< Zabura 98 >

1 Zabura ce. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto. 2 Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai. 3 Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu. 4 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya, ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi; 5 ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya, da garaya da ƙarar rerawa, 6 tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago, ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki. 7 Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa, duniya da kuma kome da yake cikinta. 8 Bari koguna su tafa hannuwansu, bari duwatsu su rera tare don farin ciki; 9 bari su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa domin yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya da adalci mutane kuma cikin gaskiya.

< Zabura 98 >