< Yohanna 19 >

1 Sai Bilatus yayi wa Yesu bulala.
Τότε οὖν ἔλαβεν ὁ Πιλᾶτος τὸν Ἰησοῦν καὶ ἐμαστίγωσεν.
2 Sojojin kuwa suka saka rawanin kaya. Suka kuwa dora wa Yesu a kai suka sa mashi kaya irin na saurata.
καὶ οἱ στρατιῶται πλέξαντες στέφανον ἐξ ἀκανθῶν ἐπέθηκαν αὐτοῦ τῇ κεφαλῇ, καὶ ἱμάτιον πορφυροῦν περιέβαλον αὐτόν,
3 Suka zo wurin sa sukace, “Ranka ya dade, sarkin Yahudawa! sai suka nushe shi.
καὶ ἤρχοντο πρὸς αὐτόν, καὶ ἔλεγον, Χαῖρε, ὁ βασιλεὺς τῶν Ἰουδαίων· καὶ ἐδίδοσαν αὐτῷ ῥαπίσματα.
4 Sai Bilatus ya sake fita waje yace masu, “Dubi, zan kawo maku mutumin domin ku sani ban same shi da wani laifi ba”,
καὶ ἐξῆλθεν πάλιν ἔξω ὁ Πιλᾶτος καὶ λέγει αὐτοῖς, Ἴδε ἄγω ὑμῖν αὐτὸν ἔξω, ἵνα γνῶτε ὅτι οὐδεμίαν αἰτίαν εὑρίσκω ἐν αὐτῷ.
5 Yesu kuwa ya fito, da rawanin kaya da kaya irin na sarauta. Sai Bilatus yace “Ga mutumin nan”.
ἐξῆλθεν οὖν [ὁ] Ἰησοῦς ἔξω, φορῶν τὸν ἀκάνθινον στέφανον καὶ τὸ πορφυροῦν ἱμάτιον. καὶ λέγει αὐτοῖς, Ἰδοὺ ὁ ἄνθρωπος.
6 Da manyan firistocin tare da yan majalisar suka ga Yesu, sai suka yi ta ihu suna cewa “A gicciye shi, A gicciye shi” Sai Bilatus yace masu, “ku dauke shi ku gicciye shi, ni kam ban same shi da wani laifi ba”.
ὅτε οὖν εἶδον αὐτὸν οἱ ἀρχιερεῖς καὶ οἱ ὑπηρέται, ἐκραύγασαν λέγοντες, Σταύρωσον, σταύρωσον. λέγει αὐτοῖς ὁ Πιλᾶτος, Λάβετε αὐτὸν ὑμεῖς καὶ σταυρώσατε· ἐγὼ γὰρ οὐχ εὑρίσκω ἐν αὐτῷ αἰτίαν.
7 Sai Yahudawan sukace mashi, “Ai muna da shari'a, kuma bisa ga shari'ar ya cancanci mutuwa domin ya mai da kansa Dan Allah”.
ἀπεκρίθησαν αὐτῷ οἱ Ἰουδαῖοι, Ἡμεῖς νόμον ἔχομεν, καὶ κατὰ τὸν νόμον ὀφείλει ἀποθανεῖν, ὅτι υἱὸν θεοῦ ἑαυτὸν ἐποίησεν.
8 Da Bilatus ya ji wannan zance sai ya tsorata kwarai.
ὅτε οὖν ἤκουσεν ὁ Πιλᾶτος τοῦτον τὸν λόγον μᾶλλον ἐφοβήθη,
9 Sai ya sake shiga fadar Gwamna, yace wa Yesu, “Daga ina ka fito?” amma Yesu bai amsa mashi ba.
καὶ εἰσῆλθεν εἰς τὸ πραιτώριον πάλιν καὶ λέγει τῷ Ἰησοῦ, Πόθεν εἶ σύ; ὁ δὲ Ἰησοῦς ἀπόκρισιν οὐκ ἔδωκεν αὐτῷ.
10 Sai Bilatus yace masa “Ba zaka yi mani magana ba? Baka san ina da iko in sake ka ba, kuma in gicciye ka?
λέγει οὖν αὐτῷ ὁ Πιλᾶτος, Ἐμοὶ οὐ λαλεῖς; οὐκ οἶδας ὅτι ἐξουσίαν ἔχω ἀπολῦσαί σε, καὶ ἐξουσίαν ἔχω σταυρῶσαί σε;
11 Yesu ya amsa masa, “Ai ba ka da iko a kaina sai dai in an baka daga sama, Saboda haka, wanda ya mika ni a gare ka shine mafi zunubi”.
Ἀπεκρίθη αὐτῷ Ἰησοῦς, Οὐκ εἶχες ἐξουσίαν κατ᾽ ἐμοῦ οὐδεμίαν, εἰ μὴ ἦν δεδομένον σοι ἄνωθεν· διὰ τοῦτο ὁ παραδιδούς μέ σοι μείζονα ἁμαρτίαν ἔχει.
12 Da jin haka, sai Bilatus yayi kokari a sake shi, amma sai Yahudawa suka tada murya sukace, “In ka saki mutumin nan, kai ba abokin Kaisar bane, duk wanda ya maida kansa sarki, ya sabawa Kaisar”.
ἐκ τούτου ὁ Πιλᾶτος ἐζήτει ἀπολῦσαι αὐτόν· οἱ δὲ Ἰουδαῖοι ἐκραύγασαν λέγοντες, Ἐὰν τοῦτον ἀπολύσῃς οὐκ εἶ φίλος τοῦ Καίσαρος. πᾶς ὁ βασιλέα ἑαυτὸν ποιῶν ἀντιλέγει τῷ Καίσαρι.
13 Da Bilatus ya ji irin maganganunsu sai ya fito da Yesu waje ya kuma zauna akan kujeransa a inda ake kira “Dakalin shari'a,” a Yahudanci kuma, “Gabbata.”
ὁ οὖν Πιλᾶτος ἀκούσας τῶν λόγων τούτων, ἤγαγεν ἔξω τὸν Ἰησοῦν, καὶ ἐκάθισεν ἐπὶ βήματος εἰς τόπον λεγόμενον Λιθόστρωτον, Ἑβραϊστὶ δὲ Γαββαθά·
14 To a ran nan ana shirye shiryen idin ketarewa, da misalin sa'a ta shidda kenan, wato tsakar rana, Bilatus yace wa Yahudawan “Ga sarkin ku!”
ἦν δὲ παρασκευὴ τοῦ πάσχα, ὥρα ἦν ὡς ἕκτη. καὶ λέγει τοῖς Ἰουδαίοις, Ἴδε ὁ βασιλεὺς ὑμῶν.
15 Su kuwa suka yi ihu, a tafi da shi, a tafi da shi, a gicciye shi, Bilatus yace masu “In gicciye sarkin ku? Sai manyan firistocin sukace “Ba mu da wani sarki sai Kaisar”.
ἐκραύγασαν οὖν ἐκεῖνοι, Ἆρον ἆρον, σταύρωσον αὐτόν. λέγει αὐτοῖς ὁ Πιλᾶτος, Τὸν βασιλέα ὑμῶν σταυρώσω; ἀπεκρίθησαν οἱ ἀρχιερεῖς, Οὐκ ἔχομεν βασιλέα εἰ μὴ Καίσαρα.
16 Sai Bilatus ya mika Yesu domin su gicciye shi.
Τότε οὖν παρέδωκεν αὐτὸν αὐτοῖς ἵνα σταυρωθῇ. Παρέλαβον οὖν τὸν Ἰησοῦν·
17 Sai suka tafi da Yesu, ya fito yana dauke da gicciyen zuwa wurin da ake kira “Wurin kwalluwa” da Yahudanci kuma “Golgota”.
καὶ βαστάζων αὐτῷ τὸν σταυρόν, ἐξῆλθεν εἰς τὸν λεγόμενον Κρανίου τόπον, ὃ λέγεται Ἑβραϊστὶ Γολγοθά,
18 Suka gicciye Yesu a wurin, tare da wasu mutum biyu, daya a kowane gefe, Yesu kuwa na tsikiya.
ὅπου αὐτὸν ἐσταύρωσαν, καὶ μετ᾽ αὐτοῦ ἄλλους δύο ἐντεῦθεν καὶ ἐντεῦθεν, μέσον δὲ τὸν Ἰησοῦν.
19 Bilatus kuwa ya rubuta wata alama a kan gicciyen, “YESU BANAZARE, SARKIN YAHUDAWA”.
ἔγραψεν δὲ καὶ τίτλον ὁ Πιλᾶτος καὶ ἔθηκεν ἐπὶ τοῦ σταυροῦ· ἦν δὲ γεγραμμένον, Ἰησοῦς ὁ Ναζωραῖος ὁ βασιλεὺς τῶν Ἰουδαίων.
20 Yahudawa da yawa kuwa suka karanta wannan alama domin wurin da aka gicciye Yesu yana kusa da Birnin. Alamar kuwa an rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da Helenanci.
τοῦτον οὖν τὸν τίτλον πολλοὶ ἀνέγνωσαν τῶν Ἰουδαίων, ὅτι ἐγγὺς ἦν ὁ τόπος τῆς πόλεως ὅπου ἐσταυρώθη ὁ Ἰησοῦς· καὶ ἦν γεγραμμένον Ἑβραϊστὶ Ῥωμαϊστὶ Ἑλληνιστί.
21 Sai manyan firistocin yahudawa sukace wa Bilatus, kada ka rubuta sarkin Yahudawa, amma kace, 'wannan yace “Ni ne sarkin Yahudawa”'.
ἔλεγον οὖν τῷ Πιλάτῳ οἱ ἀρχιερεῖς τῶν Ἰουδαίων, Μὴ γράφε, Ὁ βασιλεὺς τῶν Ἰουδαίων, ἀλλ᾽ ὅτι ἐκεῖνος εἶπεν, Βασιλεὺς τῶν Ἰουδαίων εἰμί.
22 Bilatus kuwa ya amsa, “Abinda na rubuta na rubuta kenan.”
ἀπεκρίθη ὁ Πιλᾶτος, Ὃ γέγραφα, γέγραφα.
23 Bayan da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka yayyaga rigarsa kashi hudu, kowane soja da nasa, kashin, sai kuma alkyabbar. Alkyabbar kuwa bata da dinki an saka tane daga sama har kasa.
Οἱ οὖν στρατιῶται, ὅτε ἐσταύρωσαν τὸν Ἰησοῦν, ἔλαβον τὰ ἱμάτια αὐτοῦ, καὶ ἐποίησαν τέσσερα μέρη, ἑκάστῳ στρατιώτῃ μέρος, καὶ τὸν χιτῶνα. ἦν δὲ ὁ χιτὼν ἄραφος, ἐκ τῶν ἄνωθεν ὑφαντὸς δι᾽ ὅλου.
24 Sai sukace wa junansu, “Kada mu yaga alkyabbar, amma kuzo mu jefa kuri'a a kan ta mu gani ko wanene zai dauke ta, anyi haka ne domin a cika nassi cewa “Sun raba rigata a tsakaninsu, sun kuwa jefa kuri'a domin alkyabbata.
εἶπον οὖν πρὸς ἀλλήλους, Μὴ σχίσωμεν αὐτόν, ἀλλὰ λάχωμεν περὶ αὐτοῦ τίνος ἔσται· ἵνα ἡ γραφὴ πληρωθῇ ἡ λέγουσα, Διεμερίσαντο τὰ ἱμάτιά μου ἑαυτοῖς, καὶ ἐπὶ τὸν ἱματισμόν μου ἔβαλον κλῆρον. Οἱ μὲν οὖν στρατιῶται ταῦτα ἐποίησαν·
25 Sojojin suka yi wadannan abubuwa. Uwar Yesu, da 'yar'uwarta, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya. Wadannan mataye suna tsaye kusa da gicciyen Yesu.
εἱστήκεισαν δὲ παρὰ τῷ σταυρῷ τοῦ Ἰησοῦ ἡ μήτηρ αὐτοῦ καὶ ἡ ἀδελφὴ τῆς μητρὸς αὐτοῦ, Μαρία ἡ τοῦ Κλωπᾶ, καὶ Μαρία ἡ Μαγδαληνή.
26 Da Yesu ya ga mahaifiyarsa da almajirin nan da yake kauna tsaye kusa da juna, yace, “Mace, dubi, dan ki!”
Ἰησοῦς οὖν ἰδὼν τὴν μητέρα καὶ τὸν μαθητὴν παρεστῶτα ὃν ἠγάπα, λέγει τῇ μητρί, Γύναι, ἴδε ὁ υἱός σου.
27 Sai yace wa almajirin, “Dubi, mahaifiyarka!” Daga wannan sa'a almajirin ya dauke ta zuwa gidansa.
εἶτα λέγει τῷ μαθητῇ, Ἴδε ἡ μήτηρ σου. καὶ ἀπ᾽ ἐκείνης τῆς ὥρας ἔλαβεν ὁ μαθητὴς αὐτὴν εἰς τὰ ἴδια.
28 Bayan wannan Yesu, saboda ya san yanzu komai ya kammala, domin a cika nassin, sai yace “Ina jin kishi.
μετὰ τοῦτο εἰδὼς ὁ Ἰησοῦς ὅτι ἤδη πάντα τετέλεσται, ἵνα τελειωθῇ ἡ γραφή, λέγει, Διψῶ.
29 A gefensu kuma akwai gora cike da ruwan inabi mai tsami, sai suka tsoma soso a cikin ruwan inabin mai tsami suka daura a wata sanda sai suka mika masa a baki.
σκεῦος ἔκειτο ὄξους μεστόν· σπόγγον οὖν μεστὸν τοῦ ὄξους ὑσσώπῳ περιθέντες προσήνεγκαν αὐτοῦ τῷ στόματι.
30 Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin, sai yace “An gama” Sai ya sunkuyar da kansa ya kuwa saki ruhunsa.
ὅτε οὖν ἔλαβεν τὸ ὄξος [ὁ] Ἰησοῦς εἶπεν, Τετέλεσται· καὶ κλίνας τὴν κεφαλὴν παρέδωκεν τὸ πνεῦμα.
31 Sai Yahudawan, domin ranar shirye shirye ne, domin kada a bar jikunansu akan gicciye har ranar asabacin (domin asabacin rana ce mai muhimmanci), suka roki Bilatus ya kakkarye kafafunsu kuma ya saukar da su.
Οἱ οὖν Ἰουδαῖοι, ἐπεὶ παρασκευὴ ἦν, ἵνα μὴ μείνῃ ἐπὶ τοῦ σταυροῦ τὰ σώματα ἐν τῷ σαββάτῳ, (ἦν γὰρ μεγάλη ἡ ἡμέρα ἐκείνου τοῦ σαββάτου), ἠρώτησαν τὸν Πιλᾶτον ἵνα κατεαγῶσιν αὐτῶν τὰ σκέλη καὶ ἀρθῶσιν.
32 Sai sojojin suka zo suka karya kafafun mutum na farko da kuma mutum na biyun wadanda aka gicciye tare da Yesu.
ἦλθον οὖν οἱ στρατιῶται, καὶ τοῦ μὲν πρώτου κατέαξαν τὰ σκέλη καὶ τοῦ ἄλλου τοῦ συνσταυρωθέντος αὐτῷ·
33 Da suka iso kan Yesu sai suka tarar ya riga ya mutu, sai basu kuwa karya kafafunsa ba.
ἐπὶ δὲ τὸν Ἰησοῦν ἐλθόντες, ὡς εἶδον ἤδη αὐτὸν τεθνηκότα, οὐ κατέαξαν αὐτοῦ τὰ σκέλη,
34 Duk da haka daya daga cikin sojojin ya soki kuibin shi da mashi, nan da nan sai jini da ruwa suka fito.
ἀλλ᾽ εἷς τῶν στρατιωτῶν λόγχῃ αὐτοῦ τὴν πλευρὰν ἔνυξεν, καὶ ἐξῆλθεν εὐθὺς αἷμα καὶ ὕδωρ.
35 Wanda ya ga wannan, shi ya zama shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya sani cewa abinda ya fada gaskiya ne saboda ku ma ku gaskata.
καὶ ὁ ἑωρακὼς μεμαρτύρηκεν καὶ ἀληθινὴ αὐτοῦ ἐστιν ἡ μαρτυρία, καὶ ἐκεῖνος οἶδεν ὅτι ἀληθῆ λέγει, ἵνα καὶ ὑμεῖς πιστεύητε.
36 Wadannan sun faru ne domin a cika nassi, “Babu ko daya daga cikin kasusuwansa da za'a karya”.
ἐγένετο γὰρ ταῦτα ἵνα ἡ γραφὴ πληρωθῇ, Ὀστοῦν οὐ συντριβήσεται αὐτοῦ.
37 Kuma wani nassin yace, “Zasu dube shi wanda suka soka.”
καὶ πάλιν ἑτέρα γραφὴ λέγει, Ὄψονται εἰς ὃν ἐξεκέντησαν.
38 Bayan wadannan abubuwa, Yusufu mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne (amma a boye saboda tsoron Yahudawa) ya roki Bilatus izini domin ya dauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya bashi izini, sai Yusufu yazo ya dauki jikin.
Μετὰ δὲ ταῦτα ἠρώτησεν τὸν Πιλᾶτον Ἰωσὴφ ἀπὸ Ἀριμαθαίας, ὢν μαθητὴς τοῦ Ἰησοῦ κεκρυμμένος δὲ διὰ τὸν φόβον τῶν Ἰουδαίων, ἵνα ἄρῃ τὸ σῶμα τοῦ Ἰησοῦ· καὶ ἐπέτρεψεν ὁ Πιλᾶτος. ἦλθεν οὖν καὶ ἦρεν τὸ σῶμα αὐτοῦ.
39 Nikodimu ma ya zo, wanda da farko ya zo wurin Yesu da daddare, ya kawo hadin man kamshi na mur da al'ul wajen nauyin awo dari.
ἦλθεν δὲ καὶ Νικόδημος ὁ ἐλθὼν πρὸς αὐτὸν νυκτὸς τὸ πρῶτον, φέρων μίγμα σμύρνης καὶ ἀλόης ὡς λίτρας ἑκατόν.
40 Sai suka dauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lillin tare da kayan kamshin nan, domin jana'iza bisa ga al'adar Yahudawa.
ἔλαβον οὖν τὸ σῶμα τοῦ Ἰησοῦ καὶ ἔδη σαν αὐτὸ ὀθονίοις μετὰ τῶν ἀρωμάτων, καθὼς ἔθος ἐστὶν τοῖς Ἰουδαίοις ἐνταφιάζειν.
41 To a wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu, a cikin lambun kuma akwai sabon kabari wanda ba'a taba sa kowa ba.
ἦν δὲ ἐν τῷ τόπῳ ὅπου ἐσταυρώθη κῆπος, καὶ ἐν τῷ κήπῳ μνημεῖον καινόν, ἐν ᾧ οὐδέπω οὐδεὶς ἐτέθη·
42 Da yake ranar shirye shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuwa na kusa, sai suka sa Yesu a ciki.
ἐκεῖ οὖν διὰ τὴν παρασκευὴν τῶν Ἰουδαίων, ὅτι ἐγγὺς ἦν τὸ μνημεῖον, ἔθηκαν τὸν Ἰησοῦν.

< Yohanna 19 >