< Waƙar Waƙoƙi 5 >

1 Na zo lambuna,’yar’uwata, amaryata; na tattara mur nawa da kayan yajina. Na sha zumana da kuma kakinsa na sha ruwan inabina da kuma madarana. Ƙawaye Ku ci, ku kuma sha, ya ku ƙawaye; ku sha ku ƙoshi, ya ƙaunatattu.
I have come into my garden, my sister, my bride. I have gathered my myrrh with my spice; I have eaten my honeycomb with my honey; I have drunk my wine with my milk. Friends Eat, friends! Drink, yes, drink abundantly, beloved.
2 Na yi barci amma zuciyata tana a farke. Ku saurara! Ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. “Buɗe mini,’yar’uwata, ƙaunatacciyata, kurciyata, marar laifina. Kaina ya jiƙe da raɓa, gashina ya yi danshin ɗiɗɗigar dare.”
I was asleep, but my heart was awake. It is the voice of my beloved who knocks: “Open to me, my sister, my love, my dove, my undefiled; for my head is filled with dew, and my hair with the dampness of the night.”
3 Na tuɓe rigata, sai in sāke sa ta kuma? Na wanke ƙafafuna, sai in sāke ɓata su?
I have taken off my robe. Indeed, must I put it on? I have washed my feet. Indeed, must I soil them?
4 Ƙaunataccena ya turo hannunsa ta cikin ramin ƙofar; zuciyata ta fara juyayi a kansa.
My beloved thrust his hand in through the latch opening. My heart pounded for him.
5 Na tashi don in buɗe wa ƙaunataccena, sai hannuna ya jiƙe sharkaf da mur, yatsotsina suna ɗiga da mur, a hannuwan ƙofar.
I rose up to open for my beloved. My hands dripped with myrrh, my fingers with liquid myrrh, on the handles of the lock.
6 Na buɗe wa ƙaunataccena ƙofa, amma ƙaunataccena ba ya nan, ya riga ya tafi. Zuciyata ta damu da tafiyarsa. Na neme shi amma ban same shi ba. Na yi ta kiransa amma bai amsa ba.
I opened to my beloved; but my beloved left, and had gone away. My heart went out when he spoke. I looked for him, but I didn’t find him. I called him, but he didn’t answer.
7 Masu gadi suka gamu da ni yayinda suke kai kawo a cikin birni. Suka yi mini dūka, suka yi mini rauni; suka ƙwace gyalena waɗannan masu gadin katanga!
The watchmen who go about the city found me. They beat me. They bruised me. The keepers of the walls took my cloak away from me.
8 ’Yan matan Urushalima, ina roƙonku, in kun sami ƙaunataccena me za ku ce masa? Ku ce masa na suma saboda ƙauna.
I adjure you, daughters of Jerusalem, If you find my beloved, that you tell him that I am faint with love.
9 Mafiya kyau a cikin mata me ya sa ƙaunataccenki ya fi sauran? Don me kike roƙonmu mu faɗa masa yadda kike ji?
How is your beloved better than another beloved, you fairest among women? How is your beloved better than another beloved, that you do so adjure us?
10 Ƙaunataccena kyakkyawa ne ƙaƙƙarfa kuma, da ƙyar a sami irinsa ɗaya a cikin dubu goma.
My beloved is white and ruddy. The best among ten thousand.
11 Kansa zinariya ce zalla; gashinsa dogaye ne baƙi wuluk kamar hankaka.
His head is like the purest gold. His hair is bushy, black as a raven.
12 Idanunsa sun yi kamar na kurciyoyin da suke kusa da ruwan rafi, da aka wanke da madara aka kuma kafa kamar kayan ado masu daraja.
His eyes are like doves beside the water brooks, washed with milk, mounted like jewels.
13 Kumatunsa kamar lambun kayan yaji suna ba da turare. Leɓunansa sun yi kamar furen bi-rana suna ɗiga da mur.
His cheeks are like a bed of spices with towers of perfumes. His lips are like lilies, dropping liquid myrrh.
14 Hannuwansa kamar sandunan zinariyar da aka sa musu duwatsu masu daraja. Jikinsa ya yi kamar gogaggen hauren giwan da aka yi masa ado da duwatsun saffaya.
His hands are like rings of gold set with beryl. His body is like ivory work overlaid with sapphires.
15 Ƙafafunsa sun yi kamar ginshiƙan dutsen alabastar da aka kafa su a cikin rammukar zinariya. Kamanninsa ya yi kamar Lebanon, mafi kyau kamar itacen al’ul nasa.
His legs are like pillars of marble set on sockets of fine gold. His appearance is like Lebanon, excellent as the cedars.
16 Bakinsa zaƙi ne kansa; komensa yana da kyau. Haka ƙaunataccena, abokina, yake’yan matan Urushalima.
His mouth is sweetness; yes, he is altogether lovely. This is my beloved, and this is my friend, daughters of Jerusalem.

< Waƙar Waƙoƙi 5 >