< Luka 2 >

1 Ananan cikin kwanakin, sai Kaisar Augustas ya yi shela ya umarta a kidaya dukan mutane da ke zaune a cikin duniya. 2 Wannan itace kidaya ta farko da aka yi lokacin da Kiriniyus yake mulkin Suriya. 3 Sabili da haka, kowa ya koma garinsa domin a yi masa rijista domin kidayan. 4 Yusufu kuma ya tashi ya bar birnin Nazarat zuwa garin Baitalami da ke Yahudiya, wanda ake kuma kira birnin Dauda, domin shi daga zuriyar iyalin Dauda ne. 5 Ya je can ya yi rijista tare da Maryamu, wadda yake tashi tana kuma da juna biyu. 6 Ya zama sa'adda suke can, lokaci ya yi da za ta haifi danta. 7 Ta haifi da, dan farinta kuwa, ta nade shi da kyau da 'yan tsummoki. Ta sa shi cikin wani kwami na dabbobi, gama babu daki dominsu a masaukin. 8 A cikin wannan yankin, akwai makiyaya wadanda suke zama a sarari suna tsaron garken tumakinsu da dare. 9 Nan da nan, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare su, daukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, sai suka figita kwarai. 10 Sai mala'ikan ya ce masu, “Kada ku ji tsoro, domin na kawo maku labari mai dadi da zai kawo murna da yawa ga dukan mutane. 11 Yau an haifi maku mai ceto a cikin birnin Dauda! Shine Almasihu Ubangiji! 12 Wannan itace alama da za a ba ku. Za ku ga dan jariri nade cikin 'yan tsummoki kwance cikin kwamin dabbobi.” 13 Nan take, sai ga babban taro daga sama tare da mala'ikan suna yabon Allah, suna cewa, 14 “Daukaka ga Allah daga bisa, bari salama ta kasance a duniya tsakanin mutanen da ya ke jin dadinsu.” 15 Ya zama sa'adda mala'iku suka bar su zuwa cikin sama, sai makiyayan su ka ce wa junansu, “Bari mu je Baitalami mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya nuna mana.” 16 Su ka yi hamzari suka tafi can sun iske Maryamu da Yusufu, suka ga jaririn kuwa kwance a cikin kwamin dabbobin. 17 Bayan da sun ga wannan, suka gaya wa mutane abinda aka gaya masu game da wannan yaro. 18 Dukan wadanda su ka ji, su ka yi mamaki kwarai game da abin da makiyayan su ka gaya masu. 19 Amma ita Maryamu ta ci gaba da tunani akan wadanan abubuwa da ta ji, tana tunani mai zurfi a cikin zuciyarta. 20 Makiyayan suka koma suna ta daukaka da yabon Allah domin dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, dadai da yadda aka gaya masu. 21 Da ya kai kwana takwas, lokacin da za a yi wa jaririn kaciya, sai aka rada masa suna Yesu, sunan da mala'ikan ya bashi kamin a yi cikinsa. 22 Da kwanakin tsarkakewar su ya wuce bisa ga shari'ar Musa, Yusufu da Maryamu suka kawo shi cikin haikali a Urushalima dominsu mika shi ga Ubangiji. 23 Kamar yadda aka rubuta a dokokin Ubangiji, “Za a kira duk da na fari kebabbe ga Ubangiji.” 24 Suka kuma zo su mika hadaya bisa ga yadda aka fada a shari'ar Ubangiji, “Kurciyoyi biyu ko 'yan tantabaru biyu.” 25 Ga shi akwai wani mutum a Ushalima mai suna Siman. Wannan mutum adali ne kuma mai ibada. Yana jiran mai ta'aziyar Isra'ila, kuma Ruhu Mai-sarki na bisansa. 26 An kuma bayyana masa ta wurin Ruhu Mai-tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kristi na Ubangiji. 27 Wata rana Siman ya zo cikin haikali ta wurin jagorar Ruhu Mai-tsarki. Da iyayen suka kawo yaron ciki, wato Yesu, domin su cika sharudan da shari'ar ke bukata, 28 sai Siman ya karbe shi cikin hanuwansa, ya yabi Allah ya ce, 29 “Yanzu bari bawanka ya tafi da salama, Ubangiji, bisa ga kalmarka. 30 Domin idanuna sun ga cetonka, 31 wanda ka shirya a gaban dukan mutane: 32 Haske ne na wahayi ga al'ummai, kuma daukakar mutanenka Isra'ila.” 33 Mahaifin yaron da Mahaifiyarsa, sun yi mamaki kwarai domin abubuwan da aka fada akansa. 34 Sai Siman ya albarkace su ya ce wa uwatasa Maryamu, “Ki ji da kyau, wannan yaro zai zama sanadiyar faduwa da tashin mutane dayawa a Isra'ila, kuma alama wadda ake kushen ta. 35 Kuma takobi zai tsaga zuciyar ki yadda tunanin mutane za ya bayyana.” 36 Wata annabiya mai suna Annatu ta na nan wurin. Ita diyar Fanuyila ce daga kabilar Ashiru. Ta riga ta manyanta a shekaru sosai. Ta kasance da maigidanta shekaru bakwai bayan auren ta, 37 sannan ta yi zama gwambranci na shekaru tamanin da hudu. Ba ta taba barin haikali ba, tana ci gaba da yi wa Ubangiji sujada, dare da rana. 38 A dadai lokacin nan, ta hau zuwa wurinsu ta fara yi wa Allah godiya. Ta gaya wa dukan wadanda ke jiran fansar Urushalima. 39 Da su ka gama komai da aka bukace su suyi bisa ga tafarkin shari'ar Ubangiji, sai suka koma Galili, zuwa birninsu, Nazarat. 40 Yaron kuma ya yi girma ya zama da karfi, yana karuwa da hikima, alherin Ubangiji kuma yana kansa. 41 Iyayensa sukan tafi Urushalima kowacce shekara domin idin ketarewa. 42 Da yana shekara goma sha biyu, suka sake haurawa daidai lokacin idin a al'adance. 43 Bayan da sun cika dukan kwanakin idin, sun fara dawowa gida. Amma dan yaron Yesu ya jinkirta ya zauna a Urushalima, kuma iyayensa basu sani ba. 44 Suna tsammani yana tare da sauran mutane da suke tafiya tare, sai suka yi tafiya na kwana daya. Suka fara neman sa a cikin danginsu da abokansu. 45 Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima suna cigiyar sa a can. 46 Ya zama bayan kwanaki uku, su ka same shi a cikin haikali, yana zama a tsakiyar malamai, yana sauraron su yana kuma yi masu tambayoyi. 47 Dukan wadanda suka ji shi suna ta mamakin fahimtar sa da amsoshin sa. 48 Da suka gan shi, suka yi mamaki kwarai. Mahaifiyarsa ta ce masa, “Da na, don me ka yi mana haka? Ka ji, mahaifinka da ni muna ta neman ka rai a bace.” 49 Ya ce masu, “Don me kuke nema na? Ba ku sani cewa dole in kasance a gidan Ubana ba?” 50 Amma ba su gane abin da yake nufi da kalmomin nan ba. 51 Sa'annan ya koma gida tare da su zuwa Nazarat yana kuma masu biyayya. Mahaifiayarsa kuma ta ajiye dukan wadannan abubuwa a zuciyarta tana yin tunani akansu. 52 Amma Yesu ya ci gaba da hikima da girma, ya kuma karu da tagomashi wurin Allah da mutane.

< Luka 2 >