< 1 Yohanna 2 >

1 'Ya'yana, na rubuta ma ku wadannan abubuwa domin kada kuyi zunubi. Amma idan wani yayi zunubi muna da matsakanci a wurin Uba, Yesu Almasihu, mai adalci.
わたしの小さな子供たちよ,わたしがこれらの事をあなた方に書き送るのは,あなた方が罪を犯さないようにするためです。だれかが罪を犯すなら,わたしたちには父のもとに助言者,公正なるイエス・キリストがおられます。
2 Shine fansar zunubanmu, ba ma namu kadai ba amma na duniya dukka.
彼はわたしたちの罪のため,いいえ,わたしたちの罪のためだけではなく,全世界のための贖いの犠牲です。
3 Ta haka muka san cewa mun san shi, idan mun kiyaye dokokinsa.
これこそ,わたしたちが彼を知っているということを知る方法です。すなわち,わたしたちが彼のおきてを守っているかどうかです。
4 Duk wanda yace, “Na san Allah” amma bai kiyaye dokokinsa ba, makaryaci ne gaskiya kuwa ba ta cikinsa.
「彼を知っている」と言いながら彼のおきてを守っていない者は,偽り者であって,真理はその人の内にありません。
5 Amma duk wanda ya kiyaye maganarsa, hakika kaunar Allah ta kammala a cikin wannan mutum. Ta wurin haka muka sani muna cikinsa.
しかし,だれでも彼の言葉を守っている者は,神の愛が本当にはっきりとその人の内に全うされています。これこそ,わたしたちが彼の内にいることを知る方法です。
6 Duk wanda yace yana cikin Allah dole ne shi da kansa yayi tafiya kamar yadda Yesu Almasihu yayi.
自分が彼の内にとどまっていると言う者は,彼が歩まれたとおりに自らも歩むべきです。
7 Kaunatattu, ba sabuwar doka nike rubuta maku ba, amma tsohuwar doka ce wadda kuka ji tun farko. Tsohuwar dokar kuwa itace maganar da kuka ji tun farko.
兄弟たち,わたしがあなた方に書き送るのは新しいおきてではなく,あなた方がはじめから持っていた古いおきてです。古いおきてとは,あなた方がはじめから聞いていた言葉です。
8 Amma yanzu ina rubuta maku sabuwar doka wadda gaskiya ce a cikin Almasihu da cikinku, saboda duhu yana wucewa, haske na gaskiya yana haskakawa.
それでも,わたしは新しいおきてをあなた方に書き送ります。それは,彼においてもあなた方においても真実です。なぜなら,闇が過ぎ去り,真の光がすでに輝いているからです。
9 Duk wanda yace yana cikin haske amma yana kin dan'uwansa, yana cikin duhu har yanzu.
自分は光の中にいると言いながら自分の兄弟を憎む者は,今なお闇の中にいるのです。
10 kuma wanda yake kaunar dan'uwansa yana cikin haske babu dalilin tuntube a wurinsa.
自分の兄弟を愛している者は光の中にとどまっており,その人にはつまずきのもとがありません。
11 Amma duk wanda yake kin dan'uwansa yana cikin duhu, yana kuma tafiya cikin duhu, bai san ma inda ya nufa ba, domin duhu ya makantar da shi.
しかし自分の兄弟を憎む者は,闇の中にいて,闇の中を歩んでおり,自分がどこへ行こうとしているのかを知りません。闇がその人の目を見えなくしてしまったからです。
12 Na rubuta maku, ya ku kaunatun 'ya'yana, saboda an gafarta zunubanku domin sunansa.
小さな子供たちよ,わたしがあなた方に書き送るのは,あなた方の罪が彼の名のために許されたからです。
13 Na rubuta maku, ubanni, saboda kun san shi wanda yake tun daga farko. Na rubuta maku matasa saboda kun yi nasara da mugun. Na rubuta maku, yara kanana, saboda kun san Uban.
父たちよ,わたしがあなた方に書き送るのは,あなた方がはじめからおられる方を知っているからです。 若者たちよ,わたしがあなた方に書き送るのは,あなた方が悪い者に打ち勝ったからです。 小さな子供たちよ,わたしがあなた方に書き送るのは,あなた方が父を知っているからです。
14 Na rubuta maku, Ubanni, saboda kun san shi wanda yake tun daga farko. Na rubuta maku, matasa, saboda kuna da karfi, kuma maganar Allah tana zaune cikinku. Kuma kun yi nasara da mugun.
父たちよ,わたしがあなた方に書き送るのは,あなた方がはじめからおられる方を知っているからです。 若者たちよ,わたしがあなた方に書き送るのは,あなた方が強く,神の言葉があなた方の内にとどまっており,あなた方が悪い者に打ち勝ったからです。
15 Kada kuyi kaunar duniya ko abubuwan da suke cikin duniya. Idan wani yayi kaunar duniya, kaunar Uban bata cikinsa.
世も世にあるものをも愛していてはなりません。だれかが世を愛するなら,父の愛はその人の内にありません。
16 Domin dukkan abubuwan da suke a cikin duniya, kwadayi na jiki, abin da idanu suke sha'wa, da rayuwar girman kai ta wofi, ba na Uban bane amma na duniya ne.
すべて世にあるもの,すなわち肉の欲望と目の欲望,そして暮らしに関する自慢は,父のものではなく,世のものだからです。
17 Duniya tana wucewa tare da sha'awarta. Amma dukkan wanda ya aikata nufin Allah zaya kasance har abada. (aiōn g165)
世はその欲望と共に過ぎ去りますが,神のご意志を行なう者は永遠にとどまります。 (aiōn g165)
18 Yara kanana, sa'a ta karshe ce. Kamar dai yadda kuka ji magafcin Almasihu yana zuwa, ko yanzu ma magaftan Almasihu da yawa sun rigaya sun zo, ta haka muka san sa'a ta karshe ce.
小さな子供たちよ,今は終わりの時です。そして,反キリストが来ることを聞いていたとおり,今でも多くの反キリストが現われています。これによって,わたしたちは今が終わりの時であることを知っています。
19 Sun fita daga cikinmu, dama su bana cikinmu bane. Gama idan da su namu ne da sun ci gaba tare damu. Amma da yake sun fita, ya nuna su ba na cikinmu bane.
彼らはわたしたちから去って行きました。しかし,彼らはわたしたちの仲間ではなかったのです。もしわたしたちの仲間だったなら,彼らはわたしたちと共にとどまったはずです。しかし彼らが去って行ったのは,彼らがわたしたちの仲間ではないことが示されるためだったのです。
20 Amma ku kun karbi shafewa daga wurin Mai Tsarki, kuma dukkanku kun san gaskiya.
あなた方は聖なる方から油を注がれているので,真理を知っています。
21 Bana rubuta maku bane domin baku san gaskiya ba, amma saboda kun santa, kuma ba wata karya da ta fito daga gaskiya.
わたしがあなた方に書いているのは,あなた方が真理を知っていないからではなく,むしろそれを知っているからであり,また偽りが真理に属していることは決してないからです。
22 Wanene makaryaci shine wanda yayi musu cewa Yesu ba Almasihu bane? Wannan mutumin shi ne magafcin Almasihu, tun da yayi musun Uba yayi musun Dan.
偽り者とは,イエスがキリストであるということを否認する者でなくてだれでしょう。これこそ反キリスト,父とみ子を否認する者です。
23 Ba wanda yayi musun Dan kuma yake da Uban. Dukkan wanda ya amince da Dan yana da Uban ma.
だれでもみ子を否認する者は父を持っていません。み子を告白する者は父をも持っています。
24 A game daku kuma, sai ku bari abinda kuka ji daga farko ya zauna a cikinku. Idan abin da kuka ji daga farko ya zauna a cikinku, kuma zaku kasance a cikin Dan da kuma Uban.
それで,あなた方に関する限り,あなた方がはじめから聞いていたことがあなた方の内にとどまっているようにしなさい。あなた方がはじめから聞いていたことがあなた方の内にとどまっているなら,あなた方もみ子の内,また父の内にとどまるでしょう。
25 Alkawarin da ya bamu kenan, rai na har abada. (aiōnios g166)
これこそ,彼がわたしたちに誓われた約束,すなわち永遠の命です。 (aiōnios g166)
26 Na rubuta maku wadannan abubuwa ne game da wadanda zasu baudar daku.
わたしはあなた方に,あなた方を惑わそうとしている者たちに関して,これらの事を書いてきました。
27 Game daku, shafewar daku ka samu daga wurinsa tana nan a cikinku, baku bukatar wani ya koyar daku. Amma kamar yadda shafewar da kuka karba a wurinsa ta koya maku dukkan abu, kuma gaskiya ne ba karya bane, tana nan a cikinku kamar yadda a ka koya maku, ku kasance a cikinsa.
あなた方に関する限り,彼から受けた油注ぎがあなた方の内にとどまっており,あなた方はだれかに教えてもらう必要はありません。むしろ,彼の油注ぎがあなた方にすべての事柄について教えており,またそれが真実であって偽りではないように,そしてそれがあなた方を教えたとおりに,あなた方は彼の内にとどまることになります。
28 Yanzu fa, 'ya'ya na kaunatattu, ku kasance a cikinsa domin sa'adda zai baiyyana mu zama da gabagadi ba tare da kunya ba a gabansa sa'adda zai zo.
それでは,小さな子供たちよ,彼の内にとどまっていなさい。それは,彼が現われる時に,わたしたちが大胆さを抱くことができ,彼の来臨の際に彼の前で恥じることのないためです。
29 Idan kun sani shi mai adalci ne, kun sani dukkan wanda ke aikata adalci haifaffe ne daga wurinsa.
彼が義なる方だと知っているなら,あなた方は義を行なう者がすべて彼から生まれた者であることも知っているのです。

< 1 Yohanna 2 >