< Luka 23 >

1 Sai duk taron suka tashi, suka kawo Yesu gaban Bilatus.
The whole council rose and took him to Pilate.
2 Suka fara saransa, cewa “Mun same wannan mutum yana ruda kasarmu, ya haramta a ba Kaisar haraji, yana kuma cewa shi da kansa ne Almasihu, sarki.”
There they started to accuse him. “We found this man deceiving our nation, telling people not to pay taxes to Caesar, and claiming he is Messiah, a king,” they said.
3 Bilatus ya tambaye shi, cewa “Shin kaine Sarkin Yahudawa?” Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Haka ka ce.”
“Are you the King of the Jews?” Pilate asked him. “So you say,” replied Jesus.
4 Sai Bilatus ya ce wa manyan firistocin da taro mai yawa, “Ban samu ko laifi daya game da wannan mutumin ba.”
Then Pilate said to the chief priests and the crowds, “I don't find this man guilty of any crime.”
5 Amma suka yi ta cewa, “Yana ta da hankalin mutane da koyarwa a dukan Yahudiya, ya fara daga Galili har zuwa ga wannan wuri.”
But they insisted, saying, “He is inciting rebellion all over Judea with his teachings, from Galilee to right here in Jerusalem.”
6 Sa'adda Bilatus ya ji wannan, sai ya tambaya ko mutumin daga Galiline.
When he heard this, Pilate asked, “Is this man a Galilean?”
7 Sa'adda ya gane cewa yana karkashin mulkin Hirudus, sai ya tura Yesu wurin Hirudus, wanda shi da kansa yana Urushalima a wadannan kwanakin.
When he discovered that Jesus came under Herod's jurisdiction, he sent him to Herod who was also in Jerusalem at the time.
8 Sa'adda Hirudus ya ga Yesu, sai ya cika da farin ciki sosai, saboda ya so ganinsa tunda dadewa. Tun can ya ji game da shi sai ya yi begen ganin wadansu al'ajibai da zai yi.
Herod was very pleased to see Jesus since he had wanted to meet him for a long time. He had heard about Jesus and was hoping to see him perform a miracle.
9 Hirudus ya tambaye Yesu cikin kalmomi masu yawa, amma Yesu bai amsa masa da komai ba.
He asked Jesus many questions, but Jesus did not answer him at all.
10 Sai manyan firistoci da marubuta suka tsaya, suna ta yi masa zargi mai zafi.
The chief priests and religious teachers stood there, angrily accusing him.
11 Hirudus da sojojinsa suka zarge shi, suka kuma yi masa ba'a, suka sa masa tufafi masu kyau, sa'annan ya sake aika Yesu zuwa wurin Bilatus.
Herod and his soldiers treated Jesus with contempt and mocked him. Then they placed a royal robe on him and sent him back to Pilate.
12 Sai Hirudus da Bilatus suka zama abokai a wannan rana (da ma su abokai gaba ne).
From that day on Herod and Pilate were friends—before that they had been enemies.
13 Bilatus ya kira manyan firistoci tare da masu mulki da kuma taron jama'ar,
Pilate called together the chief priests, rulers, and the people,
14 sai ya ce masu, “Kun kawo mani wannan mutum kamar wanda yake jagorar mutane ga munanan ayyuka, ku kuma gani, Ni, na tuhume shi a gabanku, ban sami ko kuskure daya daga mutumin nan game da abinda ku ke zarginsa da shi ba.
and told them, “You brought this man before me, accusing him of inciting the people to rebellion. I've carefully examined him in your presence, and do not find him guilty of the charges you have brought against him.
15 Babu, ko Hirudus ma, ya sake komar mana da shi, kun gani, babu wani abu wanda ya yi da ya cancanci mutuwa,
Neither did Herod, for he sent him back to us. He has done nothing that demands he should be put to death.
16 saboda haka zan yi masa horo sa'annan in sake shi.”
So I will have him flogged and then release him.”
17 [Ya zama dole Bilatus ya sakar wa Yahudawa wani daurarre guda daya lokacin idin.]
18 Amma dukansu suka yi ihu tare, cewa, “A tafi da wannan mutumin, sai a sako mana Barabbas!”
But they all shouted together, “Kill this man, and release Barabbas to us.”
19 Barabbas mutum ne wanda aka sa a cikin kurkuku saboda wani tada hankali a cikin birni da kuma kisankai.
(Barabbas had been put in prison for taking part in a rebellion in the city, and for murder.)
20 Bilatus ya sake yi masu magana, yana so ya saki Yesu.
Pilate wanted to release Jesus, so spoke to them again.
21 Amma suka yi ihu, cewa, “A giciye shi, a giciye shi.”
But they kept on shouting, “Crucify him! Crucify him!”
22 Sai ya sake ce masu sau na uku, “Don me, wace magunta wannan mutum ya yi? Ban sami wani abu da ya isa sanadin mutuwa game da shi ba. Saboda haka bayan na hore shi, zan sake shi.”
Pilate asked them for the third time, “But why? What crime has he committed? I don't find any reason for executing him. So I will have him flogged and then release him.”
23 Amma suka nace da murya mai karfi, suna so a giciye shi, sai muryarsu ta rinjayi Bilatus.
But they continued insisting with loud shouts, demanding that he be crucified. Their shouting succeeded,
24 Sai Bilatus ya yarda ya yi masu bisa ga abin da suke so.
and Pilate gave the sentence they demanded.
25 Ya sako masu wanda suka tambaya ya ba su wanda aka sa a kurkuku domin tada hankali da kuma kisankai. Amma ya ba da Yesu bisa nufinsu.
He released the man imprisoned for rebellion and murder, but he sent Jesus to be put to death in accordance with their demands.
26 Da suka tafi da shi, sai suka kama wani mai suna siman Bakurane, yana zuwa daga karkara, sai suka daura masa giciyen ya dauka, yana biye da Yesu.
As the soldiers led him away, they seized a man called Simon of Cyrene, who had come in from the countryside. They put the cross on him and made him carry it behind Jesus.
27 Babban taron jama'a, da na mata da suke makoki da kuka dominsa, suna binsa.
A large crowd followed him, along with women who were mourning and lamenting him.
28 Amma da ya juya wurinsu, Yesu yace, “Yan matan Urushalima, kada ku yi kuka domina, amma ku yi kuka domin kanku da 'ya'yanku.
Jesus turned to them and said, “Daughters of Jerusalem, don't weep for me. Weep for yourselves and your children.
29 Gama ku gani, kwanaki suna zuwa da za su ce, 'Albarka ta tabbata ga bakararru da wadanda basu taba haihuwa ba da kuma wadanda ba a taba shan mamansu ba.'
For the time is coming when they'll say, ‘Happy are those who are childless, and those who never had babies, and those who never nursed them.’
30 Sa'annan za su fara ce wa duwatsu, 'Ku fado bisanmu,' da tuddai ma, 'Ku rufe mu.'
They'll say to the mountains, ‘Fall down on us,’ and to the hills, ‘Cover us.’
31 Gama idan sun yi wadannan abubuwan lokacin da itace yana danye, me zai faru sa'adda ya bushe?”
For if they do this to wood that is green, what will happen when it's dried out?”
32 Aka kai wadansu mutum biyu masu laifi, domin a kashe shi tare da su.
They also took two others who were criminals to be executed with him.
33 Sa'adda suka zo wurin da a ke kira kwalluwa, nan suka giciye shi da barayin, daya daga hannun damansa dayan kuma daga hannun hagu.
When they reached the place called the Skull they crucified him together with the criminals, one on his right, and the other on his left.
34 Yesu yace, “Uba, ka yafe masu, gama basu san abin da suke yi ba.” Sai suka jefa kuri'a, suka rarraba tufafinsa.
Jesus said, “Father, please forgive them, for they don't know what they're doing.” They divided up his clothes by throwing dice for them.
35 Mutane sun tsaya suna kallo sa'annan masu mulki suna ta yin masa ba'a, cewa, “Ya ceci wadansu. Bari ya ceci kansa, idan shine Almasihu na Allah, zababben nan.”
The people stood and watched and the leaders sneered at Jesus. “He saved others, let him save himself, if he is really God's Messiah, the Chosen One,” they said.
36 Sojojin ma suka yi masa dariya, suna zuwa wurinsa, suna mika masa ruwan tsami,
The soldiers also mocked him, coming up to him and offering him wine vinegar, saying,
37 suna cewa, “Idan kai Sarkin Yahudawa ne, ceci kanka.”
“If you're the King of the Jews, then save yourself.”
38 Akwai wata alama bisansa, “Wannan shine Sarkin Yahudawa.”
Above Jesus was a sign on which it was written, “This is the King of the Jews.”
39 Daya daga cikin barayi wanda aka giciye, ya zage shi, cewa, “Ba kai ne Almasihu ba? Ka ceci kanka da mu.”
One of the criminals hanging there joined in the insults against Jesus. “Aren't you the Messiah?” he asked. “Then save yourself—and us too!”
40 Amma dayan ya amsa, ya tsauta masa cewa, “Ba ka tsoron Allah, da yake shari'arka daya ne da nasa?
But the other criminal disagreed and argued with him, “Don't you fear God even when you're suffering the same punishment?” he asked.
41 Mu kam an yi ma na daidai, gama mun samu bisa ga abin da muka yi. Amma wannan mutum bai yi wani abu mara kyau ba.”
“For us the sentence is right since we're being punished for what we did, but this man didn't do anything wrong.”
42 Sai ya kara, “Yesu, ka tuna da ni sa'adda ka shiga mulkinka.”
Then he said, “Jesus, please remember me when you come into your kingdom.”
43 Yesu ya ce masa, “Gaskiya ina ce maka, yau za ka kasance tare da ni a firdausi.”
Jesus replied, “I promise you today you will be with me in paradise.”
44 Anan nan a wajen sa'a na shida, sai duhu ya mamaye kasar duka har zuwa sa'a na tara
By this time it was around noon and darkness fell over the whole land until three in the afternoon.
45 sa'adda rana ya fadi. Sai labulen haikalin ya rabu a tsakiya zuwa kasa.
The sun's light was shut out, and the Temple veil was torn in two.
46 Da kuka da murya mai karfi, Yesu yace, “Uba, na mika Ruhu na a hannunka.” Bayan da ya fadi wannan, sai ya mutu.
Jesus called out in a loud voice, “Father, I place myself in your hands.” Having said this he breathed his last.
47 Sa'adda jarumin ya ga abin da ya faru, ya daukaka Allah, cewa, “Lallai wannan mutumin mai adalci ne.”
When the centurion saw what had happened he praised God and said, “Surely this man was innocent.”
48 Sa'adda dukan taro mai yawa wadanda suka zo tare domin su shaida da idanunsu suka ga abubuwan da suka faru, suka koma suna bugan kirjinsu.
When all the crowds that had come to watch saw what happened they went home beating their chests in grief.
49 Amma duk idon sani, da kuma matan da suka bi shi tun daga Galili, suka tsaya daga nesa, suna duban wadannan abubuwa.
But all those who knew Jesus, including the women who'd followed him from Galilee, watched from a distance.
50 Ga shi kuwa, wani mutum mai suna Yusufu, shi dan majalisa ne, nagari ne kuma mutum mai adalci ne
There was a man called Joseph who was good and honest. He was a member of the council,
51 (bai yarda da shawarar da kuma abin da suka aikata ba), daga Arimatiya a kasar Yahudiya, wanda yake jiran mulkin Allah.
but he hadn't agreed with its decisions and actions. He came from the Jewish town of Arimathea, and was waiting expectantly for the kingdom of God.
52 Wannan mutum, ya sami Bilatus, ya tambaya a bashi jikin Yesu.
Joseph went to Pilate and asked for Jesus' body.
53 Ya saukar da shi kasa, sai ya nade shi cikin likafani na linin mai kyau, ya kwantar da shi cikin kabari da aka sassaka shi daga dutse, inda ba a taba binne wani ba.
Once he'd taken it down, he wrapped it in a linen cloth. He laid Jesus in an unused tomb cut into the rock.
54 Ranar kuwa, ranar shiri ce, Asabaci kuma ta kusato.
It was preparation day and the Sabbath would soon begin.
55 Matan da suka taho da shi tun daga Galili, suka biyo baya, su ga kabarin da inda aka ajiye shi.
The women who had come with Jesus from Galilee had followed Joseph and had seen the tomb where Jesus' body had been laid.
56 Suka koma, sai suka shirya kayan kamshi da mai. Suka kuma huta a ranar Asabaci bisa ga doka.
They returned home and prepared spices and ointments. But on the Sabbath they rested, observing the commandment.

< Luka 23 >