yohanna 19 >

1 Bayan wadannan abubuwa na ji wata karar da ta yi kamar muryar mutane masu yawa a sama suna cewa, “Halleluya. Ceto, daukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu.
Après cela, j'entendis dans le ciel quelque chose comme la voix forte d'une grande foule qui disait: Alléluia! Le salut, la puissance et la gloire appartiennent à notre Dieu;
2 Hukunce - hukuncensa gaskiya ne da adalci, domin ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta kazamtar da duniya da fasikancinta. Ya dauki fansar jinin bayinsa, wadda ita da kanta ta zubar.”
car ses jugements sont vrais et justes. Car il a jugé la grande prostituée qui corrompait la terre par son immoralité sexuelle, et il a vengé de sa main le sang de ses serviteurs. »
3 Suka yi magana a karo na biyu: “Halleluya! Hayaki na tasowa daga wurinta har abada abadin.” (aiōn g165)
Un deuxième a dit: « Alléluia! Sa fumée monte aux siècles des siècles. » (aiōn g165)
4 Dattawan nan ashirin da hudu da rayayyun halittun nan hudu, suka fadi suka yi wa Allah sujada shi da yake zaune a kan kursiyin. Suna cewa, “Amin. Halleluya!”
Les vingt-quatre anciens et les quatre êtres vivants se prosternèrent et adorèrent le Dieu qui est assis sur le trône, en disant: « Amen! Alléluia! »
5 Sai wata murya ta fito daga kursiyin tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, dukanku bayinsa, ku da kuke tsoronsa, da duk marasa iko da masu iko.”
Une voix s'éleva du trône, disant: « Louez notre Dieu, vous tous ses serviteurs, vous qui le craignez, petits et grands! »
6 Sai na ji murya kamar na kasaitaccen taron mutane, kamar rurin kogi na ruwaye masu yawa, kuma kamar tsawar aradu, cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji yana mulki, Allah mai iko duka.
J'entendis quelque chose comme la voix d'une grande foule, comme la voix de grandes eaux, et comme la voix de puissants tonnerres, disant: « Alléluia! Car le Seigneur notre Dieu, le Tout-Puissant, règne!
7 Bari mu yi murna, mu yi farinciki matuka mu kuma ba shi daukaka domin bikin auren Dan Ragon ya zo, amaryarsa kuma ta shirya kanta.
Réjouissons-nous et soyons dans l'allégresse, et rendons-lui gloire. Car les noces de l'Agneau sont arrivées, et sa femme s'est préparée. »
8 An yardar mata ta sa kaya masu haske da tsabta na lilin mai laushi” (domin lilin mai laushi shine ayyukan adalci na tsarkaka).
Il lui a été donné de se revêtir d'un lin fin, brillant et pur, car le lin fin, ce sont les actes justes des saints.
9 Mala'ika ya ce mani, “Rubuta wannan: Masu albarka ne wadanda aka gayyace su zuwa bikin auren Dan Ragon.” Ya kuma ce mani, “Wadannan kalmomin Allah na gaskiya ne.”
Il me dit: « Ecris: « Heureux ceux qui sont invités au repas de noces de l'Agneau! ». Il me dit: « Ce sont les vraies paroles de Dieu. »
10 Na fadi a gaban kafafunsa domin in yi masa sujada, amma ya ce mani, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne tare da kai da 'yan'uwanka wadanda ke rike da shaida game da Yesu. Yi wa Allah sujada, domin shaida game da Yesu shine ruhun annabci.”
Je me suis jeté à ses pieds pour l'adorer. Il m'a dit: « Regarde! Ne fais pas cela! Je suis compagnon de servitude avec toi et avec tes frères qui détiennent le témoignage de Jésus. Adorez Dieu, car le témoignage de Jésus est l'Esprit de prophétie. »
11 Sai na ga sama a bude, na kuma duba sai ga wani farin doki. Mahayinsa ana kiransa amintacce da gaskiya. Yana shari'a da adalci yana yaki.
Je vis le ciel ouvert, et voici un cheval blanc. Celui qui le montait s'appelle Fidèle et Véritable. Il juge et combat avec justice.
12 Idanunsa kamar harshen wuta suke, a kansa akwai kambuna da yawa. Yana da suna a rubuce a jikinsa wanda ba wani da ya sani sai dai shi da kansa.
Ses yeux sont une flamme de feu, et il y a sur sa tête beaucoup de couronnes. Il a des noms écrits et un nom écrit que personne ne connaît, sinon lui-même.
13 Yana sanye da riga da aka tsoma a cikin jini, kuma ana kiran sunansa Kalmar Allah.
Il est revêtu d'un vêtement aspergé de sang. Son nom est appelé « la Parole de Dieu ».
14 Rundunonin sama suna biye da shi a kan fararen dawakai, suna sanye da lilin mai laushi, fari mai tsabta.
Les armées qui sont dans le ciel, vêtues de lin blanc, pur et fin, le suivent sur des chevaux blancs.
15 Daga cikin bakinsa takobi mai kaifi na fitowa, da ita yake sarar al'ummai, zai kuma mulke su da sandar karfe. Yana tattake wurin matsar ruwan inabi da matsananciyar fushin Allah Mai iko duka.
De sa bouche sort une épée aiguë, à double tranchant, pour qu'avec elle il frappe les nations. Il les gouvernera avec une verge de fer. Il foule la cuve du vin de l'ardeur de la colère de Dieu, le Tout-Puissant.
16 Yana da suna a rubuce a rigarsa da cinyarsa: “Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.”
Il a sur son vêtement et sur sa cuisse un nom écrit: « ROI DES ROIS ET SEIGNEUR DES SEIGNEURS ».
17 Na ga mala'ika tsaye a rana. Yayi kira da murya mai karfi ga dukan tsuntsaye da ke firiya a sama.
Je vis un ange qui se tenait dans le soleil. Il criait d'une voix forte, disant à tous les oiseaux qui volent dans le ciel: « Venez! Rassemblez-vous pour le grand souper de Dieu,
18 “Ku zo, ku tattaru saboda babban bukin Allah. Ku zo ku ci naman sarakuna, da naman sarakunan yaki, da naman manyan mutane, da naman dawakai, da na mahayansu, da naman dukan mutane, yantattu da bayi, marasa iko da masu iko.”
afin de manger la chair des rois, la chair des chefs militaires, la chair des héros, la chair des chevaux et de ceux qui les montent, et la chair de tous les hommes, libres et esclaves, petits et grands. »
19 Na ga dabban da sarakunan duniya da rundunoninsu. Suna tattaruwa domin su yi yaki da wanda ke bisa doki da rundunarsa.
Je vis la bête, les rois de la terre et leurs armées, rassemblés pour faire la guerre à celui qui était assis sur le cheval et à son armée.
20 Aka kama dabban tare da makaryatan annabawa da suka yi ayyukan al'ajibai a gabansa. Da wadannan alamu ya yaudari wadanda suka karbi alamar dabbar da wadanda suka yi wa siffarta sujada. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin farar wuta mai ci. (Limnē Pyr g3041 g4442)
La bête fut prise, et avec elle le faux prophète qui accomplissait les prodiges par lesquels il séduisait ceux qui avaient reçu la marque de la bête et ceux qui adoraient son image. Ces deux-là furent jetés vivants dans l'étang de feu qui brûle avec du soufre. (Limnē Pyr g3041 g4442)
21 Sauran aka karkashe su da takobin da ke fitowa daga bakin mahayin dokin. Dukan tsuntsaye suka ci gawarwakinsu.
Les autres furent tués par l'épée de celui qui était assis sur le cheval, l'épée qui sortait de sa bouche. Et tous les oiseaux se rassasièrent de leur chair.

< Ru’uya ta Yohanna 19 >