< Markus 2 >

1 Da ya dawo Kafarnahum bayan yan kwanaki kadan, aka ji cewa yana gida. 2 Da yawa suka taru a can, ba wuri har kofa, sai Yesu ya yi masu magana. 3 Sai wadansu mutane su ka zo wurinsa dauke da wuni mutum shanyayye, mutane hudu na dauke da shi. 4 Lokacin da ba su iya zuwa kusa da shi ba domin yawan jama'a, sai su ka daye jinkar dakin daidai da inda ya ke. Bayan da suka huda ramin suka saukar da gado wanda shanyayyen ke kwance a kai. 5 Da ganin bangaskiyarsu, Yesu ya ce wa shanyayyen mutumin, “Da, an gafarta maka zunuban ka”. 6 Amma wadansu marubuta da ke zaune a nan, suka yi tunani aransu. 7 Yaya wannan mutum zai yi magana haka? Ya yi sabo! wa ke iya gafarta zunubi “sai Allah kadai?” 8 Nan da nan Yesu ya sani a ruhunsa, abinda suke tunani a tsakaninsu. Ya ce masu, “Me ya sa kuke tunanin wannan a zuciyarku? 9 Me yafi sauki a cewa shanyayyen mutumin, 'An gafarta maka zunuban ka' ko kwa a ce masa, 'tashi, ka dauki shinfidarka, ka yi tafiyarka'? 10 Amma domin ku san cewa Dan mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya, ya ce wa shanyayyen, 11 ''Na ce maka, tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidan ka.” 12 Sai nan da nan ya tashi ya dauki tabarmarsa, ya fita gidan a gabansu, dukansu su ka yi mamaki, su ka girmama Allah, ''suka ce ba mu taba ganin abu irin wannan ba.” 13 Ya sake fita gefen tafki, dukan taron jama'a suka zo wurinsa, sai ya koya masu. 14 Sa'adda ya na wucewa, ya ga Levi dan Halfa yana zaune a wurin karbar haraji, sai ya ce masa, “Ka biyo ni.” Ya tashi, ya bi shi. 15 Sa'adda Yesu ya shiga gidan Levi yana cin abinci, masu karbar haraji da masu zunubi da yawa su ka zo wurinsa da almajiransa, jama'a masu yawan gaske suka ka bi shi. 16 Da Marubuta wadanda su ke Farisawa, sun ga cewa Yesu na cin abinci da masu zunubi da masu karbar haraji, sai su ka ce wa almajiransa, “Me ya sa ya ke ci da masu karbar haraji da mutane masu zunubi?” 17 Da Yesu ya ji wannan ya ce masu, “Mutane wadanda ke da lafiya a jiki ba su bukatar likita; sai dai ko marasa lafiya ke bukatarsa. Ban zo domin in kira mutane masu a dalci ba, amma mutane masu zunubi.” 18 Almajiran Yahaya da Farisawa suna azumi, sai wadansu mutane suka zo suka ce, “Don me almajiran Yahaya da almajiran Farisawa na azumi amma na ka almajiran ba su yi?” 19 Sai Yesu yace masu, “Abokan ango, za su yi azumi sa'adda ango yake tare da su? muddin suna tare da ango ba za su yi azumi ba. 20 Amma kwanaki za su zo da za a dauki angon daga gare su, a wadancan kwanakin ne, za su yi azumi. 21 Babu wanda zai dinka sabuwar riga ya hada ta da tsohuwar riga, sai rigar ta yage, kuma ta yi mummunar yagewa. 22 Babu wanda zai sa sabon ruwan inabi a cikin tsohuwar salka, ai sai salkar ta fashe kuma ruwan inabin ya zube. duka biyu ruwan inabin da salkar arasa su. A maimakon haka, sai ka sanya sabon ruwan inabi cikin sabuwar salka.” 23 A ranar asabar Yesu ya tafi cikin gonakin hatsi, sai almajiransa su ka fara zagar hatsi, 24 Sai Farisawa su ka ce masa, “Duba, don me suke yin abin da bai dace a yi ranar Asabar ba?” 25 Yace masu, Ba ku karanta ba abinda Dauda ya yi sa'adda yake jin yunwa, shi da mutanen da ke tare da shi? 26 Yadda ya shiga gidan Ubangiji, sa'adda Abiyata ya ke babban firist, ya ci gurasa da ke ta firist wadda bai dace wani ya ci ba sai Firistoci. Har kuma ya ba wadanda ke tare da shi.” 27 Yesu yace, “Asabar an yi ta don mutum ne, ba a yi mutum don Asabar ba. 28 Saboda haka, Dan Mutum Ubangiji ne, har da na Asabar.”

< Markus 2 >