< 1 Yohanna 4 >

1 Kaunatattu, kada ku amince da kowanne ruhu. Amma ku gwada ruhohi ku gani ko na Allah ne, gama annabawan karya masu yawa sun fito zuwa cikin duniya.
My loved ones, do not put your faith in every spirit, but put them to the test, to see if they are from God: because a great number of false prophets have gone out into the world.
2 Ta haka zaku gane Ruhun Allah, dukkan ruhun da ya amince Yesu Almasihu ya zo cikin jiki na Allah ne,
By this you may have knowledge of the Spirit of God: every spirit which says that Jesus Christ has come in the flesh is of God:
3 kuma dukkan ruhun da bai amince da Yesu ba, ba na Allah bane. Wannan ruhun magafcin Almasihu ne, wanda kuka ji cewa yana zuwa, ya kuwa rigaya yazo cikin duniya.
And every spirit which does not say this is not from God: this is the spirit of Antichrist, of which you have had word; and it is in the world even now.
4 'Ya'yana kaunatattu, daga Allah ke, kuma kun rigaya kun yi nasara da su da yake wanda ke cikinku ya fi wanda ke cikin duniya girma.
You are of God, my little children, and you have overcome them because he who is in you is greater than he who is in the world.
5 Su na duniya ne, saboda haka abin da suke fadi na duniya ne, duniya kuma tana sauraronsu.
They are of the world, so their talk is the world's talk, and the world gives ear to them.
6 Mu na Allah ne, duk wanda ya san Allah yana saurarenmu. Wanda ba na Allah bane, ba ya sauraronmu. Ta haka muka gane ruhun gaskiya da ruhun karya.
We are of God: he who has the knowledge of God gives ear to us; he who is not of God does not give ear to us. By this we may see which is the true spirit, and which is the spirit of error.
7 Kaunatattu, mu yi kaunar juna, gama kauna ta Allah ce, wanda yake kauna an haife shi daga wurin Allah, kuma ya san Allah.
My loved ones, let us have love for one another: because love is of God, and everyone who has love is a child of God and has knowledge of God.
8 Mutumin da baya kauna ba na Allah ba ne, kuma bai san Allah ba, gama Allah kauna ne.
He who has no love has no knowledge of God, because God is love.
9 A cikn haka aka bayyana kaunar Allah a garemu, Allah ya aiko tilon Dansa cikin duniya domin mu rayu ta wurinsa.
And the love of God was made clear to us when he sent his only Son into the world so that we might have life through him.
10 A cikin wannan akwai kauna, ba mune muka kaunaci Allah ba, amma shi ya kaunace mu ya aiko da Dansa ya zama mai gafarta zunubanmu.
And this is love, not that we had love for God, but that he had love for us, and sent his Son to be an offering for our sins.
11 Kaunatattu, da yake Allah ya kaunace mu haka, ya kamata mu kaunaci junanmu.
My loved ones, if God had such love for us, it is right for us to have love for one another.
12 Ba wanda ya taba ganin Allah. Idan muna kaunar juna, Allah yana zaune cikinmu, kuma kaunarsa tana zaune a cikinmu.
No man has ever seen God: if we have love for one another, God is in us and his love is made complete in us:
13 Ta haka mun sani muna zaune a cikinsa shi kuma a cikinmu, saboda ya bamu Ruhunsa.
And his Spirit which he has given us is the witness that we are in him and he is in us.
14 Mun gani mun shaida, cewa Allah ya aiko Dan, domin ya zama mai ceton duniya.
And we have seen and give witness that the Father sent the Son to be the Saviour of the world.
15 Duk wanda ya amince Yesu Dan Allah ne, Allah na zaune cikinsa, shi kuma a cikin Allah.
Everyone who says openly that Jesus is the Son of God, has God in him and is in God.
16 Mun sani kuma mun gaskata da kaunar da Allah yake da ita dominmu, Allah kauna ne wanda yake zama cikin kauna yana zaune cikin Allah, Allah kuma a cikinsa.
And we have seen and had faith in the love which God has for us. God is love, and everyone who has love is in God, and God is in him.
17 Dalilin wannan kauna ta kammala a cikinmu, domin mu kasance da gabagadi a ranar shari'a, domin kamar yanda ya ke haka muma muke a cikin duniyan nan.
In this way love is made complete in us, so that we may be without fear on the day of judging, because as he is, so are we in this world.
18 Babu tsoro a cikin kauna. Amma cikkakiyar kauna takan kawar da tsoro, domin kuwa tsoro na tafi tare da hukunci. Amma wanda yake da tsoro ba shi da cikkakiyar kauna.
There is no fear in love: true love has no room for fear, because where fear is, there is pain; and he who is not free from fear is not complete in love.
19 Muna kauna domin Allah ne ya fara kaunarmu.
We have the power of loving, because he first had love for us.
20 Idan wani ya ce,”Ina kaunar Allah”, amma yana kin dan'uwansa, makaryaci ne. Domin wanda baya kaunar dan'uwansa da yake gani, ba zai iya kaunar Allah da bai taba gani ba.
If a man says, I have love for God, and has hate for his brother, his words are false: for how is the man who has no love for his brother whom he has seen, able to have love for God whom he has not seen?
21 Wannan ne umarnin da muke da shi daga wurinsa: Duk wanda yake kaunar Allah dole ne ya kaunaci dan'uwansa.
And this is the word which we have from him, that he who has love for God is to have the same love for his brother.

< 1 Yohanna 4 >